Hajiya Lauratu Ado diso: Tallafa wa marayu shi ne zabina

Hajiya Lauratu Ado diso, ita ce shugabar makarantar sakandiren ‘yan mata ta Arabiyya da ke dambatta kuma tun tasowarta tana aiki ne a fannin ilimi amma ta yi fice wajen tallafa wa marayu da masu karamin karfi wanda yanzu haka akwai marayu masu yawa a hannunta tana kula da su ba tare da nuna gajiyawa […]

Hajiya Lauratu Ado diso: Tallafa wa marayu shi ne zabina

Hajiya Lauratu Ado diso, ita ce shugabar makarantar sakandiren ‘yan mata ta Arabiyya da ke dambatta kuma tun tasowarta tana aiki ne a fannin ilimi amma ta yi fice wajen tallafa wa marayu da masu karamin karfi wanda yanzu haka akwai marayu masu yawa a hannunta tana kula da su ba tare da nuna gajiyawa ba.

Tarihina

Sunana Lauratu Ado diso kuma an haife ni a unguwar diso cikin yankin karamar hukumar Gwale a shekara ta 1964. Na shiga firamare ta kofar Kudu a shekara ta 1971 na gama a shekarar 1974 inda na tafi makarantar firamare ta kwana ta Shekara wadda na kammala a shekara ta 1977.Daga nan na tafi kwalejin ‘yan mata ta Dala watau GGC Dala daga shekara ta 1977 zuwa 1982 .Sai makarantar share fagen shiga jami’a daga 1983 zuwa 1984 inda daga bisani na shiga jami’ar ta Bayero daga shekara ta 1984 zuwa 1987 kuma na yi bautar kasa daga 1987 zuwa 1988 sannan na sake komawa jami’ar Bayero na yi karatun digiri a fannin ilimi.
Bayan kammala karatu sai na fara aiki a makarantar sakandiren ‘yan mata ta Arabiyya ta Goron Dutse da ke jihar Kano daga shekara ta 1988 zuwa 1990. Sai aka mayar da ni makarantar sakandiren ‘yan mata ta danzomo da ke jihar Jigawa a matsayin mataimakiyar shugabar makaranta daga 1990 zuwa 1991.Daga nan kuma aka mayar da ni makarantar sakandiren Arabiyya ta ‘yan mata ta Sumaila da ke jihar Kano a matsayin shugabar makarantar daga shekara ta 1992 zuwa shekarar 1994.
Haka kuma an mayar da ni makarantar ‘yan mata ta Sumaila da na baro a matsayin mataimakiyar shugabar makaranta daga shekara ta 1994 zuwa 1998. Sannan aka mayar da ni makarantar sakandire ta ‘yan mata ta Gezawa da ke jihar Kano a matsayin shugabar makarantar daga shekara ta 1988 zuwa 2003.Na yi shugabancin makarantar sakandire ta ‘yan mata ta ’yar Gaya daga shekara ta 2003 zuwa 2007 inda kuma aka mayar da ni kwalejin ‘yan mata ta Dala a matsayin shugabar makarantar daga shekara ta 2007 zuwa 2012. A yanzu kuwa ni ce shugabar makarantar sakandiren ‘yan mata ta Arabiyya ta dambatta da ke jihar Kano tun daga shekara ta 2012 zuwa yau .
Sauran aiyuka
Kasancewa ta cikin fannin ilimi tun bayan na kammala karatu , na kasance cikin aiyuka da wasu hidimomi da suka shafi ilimin mata.Kuma na samu kaina cikin wasu kungiyoyi da suka jibanci ilimi kamar kungiyar shugabannin makarantun sakandire watau ANCOPSS da kungiyar tsofaffin dalibai da ta iyaye da malamai da kungiyoyi makamantansu wadanda lokaci ba zai bari in bayyana su duka ba. Kuma har yanzu dinnan ina cikin hidima wadda ta shafi ilimi domin shi ne aikin da na dauka muhimmi a rayuwar dan Adam.

Lambobin yabo
Akwai abubuwa da nake matukar jin dadi idan na dube su watau su ne lambobin yabo da na samu daga kungiyoyi na ciki da wajen kasar nan. Akwai wadanda na samu daga gwamnatin jihar Kano da wadanda na samu daga masarautar Kano, duk a kan kokarin da nake yi kan ilimin mata da kawo ingantuwar al’amura a kusan dukkan inda na shugabanta. Gaskiya ina mai alfahari da wannan al’amari kuma lambar yabo ta baya-bayan nan da na samu , wadda kuma ta kara min kwarin gwiwa ita ce wadda hukumar kula da makarantun sakandire ta jihar Kano ta ba ni.
Don haka ina mai matukar godiya ga Allah madaukakin Sarki da ya raya ni har na zamo mai ba da gudumawa ga al’umma musamman bai wa mata ilimi wanda kowa ya san cewa mata su ne iyayen al’uma.

kalubalen rayuwa
Kowane dan Adam yana da kalubale da yake damunsa, kuma Allah ne da kansa yake taimaka wa bayinsa wajen ganin sun fita daga wannan kalubale musamman daga karshe sai mutum ya cimma nasara, don haka ina kara shawartar ‘yan uwana mata da kada su yanke kauna da samun nasarar rayuwa muddin dai sun kasance masu yadda da hukuncin Ubangiji.

Darussan da na koya a rayuwa
Babu shakka na koyi darussa masu matukar amfani ga rayuwar dan Adam idan na dubi irin gwagwarmayar da na yi ta rayuwa. Na koyi abubuwa masu tarin yawa wajen abokan aiki domin kowane dan Adam Allah ya ba shi wata baiwa walau a fannin jagoranci ko kuma ta fuskar mu’amulla ta yau da kullum.Don haka ina gode wa Allah da na samu gogewa a sha’anin jagoranci da kawo sauyi a dukkan inda na shugabanta.

Iyali
Ina da iyalai a halin yanzu kuma ina tare da maigidana watau Farfesa Isa Muktar na jami’ar Bayero da ke Kano.Muna da ‘ya’ya da kuma jika wanda ko shakka babu muna zaune cikin matukar farin ciki da walwala.Alhamdulillahi.

Burina
Kasancewa ta ‘ya mace, babban burina shi ne in taimaka wa marayu a duk inda na samu kaina saboda tausayawa da nuna kauna ga bayin Allah. Yanzu haka akwai marayu guda 13 a hannuna wadanda nake rike da su ‘ya’yan ‘yan uwa da wasu da na dauka

saboda ba su da wata madafa .Akwai wata daliba wadda na karba a hannun mahaifinta da yake mai karamin karfi ne, yanzu haka tana hannuna na sanya ta a makaranta tana karatu bisa daukar dawainiyar da na yi mata.
Haka kuma ina nan ina kokarin kafa wata gidauniya wadda zan rika taimakon marayu da ita duk da cewa dukkan abin da nake yi, ina yi ne da abin da nake da shi daga albashina da hakkokin aiki. Amma da yardar Allah zan ci gaba da aikin taimaka wa marayu har iya bakin rayuwata kuma komai zan samu zan yi amfani da wani kaso wajen taimaka wa marayu saboda tausayawa.

Shawara ga mata
Ina fata ‘yan uwana mata za mu kara kasancewa masu daraja da kare mutuncin kanmu da mutuncin mazajenmu da kuma kyautata tarbiyyar ‘ya’yan mu saboda zamani ya canza. Mu tsaya mu rike iyalinmu da kyau mu daina yawan la’antar ‘ya’yanmu ko na ‘yan uwa, mu sani cewa ‘ya’ya da Allah ya ba mu amana ce ya ba mu . Sannan ina kira ga mata wadanda ba su da yawan iyali su rika daurewa suna daukar marayu suna rike su.In sha Allahu, Allah zai ba su biyan bukata a nan duniya da lahira .Kuma ina fata Allah ya kara mana lafiya da zaman lafiya a wannan kasa tamu .
Sannan ina jaddada rokona ga dukkan wadanda Allah ya bai wa iko da su rika daurewa suna taimaka wa marayu domin su kara jin dadin rayuwa kamar masu iyaye, domin maraici daga Allah yake kuma Allah yana kishin dukkan bayinsa.