Hajiya Salima Makama: Burina matan Arewa su tsaya da kafafunsu

Hajiya Salima Makama ita ce Manajin-Daraktar Kamfanin gine-gine na Shelter Plus da ke Abuja. Tana noma da kiwo da kuma kasuwanci. Ta yi digirinta a kan aikin lauya, ta shawarci ‘yan Arewa su rike al’adunsu da mahimmmanci, ta ce burinta matan Arewa su tsaya da kafafunsu. Tarihin RayuwataBismillahir Rahmanir Rahim, sunana Salima Makama, an haife […]

Hajiya Salima Makama: Burina matan Arewa su tsaya da kafafunsu

????????????????????????????????????

Hajiya Salima Makama ita ce Manajin-Daraktar Kamfanin gine-gine na Shelter Plus da ke Abuja. Tana noma da kiwo da kuma kasuwanci. Ta yi digirinta a kan aikin lauya, ta shawarci ‘yan Arewa su rike al’adunsu da mahimmmanci, ta ce burinta matan Arewa su tsaya da kafafunsu.

Hajiya Salima MakamaTarihin Rayuwata
Bismillahir Rahmanir Rahim, sunana Salima Makama, an haife ni a Jos, Jihar Filato. Mahaifiya ita ce Hajiya Asabe ‘yar Duba-gari Farinwata da maihaifina Alhaji Muhammad Sani Mutawakil. Na fara makarantar firamare ta Township a Jos inda na yi zuwa aji biyar. Daga nan na dawo Minna, Jihar Neja na karasa, daga nan sai Kwalejin Horon Malamai mata (WTC) a Minna. A cikin ikon Allah daga nan kawai sai na wuce jami’a, a cikin shekarar 1977, amma kafin wannan lokacin sai da na halarci makarantar share fagen shiga jami’a, bayan na ci jarrabawa sai aka ba ni karatun aikin lauya. Na kammala jami’a a 1981, daga nan na je Legas na yi makarantar koyon aikin lauya (law school) daga 1981 zuwa 1982. An rantsar da mu (call to bar) a 1982. Na yi hidimar kasa  a Legas 1982 zuwa 1983. Na ci gaba da zama da maigidana a Legas har na haifi dana na farko da kuma ‘yata ta farko. Na yi aikin majistare na wani lokaci kadan a Bidda.
Bayan mun dawo Kaduna sai na yi aikin gwamnati kadan inda na bar aikin gwamnati a 1989. Bayan na yi ritaya sai na koma noma da kasuwanci da sauransu. Yanzu kuma ina da kamfanin gine-gine mai suna Shelter Plus Nig. Ltd da ke Abuja. Mukan sayi fili mu gina sannan mu sayar, ko kuma a ba mu kwangilar gini.  Ina da kuma kamfanin lauyoyi mai suna Salima and Co. da kuma kamfanin Umruk Nig. Ltd. na shigo da atampa da ake kira Husra.
Abin da ba zan manta da shi ba lokacin da nake karama
 Akwai abubuwan kuruciya da mutum ba zai taba mantawa da su ba musamman ma da a yanzu abubuwa suka tabarbare. A gaskiya mun ji dadin rayuwarmu. Mun yi zaman lumana da mutunci da makwabtanmu. A lokacin za ka iya shiga kowane gida ka ci ka sha babu tsangwama. Bayan mun dawo daga makarantar boko, sai ta allo, sai kuma mu yi ta tsalle-tsallenmu. Amma yanzu abin ba haka yake ba, rikicin yau daban na gobe ma daban.
Halayen da na koya daga iyayena
Mahaifina ba ya wasa da aiki, shi ne ya sa idan za ka tuna duk abubuwan da nake yi ba na rago ba ne, domin na yi gini da noma da kasuwanci. Mahaifinmu ya hana mu roko inda ya ce duk mai ba-ni-ba-ni zai kammala rayuwarsa cikin kaskanci. Mahaifiyarmu ba ta yarda mu raina na gaba da mu ba, ta kuma ce duk abin da za mu fada mu fadi gaskiya.
Shawara ga mata
Shawarata ga mata musamman ma ‘yan matan Arewa ita ce, su sani kowa ya bar gida, to gida ma zai bar shi. Muna da al’ada mai kyawu da fasali, don haka babu wani abu na waje da za a kawo mana ya fi namu fasali. Kuma duk yadda za ka koyi al’adar wani ba za ka taba zama shi ba, kama da wane ba wane ba ne, masu magana sun ce rabon kwado ba ya hawa sama. Na biyu, mata su daina sa ido, su nemi na kansu. Su rika sana’a, ba a kunya a neman halal.
Shawara ga matan aure
Na hadu da mutane da yawa maza da mata, sau da yawa wadansu mazan mukan tattauna da su inda suke fada mini sun bar iyalinsu a gida, amma wani abu da matan aure shi ne ba su taba yarda da babu ba, kowace mace sai dai ta ce a ba ta idan ba a samu ba ta rika fushi. Ya kamata idan mace tana da hali ta rika taimaka wa mijinta. Don haka ya kamata su rika tausaya wa mazajensu, su ma maza su rika dagewa wurin sauke nauyin iyalinsu da ya rataya a kansu.
kalubale a wurin aiki
Na fara aikin gwamnati sai na bari, dalilin da ya sa na bar aikin gwamnati kuwa shi ne, bayan na kammala jami’a na ci burin yin aiki da gaskiya amma sai na ga hakan ba zai yiwu ba saboda wadansu matsaloli. Daga nan na yanke shawarar na dogara da kaina, kuma Allah Ya taimake ni har zuwa yanzu.
Yadda nake taimaka wa jama’a
Na fi mayar da hankali wurin karatu, nakan sa a binciko mini yaran da iyayensu ba su da hali, ko kuma marayu sai na rika biya musu kudin makaranta. Baya ga haka na dauki mutane aiki a kamfanonina.

Shawara ga mutanen arewa
Idan har za mu yi amfani da albarkatun kasarmu a nan Arewa babu wanda zai ci gaba da daga mana yatsa ko kuma ya ce mu cima-zaune ne, sannan talaucin da ya mamaye mu zai zo karshe. Abin da ya sa na ce haka shi ne, a watan Maris da ya gabata mun yi taron kasa a Abuja a kan yadda ake sarrafa kade. Taron ya hada da ‘yan kasar Amurka da Birtaniya da Jamus da kasashen Afrika da sauransu. Wannan taron sai ya bude mini idanu na gane cewa Allah Ya albarkaci Arewa, domin wannan kade da ake rububinsa a Arewa kadai ake samunsa a Najeriya, kuma ba shuka shi ake yi ba kuma yakan yi shekara 300. Idan ya nuna sai ya rika fadowa da kansa. Za ka same shi tun daga Ilorin zuwa Neja har zuwa Sakkwato. Abin takaicin shi ne an bar shi ya lalace, yanzu misali a dauki dubu 30 a ba mata uku, a nuna musu irin wanda ake so da yadda ake sarrafawa. Mata za su samu abin yi, haka bangaren zogale da ake rububinsa a kasashen waje. A ce kansila a yankinsa ya ba mata kudi su rika nomansa. A shirye nake wurin ba da gudunmawata ga duk wanda zai dauki nauyin horar da mata hanyoyin sarrafa kade da zogale da sauransu.
Burina
Burina Arewa ta yi fice a kasar nan, mu wayi gari Arewa ta fita daga cikin talauci. Muna da yawan jama’a a Arewa, zan yi farin ciki idan na tashi na ga ana sarrafa albarkatun kasar Arewa. Fatana na wayi gari na ga an bar roko a Arewa, idan ka ga wani yana roko ma za ka iya marinsa saboda ta tabbata lalacinsa ya yi yawa. Mu fahimta ba daga koyon al’adar wani ne za mu ci gaba ba. Mu duba Indiya da China duka tufafinsu suke sanyawa amma sun ci gaba, don haka mu duba abin da muke da su mu gyara ba wai mu rusa su ba.
kungiya
Ina da kudurin a samu mata masu dan abin hannu sai mu hada kudi mu shiga kauyuka, idan mun shiga sai mu fahimci albarkatun kasar da suke wurin sai mu taimaka wurin samar musu da aikin yi ta hanyar sarrafa wadannan albarkatun kasar. Babu mamaki idan gwamnatocin jihohin suka ga mun yi haka sai su tashi tsaye, ka ga da haka sai komai ya inganta. Saboda ina da yakinin ba za ka ce wa mutum yi kaza ba kawai ya yi, amma idan ya ga ka yi kuma aka samu nasara cikin sauri shi ma zai yi.
Amfanin da karatun lauya wurin taimaka wa mata
Ban yi ba kasancewar ban dade a wannan bangaren ba na dogara da kaina, amma duk da haka nakan ba da shawararin da suka dace.

DAGA LARABA: Hanyoyin Dawo Da Martabar Karatun Tsangaya

Fitaccen ɗan kasuwar Kebbi, BLB ya rasu yana da shekara 54

Zaɓen Ondo: Ɗan takarar PDP ya garzaya kotu

Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni — Sarkin Musulmi