Hajiya Rabi Ishak: Burina in samar da ilimi ga al’umma

Hajiya Rabi Ishak fitacciyar ‘yar siyasa ce a Jihar Jigawa, ita ce mace ta farko da ta zama shugabar makarantar Polytechnic ta Jihar Jigawa, ita ce kwamishinar lafiya ta farko a jihar. Ta jima tana fafutikar ganin ilimi ya inganta a arewacin Najeriya. Ta tattauna da Zinariya inda ta yi bayanin yadda za a shawo […]

Hajiya Rabi Ishak: Burina in samar da ilimi ga al’umma

Hajiya Rabi Ishak fitacciyar ‘yar siyasa ce a Jihar Jigawa, ita ce mace ta farko da ta zama shugabar makarantar Polytechnic ta Jihar Jigawa, ita ce kwamishinar lafiya ta farko a jihar. Ta jima tana fafutikar ganin ilimi ya inganta a arewacin Najeriya. Ta tattauna da Zinariya inda ta yi bayanin yadda za a shawo kan tabarbarewar ilimi a kasar nan.

Tarihina
Assalamu alaikum, sunana Rabi Ishak, an haife ni a garin Kazaure cikin fadar Mai Martaba Sarkin Kazaure, a Jihar Jigawa a shekarar 1957. Ni ‘yar gidan Sarkin Kazaure marigayi Hussaini Adamu ce. Mahaifina  babban malami ne, domin yana daya daga cikin manyan malamai a cikin sarakuna na zamaninsa. Na girma a wajen kakannina kafin na koma hannun mahaifina a Kaduna, inda yake harkar koyarwa. Na yi makarantar firamare a makarantar Sultan Bello;  makaranta ce da ake koyar da ilimin zamani da na addini. Ina daya daga cikin daliban farko, bayan na kammala ne sai na je makarantar sakandare ta Shekara da ke Jihar Kano, daga nan sai na koma makarantar kueens Amina. A shekarar 1972 na samu damar shiga jami’ar Bayero da ke Kano, inda na karanta Turanci, bayan na kammala digirina ne na sai na yi aure. Daga baya na yi digiri na biyu a kwas din International Studies.
Gudunmuwa ga al’umma
Sakamakon irin horon da na samu ne ya sanya na kafa makaranta mai zaman kanta mai suna First Grade a Kano, kuma ni ce shugabar makarantar. Na kafa makarantar ne da nufin taimaka wa marasa karfi, kasancewar burina in taimaka wa jama’a don ‘ya’yansu su samu ilimi mai nagarta, kasancewar idan al’umma ta samu ilimi mai inganci, to babu shakka ta samu komai na rayuwa. Baya ga haka na samar da makarantar al’umma wacce ake kira Community School. Na yi hakan ne duk don in taimaka wa al’umma, kasancewar akwai karancin makaratun hadaka a arewacin kasar nan. Burina a ce akalla kowace shekara yara 15 su samu ilmin addini da na zamani, su iya rubutu da karatu.
Burina
Burina a rayuwa shi ne in samar da ilimi ga al’umma. Burina in ga jama’a sun san abin da suke yi; in ga sun samu ilimi mai inganci, domin ilimi shi ne rayuwa. Burina dai na ga jama’a suna cikin walwala, sun fita daga cikin kuncin rayuwa.
Gwagwarmayar rayuwa
Na fara da koyar da Turanci ne a makarantar share fagen shiga jami’a da ake kira KAS, daga baya aka hada ni da babbar daraktar ilimi ta Jihar Kano ta wancan lokacin. Daga baya aka sake hada ni da Darakta-Janar na Ma’aikatar Walwala da harkokin Mata na Jihar Kano. Bayan an kirkiro Jihar Jigawa a zamanin mulkin Olayinka Sule sai aka nada ni mukamin Kwamishanar Lafiya ta Jihar Jigawa. Mu ne kwamishinonin farko na Jihar Jigawa. Ni ce shugabar makarantar Jigawa Polytechnic ta farko. Daga nan sai na tsunduma harkokin siyasa gadan-gadan. Na ba da gudunmuwa mai tarin yawa wajen raya kungiyoyi masu zaman kansu.
Abin da ya jawo lalacewar ilimi
Babban abin da ya jawo lalacewar ilimi a daukacin makarantun kasar nan shi ne, rashin kulawa daga shugabanni, gwamnati ta ki tsayawa ka-in-da-na-in a kan harkar ilimi, hakan ne ya sanya ilimi ya tabarbare a Najeriya, musamman ma a arewacin kasar nan. Rashin ba koyarwa muhimmanci shi ya sa ba a samun kwararrun malaman da za su rika koyarwa a makarantunmu, wannan ya yi ruwa da tsaki wajen samar da matsaloli a harkar ilimi, komai ya lalace.
Yadda za a dawo da darajar ilimi
Ya zama dole gwamnati ta dawo da takardar shaidar malanta mai daraja ta biyu (grade two), yin hakan ne mafita. Rashin yin grade two ya taimaka wajen samar da karancin malaman da suka cancanta wajen koyarwa, kuma rashin malamai masu inganci ya taimaka wajen tabarbarewar ilimi. Muddin gwamnati za ta dawo da takardar shaidar malanta mai daraja ta biyu, to babu shakka za a samu malamai masu inganci a daukacin makarantun kasar nan, sannan malaman da suke koyarwa a kasar nan musamman a arewa suna bukatar horo ko bita kan yadda za su koyar da dalibai, malaman ba su da kwarewa, to ta yaya za su bayar da ilimi mai inganci? Sai dai a bata goma biyar ba ta gyaru ba.

Kwadayin sarauta
A lokacin da mahaifina yake da rai na yi sha’awar ya nada ni sarautar Magajiyar Sarkin Kazaure kamar yadda Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero ya nada babbar ‘yarsa, amma yanzu sarautar ta fi karfina, kasancewar ni kanwar sarki na yanzu Alhaji Najib Hussaini Adamu ce, sai dai a yi wa ‘ya’yana ko kannena ko kuma sarki ya yi wa ‘ya’yansa.
Iyali
Shekarata 55, ina da ’ya’ya hudu da jikoki da dama. Ina tare da mijina Alhaji Ishak.
Abin da na fi sha’awa
Ina sha’awar karatu a kan kwamfyuta, na fi son na rika buga wasanni a kwamfyutata, saboda ni mace ce mai yawan bincike a kan abubuwan da suka shafi kwamfyuta. Ina nazari da bincike mai zurfi a kan harkokin rayuwar yau da kullum.
Abin da ke ci mini tuwo-a-kwarya
Ina jin takaici idan na ga an danne wa jama’a hakkinsu. Abin yakan ba ni haushi matuka idan na ga ana take ‘yancin mutane. Ina so na ga an ba mutane damarsu don sun yi abin da ya dace wajen neman ‘yancinsu. Ba na so na ga an bar jama’a kara zube bayan suna da basirar da za su yi abin da zai amfanar da jama’a.
kalubalen rayuwa
Nakan ji takaici ya mamaye ni musamman idan na duba yadda jama’a suke gudanar da rayuwarsu, ina zama da mutane da zuciya daya ne, amma sai ka ga wadansu suna yi wa jama’a wata irin fassara. Ba na son jama’a masu fuska biyu. Na rika samun matsala da mutane masu fuska biyu da ba sa tafiya a kan sahihiyar hanya, hakan babban kalubale ne a gare ni, wanda har zuwa yanzu na kasa shawo kan wannan kalubalen.