Hajiya Ramatu T. Aliyu: Mata mu kare mutuncinmu
Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu ta kasance shugabar kamfanin Azah International Nig. LTD, kuma shugabar Cibiyar Global Women and Youth Empowerment Strategy da ke Abuja. Kuma a yanzu ita ce Shugabar Mata ta jam’iyyar APC. TarihinaAn haife ni a Abuja, amma ni ’yar asalin masarautar Budan ce da ke karamar hukumar Lokoja a jihar Kogi. Ni […]
Hajiya Ramatu Tijjani Aliyu ta kasance shugabar kamfanin Azah International Nig. LTD, kuma shugabar Cibiyar Global Women and Youth Empowerment Strategy da ke Abuja. Kuma a yanzu ita ce Shugabar Mata ta jam’iyyar APC.
Tarihina
An haife ni a Abuja, amma ni ’yar asalin masarautar Budan ce da ke karamar hukumar Lokoja a jihar Kogi. Ni jikar Sarki Mamman Bawan Allah ce. Mu tara ne a gurin mahaifinmu, ni ce ta biyu. Na fara karatu a makarantar firamare ta Dawaki da ke Suleja a shekarar 1976. Na yi sakandare a makarantar gwamnatin tarayya da ke Minna a jihar Neja, shekarar 1982. Da ga nan kuma sai na shiga Kwalejin kimiyya da fasaha da ke Suleja. A shekarar 1990, na shiga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda na karanci ilimin Tsara Birane. Na yi bautar kasa a ma’aikatar aiyuka da samar da gidaje da ke Abuja. Na yi karatun digiri na biyu a fannin harkokin mulki. Ina karatu kuma ina shugabancin kamfanin ‘Azah Intermediaries Nig. L.T.D.’ Inda muke gine-gine da adon kawata cikin gida.Kuma ni ce shugabar Cibiyar ‘Global Women and Youth Empowerment Strategy’, wato cibiyar da take tallafawa mata da matasa da gajiyayyu.
Na fara siyasa ne a shekarar 2004, lokacin mai girma Zakari Angulu Dobi Shugaban karamar hukumar Gwagwalada ya ba ni mai ba da shawara ta musamman a kan harkokin mata da matasa da wasanni. A shekara 2007 na tsaya takarar ’Yar Majalisar Wakilai don wakiltar mazabun Kwali da Kuje da Abaji da ke birnin tarayya Abuja.
A shekarar 2008 na kasance zababbiyar mataimakiyar shugabar jamiyyar ANPP ta kasa. Na kasance mace ta farko daga Arewa a Najeriya da ma Afirka baki daya. A shekarar 2010 na kasance zababbiyar shugabar mata ta jamiyyar ANPP. Kuma duk da haka na ci gaba da aikin tallafawa mata da matasa da gajjiyayyu.
Kuma sai zancen hade jam’iyya ya taso. Saboda haka da ni da su Bafarawa da malam Ibrahim Shekarau da su Yariman Bakora muka zagaye kasar nan kaf, a kan lallai a hade jam’iyyu, domin a sami karfin da wannan jam’iyya za ta taka rawar gani, kamar yadda muke kai a yau. Da ni aka kirkiro sunan jamiyyar APC kuma muka lakaba mata taken Canji.
Na zama zababbiyar shugabar mata ta farko a wannan jam’iyya ta APC. Muna bi gida-gida muna wayar da kan mata domin su fahimci siyasa, kuma mazajensu su ba su hadin kai, kada mu bar wa ’yan iska su mulke mu.
Maigidana Alhaji Ahmad Tijjani Aliyu yana ba ni goyon baya sosai. Saboda haka na lashi takobi, babu gudu, ba ja da baya. Sai na kai duk inda Allah ya nufa in kai a fagen siyasa, tare da kare mutuncina.
Sarauta
Har dai ni haifaffiyar masarautar Budan ce, ana kiranmu ‘Lerama’ wato Gimbiyoyi ke nan. Saboda dadewa a Gwagwalada da kuma rawar da muka taka, sai sarkin Aguman Gwagwalada ya ba ni sarautar Gwagwalada a shekarar 2002. Har yanzu ina rike da wannan sarauta kuma ina kare darajar wannan masarauta, duk da cewa ina siyasa. Ko kwanan ma a masarautar Budan wato inda na fito, an ba ni sarautar Garkuwa. Amma ban karba ba. Saboda a al’ada, ba a bayar da wannan sarauta sai wadda take kai ta mutu, kuma sai wadda take jiran gado ta kai wadansu shekaru kafin a nada ta. Duk da canjin zamani, ba na so a fara saba al’ada a kaina. Domin kuwa wadda take kai, ba ta rasu ba.
Kyaututtukan da na samu
Na samu kyaututtuka sama da ashirin ,a nan gida Najeriya da kuma kasashen waje, wadansu ma ba zan iya tunawa ba. Kuma har yanzu ana ba ni. Kadan daga cikinsu sun hada da kyautar da ‘African Women in Leadership Organization’ Washington DC da ke kasar Amurka ta ba ni a shekarar 2013 sakamakon tallafin da muke yi wa mata da matasa da gajjiyayyu. Haka nan ‘Nigerian Labour Congress’ ta ba ni kyauta a shekarar 2012 a matsayin Jarumar Mace. A wannan shekara dai ‘African Edpression News Media’ sun ba ni lambar yabo da take nuna mace mai jajircewa da iya magana ta wannan shekara. A shekarar 2013 na karbi lambar yabo ta Gwal daga ‘Distinguished Leadership in National Debelopment’sakamakon nuna kyawawan halayen jagoranci.
Abin da yake ba ni sha’wa a siyasa
Abin da ya fi burge ni a siyasa shi ne, ita ca hanyar da zan iya taimaka wa jama’a yadda nake so. Ina da sha’awar taimakawa mutane da kawo canjin rayuwa musamman ga mata da gajiyayyu da matasa. Kuma ta hanyar siyasa ake zabar shugabanni. Saboda haka dole mu mike domin kada mu bar wa ’yan iska su mulke mu, kuma su zama abin koyi ga na baya.Filin siyasa yana ba da dama ka ga yaro ya taso ya taka rawa wadda ko iyayensa basu taka ba.
Abin da na koya a gurin iyayena
Mahaifinmu ba ya wasa a gurin tarbiyya, na koyi ladabi da biyayya da girmama mutane a gurin iyayena.Kuma na fahimci komai na Allah ne. Kasancewar mu mata a gidan satarauta kin san babu sauki, domin ana ganinmu ba komai ba ne. Amma mahaifinmu ya koya mana jajircewa da kwarin gwiwa cewa mace za ta iya kai wa duk wani matsayi idan ta mike. Babanmu ya nuna mana kada mu rika ganin gazawa ko rauni saboda mu mata ne, halitta ce ta Allah, ya yi maza kuma ya yi mata.
Hada aikin gida da harkokin siyasa
Babu sauki,amma duk da haka abin sa kai ne. Idan ka sa kanka sai Allah ya kawo sauki. Har dai akwai masu taimakawa, amma ba za ka bar wa mutane hidimarka ba gaba daya. Misali harkar siyasar nan za ka yi bincike sosai kafin ka yi magana a cikin mutane, ni nake rubuta kayana,kuma in fito in karanta a bainar jama’a, wannan babu sauki. Haka ma a kicin, ni nake girka abincin maigidana, domin kuwa shi ne ma’aikata ta farko. Saboda haka babu sauki, yawanci nakan kai karfe biyu na dare ban yi barci ba.
Nasarori
Akwai nasarori domin kuwa akwai mata da almajirai da yawa da muka koya musu sana’oi daban-daban. kuma suna cin abinci da wannan sana’a. Kuma akwai wadanda muka tallafa musu a gurin zaman aure da sauransu.
Akwai gine-gine da na yi na saka ’yan makaranta a saukin kudi kamar a Zariya da Samaru da Gwagwalada.
Haka nan ta bangaren siyasa ma akwai mata da yawa da muka wayar musu da kai.
kalubale
Akwai kalubale sosai domin akwai yarfe da kage kala-kala daga wajen maza da mata. Kuma mata muna da kishi don haka wani lokaci mukan kasance sanadiyyar faduwar ’yar uwarmu da kanmu. Domin ba na mantawa lokacin da na fara fitowa takarar Shugabar Mata, wata mata ta dube ni ta ce, “An ce miki girl leader ake nema,ai ba wasan yara ake ba. Woman leader ake nema.” Wannan magana ta yi min zafi,amma hakan bai sa na janye ba.
Darasin da na koya a rayuwa
Darasin da na koya shi ne kada ka rika yi wa mutum mummunan zato. Lokacin muna ANPP ni kadai ce mace.Kafin Hajiya Fatima Muhammed ta shigo. Haka nake shiga cikin maza mu yi taro ni kadai kwal. To wani idan ya ganni zai yi min mummunar fahimta. Ya ce kullum ina tsakiyar maza. Matukar mace za ta kare addininta da mutuncinta, babu wanda zai kawo mata wargi. Saboda haka kada mu ji tsoro mu koya wa ’ya’yanmu mata rashin tsoro tare da kare mutuncinsu. Idan muka duba tarihi za muga yadda Nana Khadija ta kasance jaruma shahararraiya ta wuce ma mazan,kafin Annabi (SAW) ya ganta ya aura.
Mutanen da nake koyi da su
Akwai Sarauniyar Zazzau Amina, tana daya daga cikin matan Arewa da suka yi rawar gani. Sai kuma Janar Muhammadu Buhari, ya tsaya a kan gaskiya, ba cin amana ba ha’inci.
Burina
Shi ne in ga matan Arewa sun sami ’yanci, kansu ya waye ba tare da mun yar da addininmu da al’adunmu da mutuncimu ba. Ina son in ga ’yar Arewa ta shahara a duk abin da ta sa kanta kamar aikin likita ko kasuwanci da sauran fannonin rayuwa.Har mu zama abin koyi, a daina raina mu.
Ina so a tuna ni a matsayin wadda aka ceto Najeriya da ita.Kuma wadda ta taimaki masu karamin karfi rayuwarsu ta inganta.
Shawara ga mata
Mu kare mutauncinmu, mu rike addininmu da suturarmu. Kuma mu nemi duniya, mu nemi lahira kamar gobe za mu mutu. Kuma mu fahimci cewa kasancewarmu mata ba rauni ba ne, kuma ba uzuri ba ne, ki ce don kina mace ba za ki nemi na kanki ba. Mu rungumi gaskiya,mu tarbiyyantar da yara. Mu daina kallon fina-finan shirme,domin yara sukan koyi munanan dabi’u. Mace a Arewa a Najeriya tana iya kai wa ko ina, matukar ta nemi ilimin addini da na boko.