Hajiya Maryam Sheikh Ahmad Lemu: Yin Da’awah sai mai juriya
Hajiya Maryam Sheikh Ahmad Lemu ‘yar shahararren malami Sheikh Ahmad Lemu ce, a hirar da ta yi da Zinariya ta bayyana yadda ta fara da’awah, ta kuma bukaci iyaye su ba da himma wajen ba mata ilimin addini da na boko. Tarihina a takaiceSunana Maryam Sheikh Ahmad Lemu, an haife ni a Janairu, 1973 a […]
Hajiya Maryam Sheikh Ahmad Lemu ‘yar shahararren malami Sheikh Ahmad Lemu ce, a hirar da ta yi da Zinariya ta bayyana yadda ta fara da’awah, ta kuma bukaci iyaye su ba da himma wajen ba mata ilimin addini da na boko.
Tarihina a takaice
Sunana Maryam Sheikh Ahmad Lemu, an haife ni a Janairu, 1973 a Sakkwato. Ni ‘yar Sheikh Ahmad Lemu ce, mahaifiyata kuma Hajiya A’isha. Yayana Malam Nuruddeen Ahmad Lemu ya zama mini abin koyi a al’amura da yawa a rayuwa.
Na yi firamare a Minna, na yi sakandare a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Minna, Jihar Neja. Na yi aure bayan na kammala sakandare a lokacin ina da shekara 18. Na je makarantar koyon dabarun girke-girke da ke kasar Birtaniya, inda na koyi girke-girken kasashen Faransa da Italiya. A lokacin da na kammala na iya nau’o’in abincinsu fiye da 200. Bayan da muka yi aure ne mijina Malam Sa’id Suleiman Takuma ya kai ni kasar Amurka. Mun kasance a can har tsawon shekara 12, a can na haifi ‘ya’yanmu guda 2 duk maza. Babban yana da shekaru 16, yayin da karamin yake da shekara 13. Mijina ya yi zaman can tsawon shekara 22.
Mun dawo da ‘ya’yanmu Najeriya don su samu tarbiyya irin tamu kamar yadda iyayenmu suka yi mana. Bayan mun dawo ne mutane suka rika mamakin wannan matakin da muka dauka, suna ganin cewa ai mun baro wata duniya mai cike da jin dadi da duk abin da mutum yake bukata zai samu a Amurka. Dawowar mu ke da wuya na fara aiki a Kwalejin New Horizons a matsayin jami’a mai kula da gidajen kwanan dalibai. Bayan wasu shekaru aka sake kara mini wani aikin a matsayin Jami’ar da ke kula da Ma’aikatan Kwalejin.Wadannan ayyukan nake yi har zuwa wannan lokaci.
Yadda na tashi
Na samu duk kulawar da ta kamata. Iyayena suna da ilimin boko da na addini, wannan ya sa na samu kyakkyawar tarbiyya, sun dora dukkan ‘ya’yansu a kan kaunar addini tare da sanin yadda za mu bauta wa Mahaliccinmu da kuma nuna kauna ga jama’a kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya nemi mu yi.
Dalilin fara da’awah
Na fahimci haka ne kasancewata tare da daliban da ke makarantar da nake aiki. Suna sha’awar salon rayuwarta, na fahimci suna bukatar tunatarwa game da rayuwa don su samu babban rabo a gobe kiyama. Na kasance mace ce mai aikata abin da take koyarwa a duk wurin da na samu kaina. Ban yarda in aikata sabanin abin da nake koyarwa ba. Kada ka manta wadannan daliban suna kallace-kallacen da ke ba su sha’awa a matsayin su na yara. Abin takaicin shi ne wasu daga cikin wadannan abubuwan da suke kallo sun saba wa koyarwar addini. Misali, irin suturun da wadanda suke sha’awa suke sa wa, sun fi ba su sha’awa, fiye da hijabin da suke amfani da su. Yin da’awah sai mai juriya.
Yadda nake da’awah
Ina gudanar da shirin fadakar da jama’a game da al’amuran rayuwar yau da kullum, musamman wadanda ke ci wa al’umma tuwo a kwarya. Annabi Muhammad (SAW) ya nuna akwai bukatar mutum ya san dalilin da ya sa yake nan duniya da kuma yadda zai yi tattalin guzurinsa yayin da yake shirin koma wa ga Mahaliccinsa. Wannan ne ya sa nake shirya yadda za a gudanar da shugabanci nagari, sannan ina taimakawa wurin sanin makasudin rayuwa da yadda za su cim ma burinsu kafin wa’adin zamansu a duniya kare.
Burina
Babban burina shi ne in ci gaba a kan wannan hanyar da na dauka ta taimaka wa jama’a.
Bakin cikina
Nakan yi matukar bakin cikin yadda a wannan zamanin ake yawan samun matsalolin mace-macen aure. Za ka ga ma’aurata sun yi auren da bai wuce watanni ko shekaru kalilan ba, ka ji an ce maka auren ya mutu. Wannan wata masifa ce hakan ta sa nake shirya taron koya wa jama’a dabarun zamantakewar aure. Wasu daga cikin makasudin mutuwar aure sun hada da dogon buri da rashin fuskantar gaskiyar al’amari.
Sirrin aurena
Babban sirrin dorewar aurenmu da mijina shi ne, na farko mutunta juna da kuma musayar ra’ayoyi a duk lokacin da bukatar hakan ta taso. Bayan haka, mun amince wa juna da kuma manufofi iri daya, wadanda muke son mu cim ma a rayuwarmu. Muna yawan tsokanar juna domin samun nishadi. Wadannan sun taimaka matuka wurin shakuwarmu. Don haka, ni da shi kullum soyayyarmu na kara zama sabuwa. Mijina ya kasance mai ba ni goyon baya game da duk abubuwan da ya ga sun dace. Wannan ne ya sa nike matukar girmama shi.
kalubale
Babban kalubalen da nakan fuskanta a duk lokacin da muke irin wannan taron shi ne, jama’a kan samu shakku game da yiwuwar duk abin da muka sa a gaba, musamman idan wannan abin sabo ne. Wasu kan furta kalaman da kan karya wa da dama gwiwa. Abin da na ga ya fi dace wa shi ne, a duk lokacin da aka bullo da wani sabon al’amari, to jama’a su daina saurin karaya, ba sai sun nemi izinin wasu kafin su gwada ba. Muddin suka samu nasara a rayuwa, za su manta da irin wadannan kalubalen tunkarar sababbin abubuwan da suka gamu da su.
Yadda na ji bayan mahaifina ya lashe lambar yabo ta Sarki Faisal
Gaskiya wannan lambar yabon kalubale ne babba ga mahaifinmu Sheikh Ahmad Lemu da mu ‘ya’yansa. Ina gida misalin karfe 9 na dare mahaifiyata Hajiya A’isha Sheikh Ahmad Lemu ta kira ni, sannan ta shaida mini lambar yabon da mahaifinmu ya samu. Nan take na nemi ta mika wa mahaifina waya, ta mika masa, abin da na lura da shi, shi ne yana kuka. Ban san lokacin da ni ma na fara kuka ba. Daga bisani, na daure na rika rarrashinsa, na ce masa ka cancanci wannan lambar yabon, kuma ina alfahari da ayyukan da kake aiwatarwa, ka yi hakuri, ka bar kuka.
Ra’ayina game da ilmin mata
Har yanzu akwai iyayen da ba su son ‘ya’yansu mata su yi karatun boko. Ina ganin ya kamata a ci gaba da wayarwa irin wadannan iyaye kai don su fahimci muhimmancin ilimin ‘ya mace wurin gina al’umma. A bullo da sababbin dabarun da za su sa a samu nasara. Fiye da shekara 20 ke nan muke wannan kokarin, ba kuma za mu karaya da wannan aikin da muka sa a gaba ba. Ya kamata a bunkasa fannin tattalin arziki ta yadda iyaye ba za su rika dogaro da kudin da ‘ya’yansu ke kawo musu sanadiyyar tallace-tallace ba.
Yadda nake shakatawa
Babbar hanyar da nake shakatawa ita ce, bayan na idar da sallar Asuba kafin rana ta fito sosai, sai na zauna shiru da kofin shayi ina sauraron kukan tsuntsaye, da yadda rana ke fitowa. Ina matukar sha’awar wannan. Sai wasan tennis tare da mijina ko mahaifiyata ko kuma duk wanda ya cancanci in yi wasa da shi. Nakan yi was an tennis a Lahadi, ko duk ranar da na yi sha’awar hakan. Ni da miji na mukan fita da sassafe mu yi ‘yan guje-guje da motsa jiki, mukan yi wannan sau hudu a mako. Sannan hira da ‘ya’yanmu musamman idan suna hutu, da kuma wasanni da su. Nakan zauna in kalli mijina da ‘ya’yana suna wasan kokawar da suka yi wa lakabi da WWF. Yanzu mijina ya fahimci babban ya girma, bai cika yi da shi ba, ya fi yi da karamin. Da suka fahimci haka sai su rika taruwa masa.
Abinci
Abincin da na fi shi ne, tuwon shinkafa da miyar gyada. Sai tuwon shinkafa da miyar kuka, sannan sakwara da miyar agushi. Haka kuma macaroni da wara.
Tufafi
A gaskiya na fi sha’awar dogayen tufafi tare da hijabi, wadanda a duk lokacin da na sa su nakan ji dadi. Mijina kuma yana son su don haka sun fi yawa cikin suturata.
kasashen da na ziyarta
Na ziyarci kasashen da suka hada da Birtaniya da Amurka da Turkiyya da Masar da Bahrain. Sai Bristilabia da Kuwait da Sri Lanka da Saudiyya da katar da Hardaddiyar Daular Larabawa da kuma Afrika ta Kudu.