Hajiya ‘Yardada Maikano Bichi: Gemu ba ya hana Ilimi

Hajiya ‘Yardada Maikano Bichi ita ce Shugabar Hukumar Kula da Ilimin Manya ta Jihar Kano.   A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana muhimmancin da ilimi  ke da shi a rayuwar dan Adam, musamamn  mace.  A cewarta gemu ba ya hana ilimi, don haka ne suka fito da wani shiri na musamamn na ilimintar da ma’aikatan gwamnati […]

Hajiya ‘Yardada Maikano Bichi: Gemu ba ya hana Ilimi

Hajiya ‘Yardada Maikano Bichi ita ce Shugabar Hukumar Kula da Ilimin Manya ta Jihar Kano.   A tattaunawarta da Aminiya ta bayyana muhimmancin da ilimi  ke da shi a rayuwar dan Adam, musamamn  mace.  A cewarta gemu ba ya hana ilimi, don haka ne suka fito da wani shiri na musamamn na ilimintar da ma’aikatan gwamnati da na kamfanoni da ‘yan kungiyoyi da ba su da ilimi za su ilmanta.

Hajiya Yardada Maikano Bichi

Tarihin rayuwa:
An haife ni a garin Zakirai a karamar Hukumar Gabasawa a Jihar Kano. Kasancewar mahaifina dan karamar Hukumar Bichi ne sai na koma Bichi inda na taso a can har na yi karatuna na firamre. Bayan na kammala sai na ci gaba da karatuna na sakandare a garin Kano. Na yi digirina na farko a bangaren Ilimin manya a Jami’ar Bayero Kano. Daga nan sai na samu aiki a wanann hukuma  mai kula da ilimin manya ta Jihar Kano a shekarar 1979.

Aikace-aikacen da ta yi:
Na rike mukamai da dama a wannan ma’aikata tun daga kan malamar makaranta inda na koyar a Cibiyar bayar da ilimin manya ta garin Bichi, daga nan sai na koma cibiyar ta kofar Nassarawa a matsayin firinsifal. Daga nan sai aka mayar da ni hedikwatar wannan hukuma inda na rike mukamai da dama har zuwa lokacin da na bari a 2004. A shekarar 2004 ne wata kungiya ta Compass ta kasar Amurka (USAID) ta dauke ni aiki na shekara biyar. Ina tunanin komawa aikin gwamanti sai kuma wata kungiyar ESPIN ta kasar Ingila DFID ta dauke ni wani aikin. Ina cikin wannan aiki ne mai girma Gwaman Kano Dokta Abdullahi Umar Ganduje ya ba ni mukamin Babbar Sakatariyar a wannan hukuma mai kula da ilimin manya a shekaar 2015

Nasarori:
Tsawon shekarun da na dauka ina aiki a wannan ma’aikata ina mai alfaharin  cewa na koyar da manya ilimin zamani da na Islamiyya da na sana’o’i. Ba karamin al’amari ba ne ilimintar da dimbin mutanen da ba zan iya bayar da kiyasunsu ba. A lokacin da nake aiki a wannan ma’aikata an ba ni Kodineta mai kula da ilimintar da mata ta hanyar kula da lafiyarsu musamman a shekarun haihuwa. Mun koyar da mata yadda za su kula da kansu a lokacin da suke da ciki da yadda za su yi renon ‘ya’yansu da kuma yadda za su bai wa ’ya’yansu tarbiyya a matsyainsu na iyaye. Na rike matsayin Pokal Person na Asusun kula da yara na Majalisar dinkin Duniya (UNICEF).  A wanan lokaci mun yi kokarin bude wa alamjirai bangaren ajujuwan a cikin tsangayarsu inda muka koyar da su ilimin boko.  Haka kuma mun yi nasara wajen koyar da yara masu talla inda muke koyar da su a dandalin tallarsu ba. Koyarwar da muka yi musu a wanann lokaci ta ba su dama sun samu ilimi a matakin farko wasu daga cikinsu ma a yanzu sun dora neman ilimi a mataki na gaba inda suka ci gaba da karatunsu.
A wasu lokuta mun yi kokarin koyar da mata sana’o’i tare da ba su jari, duk a kokarinmu na ilimintar da ‘ya’yansu. A lokuta da dama za ki ji iyaye mata suna korafin cewa idan suka sanya ‘ya’yansu makaranta to wa zai yi musu talla, haka ya sa muka yi tunanin sama wa iyayen sana’o’i don su kyale ’ya’yansu su je makaranta su sami ilimi. Ni  kaina na kan bayar da tallafi ga ire-iren makarantun da ake budewa don ilimintar da manyan mutane da ba su yi karatu a farkon rayuwarsu ba.
Tarihi ya nuna cewa a farkon bude irin wadanann makarantu inda aka bude da mata 60, wadanda kuma mafi yawasnu zawarawa ne Amma Alhamdulillahi yanzu za mu iya cewa mun samu nasarar ganin a yanzu wanann cibiya tana da dalibai mata da yawansu ya kai 1,040 kuma yawancinsu matan aure. A lokuta da dama mazansu ne ke zuwa suna nema musu gurbin karatu. Alahamdulillah wannan nasara ce babba.

kalubale:
Babu shakka an fuskanci kalubale iri-iri a lokutan gudanar da aiki. Wani kalubale da ba zan manta da shi ba shi ne a lokacin da aka fito da shirin koyar da yara a tsangayun makarantun allo, bayan mun yi kokarin shawo kan malaman alamajiran sun yarda za mu rika zuwa muna koyar da wadanan yara ilimim zamani a tsangayunsu, sai bayan mun tafi mun dawo sai ki ga malamin ya nuna rashin amincewarsa a fili, inda yake nuna cewa kamar wani wayo aka shiryo don a kwace masa makaranta da sauransu. Mun yi fama da wannan matsala kafin daga karshe mu iya sake shawo kan malaman su yarda su amince mana.

Wane aikace aikace hukumarku ke yi?:
Saboda muhimmancin da ilimi ke da shi ga rayuwar al’umma ya sa a kullum muke kokarin ganin manya musamam mata wadanda ba su samu damar yin karatu a shekarun kuruciya ba a yanzu sun samu. Kamar yadda manuafr kafa wanann ma’aikata don wayar da kan al’umma su san muhimancin ilimin su zo su nemi ilimin na addni da an zamani da kuma na sana’aoi. ya kasance A wannan ma’aikata mukan ilimintar da mutane a matakai da dama tun daga kan mataki na farko.  Haka kuma idan ana tashi bayani akan ce kashi 80 na al’umarmu ba su da ilimin zamani, hakan ya sa wanan hukuma ke kokarin ganin al’umma ta ilmanta. A yanzu haka an samu canji kasancewar mazaje sun fahimci cewa idan mata suna da ilimi sukan samu sauki wajen tarbiyyantar da iyali da kuma maigidan gaba daya. Maza suna bai wa matansu goyon baya wajen samun wannan ilimi.  Haka kuma anan mukan nuna wa mata muhimmancin ilimi. A wannan lokaci gwamnati tare da hadin kan hukumarmu ta fito da shiri na bayar da ilimi ga ma’aikatan kamfanoni da kungiyoyi da ma’ikatan gwamnati wadanda ba su samu ilimi a matakin farko ba. Da kuma bayar da dama ga wadanda suka samu ilimi a matakin farko don su samu damar ci gaban iliminsu.
A yanzu haka shirye-shirye sun kammala game da yadda za mu samar da ajujuwa hudu-hudu a kowace karamar hukuma don ilimintar da manya a matakin farko. Haka kuma a mataki na biyu na ci gaba da karatunsu za mu bude ajujuwa takwas-takwas don wadanan dalibai a kowace karamar hukuma da ke Jihar Kano don kada abin da suka koya a matakin farko ya ruguje. Muna sa rai kuma kowane aji za a samu dalibai da yawansu yakai 40 insha Allah.
A yanzu haka jami’anmu da ke cibiyoyinmu na kananan hukumomin Knao sun gama tattaro bayanai game da daliban da za su ci moriyar wannan tsari. Gwamnati kawai muke jira ta ba mu damar fara aiwatar da shirin.

Iyalli:
Na yi aurena na farko kuma na haifi ‘ya’ya bakwai. daya daga ciki ta rasu a yanzu haka shida ne suka rage wadanda dukkaninsu sun yi karatun zamani a nmatakai daban-daban tun daga kan digiri da masu NCE da kuma mai diploma. Hudu daga cikinssu sun yi aure sun hayayyafa. Sai dai a yanzu haka ina tare da mijina na biyu Alhaji Isa Umar Kura.

Buri:
Burina ya danganci aikina.   Ina fatan na g  cal’ummar Jihar Kano ta ilimanta tun da ilimi shi ne ginshikin ci gaba dan adam. Ina ganin ya zama wajibi mu bayar da gudumamwarmu don al’ummarmu ta iliminta. Abin da ya sa na fi damuwa da ilimin manya shi ne sai mutum yana da ilimi sanann zai iya bai wa  ’ya’yansa ilimi tare da sanin muhimamncin ilimin. Idan al’umma ta iliminta babu wanda zai bace.  Idan za ki iya tunawa a zaben da aka gudanar a shekarar 2015 an bayyana cewa an samu kuri’a sama da miliyan da ta lalace. Babu abin da ya jawo hakan sai rashin ilimi. Da mutanen da suka sa kuri’a suna da ilimi ba za su bar ta ta lalace ba, don sun je wajen zaben nan da niyyar kadawa mutanen da suke ra’ayi kuri’a amma a karshe saboda rashin ilimi suna ji suna gani kuri’asu ta lalace a banza.
Na biyu ina fatan na ga matsalolin tatalin arziin kasa ya inganta, domin dukkanin kudurin da gwamnati ke da shi idan ba kudi to fa babu abin da gwamnati za ta iya yi. A wanann gaba ce nake amfani da wannan dama wajen yin kira ga jama’a da mu yi hakuri mu rika biyan haraji, kasashen waje da muke shawa’a suke kuma kawo mana tallafi gwamnatinsu na yi musu komai na rayuwarsu ne ta hanyar kudin harajin da suke biya.

Abin da take son a tuna ta da ni:
An kafa wannan hukuma shekaru 36 da suka wuce. A yanzu ina kokari na ga an yi wa dokar da ta kafa wanann hukuma kwaskwarima. Shekarun da yawa don haka akwai bukatar a samar da canje-canje a ciki. Ina fatan a wayi gari a tuna da ni wata rana a matsyain wace ta tabbatar da gyaran dokar wanann hukuma insha Allah.

Mutane abiin koyi:
Akwai wata mata mai suna Dokta Judth tana da kungiya DRC, wannan mata tana daga cikin mutannen da nake kwaikwayo a tsarin tafiyar da rayuwata. Matar nan ta dora ni akan tafarkin yin aiki don al’ummata ta hanyar sadaukar da kai ba tare da la’akari da abin da zan samu ko abin da zan zama ba. Alhamdulillahi da na bi shawararta na ci riba a rayuwata, domin ga shi yanzu bayan hidimtawa jama’a da muka yi muna cin moriyar abin.

Shawara ga mata:
Babbar shawarar da zan bai wa mata ‘yan uwana shi ne su dage da neman ilimi. Ina kuma horonsu da su nemi sana’a don tallafawa kansu da
‘ya’yansu wani lokacin har da maigida. Haka kuma ina shawartar mata musamman wadanda mazajensu ko iyayensu suka ba su damar zuwa irin cibiyoyin hukumarmu don samin ilimi, da su yi amfani da lokacinsu wajen dagewa da yin abinda ya kai s  na samun ilimi da kuma tsare mutuncinsu. Idan an tashi makaranta su koma gida kamar yadda aka tsara, ba wai su tafi yawo a gari ba. A takaice ina rokonsu da su zama sun tarbiyyantu da dabi’u masu kyau, hakan zai sa su zama abin koyi a tsakanin al’umma.
Ina kira ga ire-iren wadanda ba su iya sanya ‘ya’yansu a makaranta su yi kaokarri wajen ganin sun sanya ’ya’yansu makarana.  Idan mutum ba shi da ilimi to nan gaba ko magana a cikin mutane ba zai iya ba. Haka kuma ina kira ga al’umma musamman wadanda ba su da ilimi su sani cewa har yanzu dai ba su makara ba akwai sauran lokaci da za su iya zuwa ire iren cibiyoyinmu don koyon ilimin addni da na boko da kuma na sana’o’i.