Hajiya Maryam Abdullahi: Hakuri shi ne sirrin nasara a rayuwa

Hajiya Maryam Abdullahi wanda aka fi sani da Lami Jebi fitacciyar ‘yar siyasa ce a Jihar Kaduna. A hirarta da Zinariya ta yi kira ga mata da matasa su kasance masu hakuri da daraja na gaba da sauran batutuwan rayuwa. Tarihin RayuwataAssalamu alaikum, sunana Maryam Abdullahi amma wasu na kira  na da Lami Jebi, an […]

Hajiya Maryam Abdullahi: Hakuri shi ne sirrin nasara a rayuwa

Hajiya Maryam Abdullahi wanda aka fi sani da Lami Jebi fitacciyar ‘yar siyasa ce a Jihar Kaduna. A hirarta da Zinariya ta yi kira ga mata da matasa su kasance masu hakuri da daraja na gaba da sauran batutuwan rayuwa.

Tarihin Rayuwata
Assalamu alaikum, sunana Maryam Abdullahi amma wasu na kira  na da Lami Jebi, an haife ni  a shekarar 1966 a garin Tudun Saibu da ke cikin karamar Hukumar Soba ta Jihar Kaduna. Bayan kammala karatuna, sai na fara harkar kasuwanci, ban dade ba sai na tsunduma cikin harkokin siyasa a jamhuriya ta biyu wato zamanin Shagari.  
Da soja suka karbe mulki sai na kara komawa kasuwancina gadan-gadan har zuwa lokacin da muka shiga jam’iyyar NRC, wato zamanin Gwamna Dabo Lere na Jihar Kaduna ke nan. Daga nan Allah Ya kara kawo canjin gwamnati, muka ci gaba da siyasa har zuwa lokacin da Marigayi Janar Sani Abaca ya yi juyin mulki a shekarar 1993,  bayan rasuwarsa a shekarar 1998 sai aka  kafa jam’iyyun siyasa da mu. Bayan an gudanar zabubbuka jam’iyyarmu ta PDP ta lashe zabe a Jiharmu Kaduna, muka kafa gwamnati karkashin jagorancin Gwamna Ahmad Muhammad Makarfi. Da ya kammala wa’adinsa na zango biyu a jere sai Namadi Sambo ya gaje shi, daga nan  sai  Marigayi Patrick Yakowa ya canji Gwamnanmu Namadi bayan da shugaban kasa ya zabe shi mataimakinsa. Yanzu kuma muna tare da Gwamna Muktar Ramalan Yero a fatanmu na ganin mun taimaka don ciyar da jiharmu gaba.
Abin da na koya daga mahaifiyata
Fadin gaskiya a ko ina kuma ga kowa. Mahaifiyata ta tsani makaryaci saboda haka ta hore mu da fadin gaskiya a duk inda muka samu kanmu. Na biyu, ta koya mana hakuri da bin na gaba da mu. A ganina wadanan su ne tushen nasarar kowane mahaluki a bayan kasa. Sai kuma tsafta, domin ba zan manta ba daga mun tashi da safe, gabanin sallar Asuba, za mu fara aikin gyare-gyare da wanke-wanke don tsaftace gida, kuma zan so a ce kowace mace ta dauki wadannan dabi’u don ci gaban kanta da iyalinta.
kalubale
A gaskiya ba zan ce ban fuskanci kalubale ba saboda ba ya yiwuwa a ce mutum ya rayu ba tare da ya gamu da kalubale nan da can ba. daya daga cikin kalubalen baya-bayan nan da na fuskanta da kuma ba na mantawa da shi, shi ne, irin-irin kone-konen da suka faru bayan zabubbukan shekarar 2011. Saboda zaman lafiya ke kawo ci gaba, akasin haka koma baya yake kawowa, wannan abin da kowa ya sani ne. Masu iya magana ma cewa suke zaman lafiya yafi zama sarki, shi ya sa nake ganin ya dace matasa su ci gaba da ba da gudunmawar da ta dace don ganin dorewar zaman lafiya a jiharmu ta Kaduna da ma Najeriya gaba daya.
Abinci
Na fi sha’awar zogale da rama da kuma salad, a takaice dai na fi  son ganyayyaki da ‘ya’yan’itatuwa saboda yadda suke gina jiki da kara lafiya.
Tufafi
A gaskiya na fi son dogayen tufafi da za su rufe gaba daya jiki, saboda irin kananan tufafin da ‘ya’yanmu mata ke sanyawa ba su dace da al’adunmu da kuma addinanmu ba.
kasashen da na ziyarta
Bayan ziyarce-ziyarce na zuwa Saudiyya, na kuma ziyarci kasar Kenya a zamanin Gwamnan Jihar Kaduna, Dabo  Lere  don raka ‘yan wasan kwallon hannu wanda Jihar Kaduna ta wakilci Najeriya a can.  Mun yi rakiyar ne  a matsayinmu na  mambobin  Hukumar Wasanni ta Jihar Kaduna ta wancan lokacin.

Mukaman da na rike
Da farko na fara harkokin siyasa ne a jamhuriya ta biyu inda na shiga jam’iyyar NPN, daga nan sai na zama mamba a Hukumar Wasanni ta Jihar Kaduna lokacin gwamnatin Gwamnan Dabo Lere, a wancan lokacin ba ma’aikatar wasanni da ake da ita yanzu.
A lokacin da Alhaji Hamisu Abubakar (Mai Rago) ke neman takarar Gwamnan Jihar Kaduna  a shekarar 2003, ni ce jagorar mata ta kungiyar neman zabensa da ke shiyya ta biyu ta jihar. Daga nan kuma a shekarar 2007 na zama  jagorar matan shiyyar da ke goyon bayan takarar Sanata Ahmad Muhammad Makarfi  a matsayin shugaban kasa.
Sai kuma lokacin da Gwamna Namadi Sambo ya zama Gwamnan Jihar Kaduna a shekarar 2007, ya nada ni mai ba shi shawara ta fuskar ayyukan ci gaba. Bayan Shugaba Jonathan ya zabe shi Mataimakinsa a shekarar 2010, sai marigayi Patrick Yakowa  ya zama gwamna. Ya kuma  sa  ni mamba a kwamitin ci gaban yankin Badiko da kewaye.
An ci gaba da damawa da ni inda lokacin da Alhaji Isma’ila Yakawada ya fito takarar Gwamnan Jihar Kaduna a shekarar 2011, ya ba ni jagoranci  kungiyar mata da ke masa yakin neman zabe ta shiyyarmu.
Na halarci babban taron jam’iyyar PDP da ya nada Alhaji Kawu Baraje a matsayin shugaban jam’iyyar na riko, inda a lokacin gudanar da zaben na kasance mamba a kwamitin tsare-tsare.
Na kuma je babban taron jam’iyyar na watan Maris din shekara 2012, a taron da aka zabi Alhaji Bamanga Tukur kuma a matsayin shugaban jam’iyyar PDP, na zama mamba a kwamitin samar da tsaro a lokacin taron.
Shawara ga matasa
Matasa su nemi ilimi saboda duk abin da zai iya kawo canji mai ma’ana a rayuwa sai da ilimi. Ilimi shi ne zai nuna yadda za a yi cudanya da mutane. Idan da mata da matasanmu za su ilmantu kuma su yi amfani da abin da suka koya, to da matsalolinmu sun kare.
Burina
Ni dai babban burina shi ne na cika da kyau da imani, saboda  babban dalilin zamanmu a nan duniya shi ne kyautata makomarmu ta lahira. Ka ga idan na samu wannan ni zan ce buri ya gama cika.