Hajiya Safiya Muhammad: Sai da ilimi rayuwa za ta inganta

Hajiya Safiya Muhammad Babbar Darakta ce a Hukumar da ke Kula da Makarantun Firamare da Sakandare da ke karkashin Hukumar Ilimi ta Jihar Jigawa. Ta yi aikin koyarwa a Makarantar College of Art and Remedial Study (CARS) da ke Jihar Kano. Ta kuma rike mukamin shugabar sakandaren ’yan mata ta kiru da kuma sakandaren ’yan […]

Hajiya Safiya Muhammad: Sai da ilimi rayuwa za ta inganta
Hajiya Safiya Muhammad: Sai da ilimi rayuwa za ta inganta

Hajiya Safiya Muhammad Babbar Darakta ce a Hukumar da ke Kula da Makarantun Firamare da Sakandare da ke karkashin Hukumar Ilimi ta Jihar Jigawa. Ta yi aikin koyarwa a Makarantar College of Art and Remedial Study (CARS) da ke Jihar Kano. Ta kuma rike mukamin shugabar sakandaren ’yan mata ta kiru da kuma sakandaren ’yan mata ta Taura. Ta yi bayanin gwagwarmayar da ta yi a fannin koyarwa, sannan ta bukaci iyaye su rika ba karatun ’ya’yansu muhimmanci, kasancewar sai da ilimi rayuwa za ta inganta.

Tarihin Rayuwata
Assalamu alaikum, an haife ni a shekarar 1963 a garin Malam Madori da ke Jihar Jigawa. Na yi makarantar firamare da ake kira Malam Madori Primary School, daga nan na yi Makarantar hadaka (Unity) da ke garin Bidda a Jihar Neja. Bayan na kammala sakandare ne na yi Makarantar School of Basic Study da ke Jami’ar Bayero ta Kano, wato daga 1982 zuwa 1986. Na yi digiri a fannin koyarwa a Jami’ar Bayero ta Kano, sanna na yi hidimar kasa  a Ma’aikatar Kula da Ilimin ’Ya’yan Makiyaya (Agency for Mass Education) a lokacin Jihar Jigawa na tare da tsohuwar Jihar Kano.
Bayan hidimar kasa ne a shekarar 1987 na fara aikin koyarwa a Makarantar College of Art and Remedial Study (CARS) da ke Jihar Kano. Daga 1989 zuwa 1990 na rike mukamin mataimakiyar shugabar sakandaren ’yan mata ta kiru. A shekarar 1990 na zama shugabar makarantar. Daga baya aka mayar da ni karamar Hukumar Taura. Na shafe shekara 13 a matsayin shugabar sakandaren ’yan mata ta Taura. Wannan duk sun faru ne kafin a kirkiro a Jihar Jigawa.
Bayan an kirkiro Jihar Jigawa ne aka dawo da ni karkashin Hukumar Ilimi ta Jihar a matsayin Mataimakiyar Darakta mai Kula da Makarantun jihar wato (karkashin Hukumar SEMU ke nan), wadda ake cewa State Education and Monotoring Unit. Wannan hukumar tana aiki ne tamkar ’yan sandan raya harkokin ilimi da suke neman tabarbarewa a jihar, domin ganin ta ceto ilimin daga rugujewa.
Daga 2007 zuwa 2012 na rike mukamin Mataimakiyar Darakta-Janar ta Hukumar SEMU. Bayan karin girma da Gwamna Sule Lamido ya yi wa Babban Daraktan Hukumar zuwa Babban Sakataren Hukumar Ilimi na Hukumar (PS), sai Gwamna Lamido ya nada ni Darakta Janar din hukumar, wanda mukamin nake kai har yanzu.
Gwagwarmaya
A gaskiya na yi gwagwarmayar rayuwa daidai gwargwadon hali, sai tawa gwagwarmayar mai tsafta ce, ba kamar ta sauran jama’a ba, ba gwagwarmaya ce da take cike da matsaloli ba, tawa mai sauki ce, sai dai babban abin da ke ci mini tuwo a kwarya shi ne, rashin ba ilimin mata muhimmanci a wancan zamanin, saboda mahaifiyata ba ta so in tafi makaranta da ke nesa, ma’ana in yi nesa da ita, kasancewar a wancan lokacin makarantar da zan je ta yi nisa, domin an tura ni makarantar hadaka da ke Bidda, Jihar Neja ne, amma da taimakon Allah, sannan da taimakon yayana na samu nasara, kasancewar shi ne ya dauri mini gindi na yi karatun, na kuma kammala ba tare da na samu wata matsala ba.
Ta fuskar koyarwa ma na yi gwagwarmaya da iyayen yara, domin sun ki tsayawa sosai a kan karatun ’ya’yansu musamman ma mata. Na yi tsayin daka wajen ganin yara mata sun samu ilimi mai zurfi, bayan sun kammala karatunsu na sakandire, sabanin yadda iyaye suke dauke ’ya’yansu su yi musu aure bayan sun kammala karatun sakandire, wasu kuma su hana su yin karatu a jami’a alhalin za su iya karatun. Nakan tsaya sosai musamman a kan yara masu hazaka in ga sun samu damar ci gaba da karatu don su samu ilimi mai zurfi.
Dawowarmu wannan ma’aikata ta SEMU kafin zuwan Gwamna Lamido mun same ta a cikin wani mawuyacin hali, musamman ganin yadda makarantu suka lalace, babu kayan aiki; babu malamai kwararru; sukan su malaman ba sa zuwa aiki a kan lokaci, sai lokacin da suka ga dama suke koyarwa, harkokin ilimi a wancan lokacin suna neman wargajewa, amma zuwan wannan gwamnati abubuwa da dama sun gyaru, domin mun yi aiki ba dare ba rana har sai da komai ya koma muhallinsa na asali.
Jama’ar gari da malamai sun fahimci ina muka dosa, sun fahimci aikinmu na da muhimmanci, aiki ne da yake da burin kawo ci gaban ilimi a daukacin jihar.
Burina
Buri na shi ne in ga yaran Jihar Jigawa sun zama zakaru a fagen ilimin zamani, in ga sun rika gogayya da sauran jama’ar duniya a fannin ilimi, kuma ina da burin bude makaranta mai zaman kanta, domin in taimaka wa ’ya’yan talakawa su samu ilimi kyauta, ba ni da burin da yawuce in ga ilimi ya inganta.
Matsaloli
Ban taba samun matsalar da na kasa magance ta ba, yayana ya taimaka mini sosai, shi ne ya jajirce har na cim ma burina na rayuwa musamman na bangaren karatu, kuma tun da duk wani abu da na zama ta dalilin karatun ne.

Sha’awa
kyale-kyalen kayan duniya bai rufe mini ido ba, kuma ba sa burge ni, abin da nake sha’awa shi ne in yi wa kasata da jihata abin da zai sa a samu ci gaba mai amfani, kuma na fi sha’awar in ci tuwo miyar kuka.
Abin da ya fi damu na
Abin da ya fi damu na shi ne, in ga wani yana lalaci wajen gudanar da ayyukansa, ba na son mutane malalata. Na fi son mutane masu kwazo, wadanda ke kokarin neman abin kansu, musamman wadanda suke da kokari wajen neman ilimi, domin ilimi shi ne kashin bayan kowace rayuwa.
Nasarori
Na samu nasarori masu yawa musamman daliban da na yaye a yanzu sun zama manya mutane a fannoni daban-daban na rayuwa,  wasu sun zama injiniyoyi, wasu lauyoyi, wasu likitoci, wasu kuma manyan malamai a makarantun kasar nan.
Gudunmuwa
Na taimaka wa marasa karfi musamman marayu da ’ya’yan talakawa, yanzu haka akwai ’ya’yan marasa karfi da marayu da nake daukar nauyin karatunsu a makarantu daban-daban, kuma ina yi ne don Allah.
Shawara ga iyaye
Shawarata ga iyaye ita ce, su rika ba karatun ’ya’yansu musamman ma mata muhimmanci, su fahimta yanzu duniya ta canza babu wani abu da ke tafiya sai da ilimi. Su gane idan ’ya’yansu suka yi ilimi za su gudanar da rayuwarsu cikin sauki, sannan za a samu al’umma tagari.
Na biyu, mata su tashi tsaye wajen yin sana’a ko da a cikin gida ne, talauci babban ciwo ne, yana haddasa hassada da gaba da kuma kawo saurin fushi.