Hajiya Talatu Falke: Burina in rika taimakon addini

Hajiya Talatu Falke mai shekara 80, ta dauki tsawon lokaci wajen taimakon makaratun Islamiyya da kuma jama’a. Ta yi fice wajen taimakon makarantun Islamiyya a Jihar Legas. Ta ce burinta ta rika taimakon addini Musulunci, sannan ta bukaci matasa da mata su rika karatun addini da na zamani, sannan ta hori jama’a da abar zaman […]

Hajiya Talatu Falke: Burina in rika taimakon addini
Hajiya Talatu Falke: Burina in rika taimakon addini

Hajiya Talatu Falke mai shekara 80, ta dauki tsawon lokaci wajen taimakon makaratun Islamiyya da kuma jama’a. Ta yi fice wajen taimakon makarantun Islamiyya a Jihar Legas. Ta ce burinta ta rika taimakon addini Musulunci, sannan ta bukaci matasa da mata su rika karatun addini da na zamani, sannan ta hori jama’a da abar zaman banza.

Tarihin rayuwata
Assalamu alaikum, sunana na ainihi Zainab Alasan danbaba, amma an fi sanina da Hajiya Talatu Falke. An haife ni a unguwar Gabari da ke cikin Jihar Kano kimanin shekaru 80 da suka wuce. Amma da aka haife ni ban fi kamar wata uku ba aka zo da ni nan Legas. Iyayena a birnin Ikko suka fara zama, daga bisani suka dawo Agege da zama. Saboda haka kusan rayuwata a Agege na yi ta. Na yi aure a Agege na haifi ’ya’ya takwas da jikoki 29. Abin da zan iya tunawa lokacin ina karama shi ne, rayuwa tana da sauki babu tashin hankali. Ban yi karatun boko ba, amma na yi karatun addini daidai gwargwado. Saboda kwazona mahaifina yake sona sosai a cikin ’ya’yansa. Ni ce na fara sauke Alkur’ani a cikin ’ya’yan mahaifina.
Taimakon jama’a
Gaskiya ba yabon kai ba ni mace ce mai kwazo a wajen karatun addinin musulunci da kuma bayar da duk abin da Allah Ya hore mini wajen taimakon addini. Tun ina karama nake da sha’awar karatun addinin Muslunci, domin ko bayan an yi min aure na haifi ’ya’ya, ina zuwa makaranta ina koyon karatu. Saboda haka ina so na ga makarantun Islamiya sun ci gaba a kodayaushe, shi ya sa nake taimaka musu. Ina ganin kwazona suka gani shi ya sa suka yanke shawarar karrama ni. Saboda haka ina mika godiyata ga Allah da kuma malaman makarantar Ulumul Arabiyya da suka karrama ni. Allah ne ya zabe mu aka ba mu wannan kyauta.
Na fuskanci taimakon su jihadi ne babba, saboda a wannan lokacin da muke ciki ba na yaki ba ne, ba a daukar takubba a je yaki, shi ya sa na ga cewa jihadin da ya rage mana shi ne mu yi amfani da karfinmu da dukiyoyinmu, wajen taimakon addinin musamman ilimin addinin Musulunci. Da har na fara siyasa sai na watsar na kama harkar taimakon addini gadan-gadan.
Dalilin watsi da siyasa
Gaskiya na lura yarana sun girma, kuma ba sa son in rika yin siyasa shi ya sa na yi watsi da ita, na kama harkar addinin Musulunci. Ina taimaka wa makarantun Islamiyya.
Rayuwar Legas yanzu da kuma da
Akwai bambanci sosai da zai ba mutum mamaki. Duk wanda ya yi rayuwa tun yana karami har ya kai shekaru 80 zai ga sauyin al’amura daban-daban. Kamar a da zamantakewa tsakaninmu da Yarabawa tana da kyau, suna girmama mu, mu ma muna girmama su, don ko da wadanda ba Musulmi ba a cikinsu idan bikin kirsimeti ya zo suna ba mu abinci. Kuma tare muke wasanni, tare muke mu’amala da komai da komai. Amma a yanzu akwai bambanci da yawa kowa ta kansa yake yi. A da akwai amana a tsakani da adalci har auratayya ake yi.
Burina
Abin da nake so na cim ma shi ne, in ci gaba da taimakon makarantun Islamiyya da masallatai. Don ko masallacin da nake zuwa a unguwar Zango muna taimakawa wajen sayen katako na makabarta har asusu na kafa na taimakon masallaci na bangaren mata.

Matsalar Tsaro
To abin da yake faruwa A Najeriya sai dai mu ce inna lillahi wa inna ilaihir raji’una. An shiga wani hali sai dai mu ce Allah Ya kiyaye. Idan ka duba abin da yake faruwa a yankunanmu na Arewa. Tsaro ya tabarbare, kullum sai kashe jama’a ake yi, ana zubar da jini. Wannan abu ya yi muni, an shiga halin ha’ula’i, muna rokon Allah Ya kawo saukin lamarin. Don a kullum hankalina a tashe yake, ba na jin dadin tashin hankalin da ake yi. Saboda haka ina ba da shawarar mu hada kai gaba daya, domin rashin hadin kai ne ya janyo wannan abu. Mu yi watsi da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, mu zama tsintsiya madaurinki daya.
Tafiye-tafiye
Ba na tafiye-tafiye. Ban taba zuwa ko’ina ba sai Saudiyya domin yin aikin hajji. Ina za ka a yanzu yadda shekaru suka yi nisa, ni in ba mahaifata ta Arewa ba ba na zuwa wani wurin.
Abinci
Da dai da muke da cikakkiyar lafiya babu abin da ba na ci, amma yanzu da gairma ya zo kuma cututtuka suka yi yawa na fi cin abincin da zai kara mini lafiya, kamar acca da wake da kwai da kifi da kuma kuskus.
Shawara ga matasa
Ina janyo hankulansu su zauna da kowa lafiya, su rika ba manya girmansu. Wannan zai ba mutum kwarjini. Sannan su zama masu hakuri da juriya da gaskiya da rikon amana. Hakuri ya fi komai, a rika taimakon juna da tausayin juna, saboda haka sai a samu zaman lafiya.
Karramawa
Shawara da zan ba su shi ne, duk Allah muke bautawa, kuma Annabi Muhammadu shi ne jagoranmu. Da ’Yan Izala da ’yan darikar duk da shi muke takama. Saboda haka mu hada kawunanmu mu bauta wa Ubangijin da ya halicce mu.Mu kyautata wa Musulmi da wadanda ba musulmai ba.
Shawara ga mata
Ya kamata mata su rika karatu na addini da na boko, su fahimta rayuwa ba ta yiwuwa da ka, sai ana da ilimi. Su kuma rika sana’o’i domin ba zaman banza ba zai tsinana musu komai ba.