Hajiya Zainab Audu Bako: Gaskiya da rikon amana su ne tushen nasara
Hajiya zainab Audu Bako, ita ce ‘yar auta ga tsohon gwamnan mulkin soja na Jihar Kano, marigayi Kwamishinan ‘yan sanda Alhaji Audu Bako. Hajiya Zainab ta kasance shugabar gidan da ake kula da namun daji na Jihar kano , sannan ta samu karin girma zuwa mukamin Kwamishinar Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha. Aminiya ta samu tattaunawa […]
Hajiya zainab Audu Bako, ita ce ‘yar auta ga tsohon gwamnan mulkin soja na Jihar Kano, marigayi Kwamishinan ‘yan sanda Alhaji Audu Bako. Hajiya Zainab ta kasance shugabar gidan da ake kula da namun daji na Jihar kano , sannan ta samu karin girma zuwa mukamin Kwamishinar Ma’aikatar Kimiyya da Fasaha. Aminiya ta samu tattaunawa da ita tare da jin yadda aka yi har ta tsunduma cikin harkokin siyasa da kuma dalilanta na zama ’yar siyasa wadda a dan lokaci kadan ta zamo tauraruwa. Ga kuma yadda tattaunawar ta kasance:
Tarihin Rayuwa:
Sunana Zainab Audu Bako, kuma ni ce ‘yar auta cikin ’ya’yan mahaifinmu marigayi Alhaji Audu Bako. An haife ni ranar 25 ga watan Janairun shekarar 1967 a Kaduna kuma an haife ni ba dadewa ne sai aka nada mahaifinmu matsayin gwamnan mulkin soja na tsohuwar Jihar Kano tun da lokacin ana hade ne da Jihar Jigawa.
Na tashi a gidan gwamnati inda kuma muka rika samun karatun Alkur’ani daga wani malaminmu wanda yake zuwa har gidan gwamnati yana koya mana karatu sai dai ba zan iya tuna sunansa ba a halin yanzu tun da ina karama kwarai.
Na shiga makarantar Kano Capital kafin in koma wata makaranta ta sakandare da ke Bompai amma kafin mu kammala wannan makaranta sai mahaifinmu ya rasu kuma daga nan ne karatunmu ya samu matsala tun da babu mai daukar nauyi. Amma cikin ikon Allah, sai mijin yayata watau marigayi Alhaji Sale Jambo ya ci gaba da daukar nauyin karatuna har zuwa Turai, amma daga bisani nan ma karatun ya sake samun tangarda saboda nauyi ya yi wa wanda yake kula da ni yawa inda kuma na dawo gida Najeriya.
Bayan na dawo gida sai na yi aure inda na haifi ’ya’ya 4 da miji na kafin shi ma Allah Ya yi masa rasuwa, kuma daga nan sai na kama wasu harkoki na neman dogaro da kai domin rike yara da daukar dawainiyarsu ta yau da kullum, wanda hakan ta sanya na kafa wata karamar masana’anta ta yin kek da sauran kayan abinci na alfarma tunda ina da ilimi kan harkar girke-girke da na’ura mai kwakwalwa.
Daga bisani ne na sake aure kuma ina zaune tare da maigidana lafiya har ma mun aurar da ‘yata ta fari wadda na haifa da mijina da ya rasu, wannan shi ne kadan daga cikin tarihina.
kalubalen Rayuwa:
Na fuskanci kalubale na rayuwa tun daga mutuwar mahaifinmu Alhaji Audu Bako, domin gaskiya rashin sa ya sanya mun fahimci cewa ya yi kokari wajen daukar dawainiyar iyalinsa kuma cikin matukar adalci, Allah Ya gafarta masa da daukacin Musulmin duniya baki daya.
Duk wanda ya san tarihin mahaifinmu ya tabbatar cewa mutum ne mai tausayi da adalci ba don mahaifina ba ne, amma kowa ya yarda cewa Audu Bako shugaba ne mai gaskiya da sanin yakamata sai dai an gaza samun wadanda suka taimaki gidansa duk da irin bauta wa al’uma da ya yi a zamanin yana gwamnan Kano. Har yanzu ayyukansu suna nan ana cin moriyar su tun shekaru masu tsawon gaske, amma ba a cika waiwayar iyalinsa ba balle ma a ce za a taimake su ta kowane fanni na zamantakewa.
Tun rasuwarsa muke rayuwa cikin hakuri da daidaita al’amuranmu bisa halin da muka samu kammu, sannan muna sane da cewa mahaifinmu ya yi abin da ya kamata dan Adam ya yi na taimakawa al’uma amma ba a cika waiwayarmu ba kan harkokin rayuwa ko makamantan haka.
Dalilin Shigata Siyasa:
Kasancewata ’yar gwagwarmayar rayuwa tun da muka samu kammu cikin maraicin mahaifin mu, na yi kokari na kafa masana’anta ta yin dinki da harkokin abinci wanda da shi ne nake rike kaina da mahaifiyata da kuma ’yan uwa har da abokan arziki wadanda ake tare tun dadewa, kuma na yi wa wannan kamfani rajista tun cikin shekara ta 1998 kuma har ayyuka nake samu daga wasu wurare kuma Alhamdulillahi muna dogaro da kai ta wadannan harkoki nawa. Sunan kamfanina na dinki shi ne Zainab Tailoring Serbices bayan kamfanin yin kayan abinci na alfarma watau catering serbices, wadannan harkoki nawa sun rike mu ba na zuwa wajen kowa neman taimako ganin yadda al’amura suka zama.
Wata rana ina kwance ni kadai sai sha’awar siyasa ta fado min a rai, nan take na je na shaidawa ’yan uwana cewa zan shiga siyasa har wasu suna ganin kamar ba zan iya ba, ganin yadda na fi kowa kyamar siyasa ga mata a kasar nan.
Sai na tafi gidan daya daga cikin iyaye a gareni watau Alhaji Tanko Yakassai, inda na samu uwargidansa Hajiya Rabi Tanko na bayyana mata abin da yake tafe da ni kuma ta yi murna kana ta shiga wajensa ta sanar da shi abin da ke tafe da ni nan ma ya yi murna kuma ya shawarce ni da in shiga jam’iyyar Muhammadu Buhari ita ce al’umma suke bukata duk da cewa shi dan PDP ne. Nan take ya hada ni da Sanata Rufa’i Sani Hanga lokacin ana CPC inda shi kuma ya hada ni da Alhaji Ahmadu Haruna Zago shi kuma ya dauke ni tamkar ‘yar sa kuma dukkan abubuwan da ake yi na siyasa da ni ake yi har dai tafiya ta yi nisa na samu mukami a shugabancin jam’iyyar ta CPC har kuma aka hade zuwa jam’iyyar APC.
Na yi kokarin yin takarar majalisar wakilai kuma har ma na ci zaben fidda gwani amma aka yi wasu abubuwa marasa dadi kuma aka baiwa wani takarar duk da cewa ni ne na ci zaben share fage amma aka juya lamarin har ta kai ga na shigar da kara gaban kotun sauraron kararrakin zabe ina kalubalantar yadda aka hana ni tikiti.
Duk da haka dai ina cikin mutane da suke yi wa jam’iyya aiki har ma wata rana na bukaci jam’iyyar APC ta karbi ragowar wasu kudi mallakar jam’iyyar CPC a matsayinata ‘yar kwamitin kudi ta jam’iyyar amma aka ce in ci gaba da rike su har dai na ci gaba da kokarin cewa sai an karbe su inda daga karshe aka karba har ma aka shaidawa maigirma tsohon gwamnan Kano kuma Sanatan Kano ta tsakiya Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso cewa ga wata yarinya ta dawo da wasu kudi dubu 50 na jam’iyya.
Gwamna ya ji dadin wannan abu kuma ya yaba mun kwarai, ina tunanin wannan abu ne ya sa maigirma Sanata ya kirani gidan gwamnati ya ce da ni mun kira ki ne domin mu baki shugabancin gidan namun daji na Kano wanda da ma ku ne kuka samar da shi. Nan take sai na yi salati har gwamna ya ce ko ba kya son wannan aikin?, sai na ce masa ai farin ciki ne ya same ni da na ji an ba ni shugabancin gidan namun daji domin gaskiya an karrama gidan Audu Bako matuka. Domin akwai wani zaki da a halin yanzu yake gidan tun yana karami yake kwanciya kusa da ni a gidan gwamnati, kuma ga shi an tura ni in kula da su, wannan abu ya yi mun dadi kwarai har ma da daukacin zuri’ar gidan Alhaji Audu Bako, kuma ko shakka babu ba za mu manta da Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ba har abada.
Ina gidan namun daji sai wata rana aka ce in je gwamna yana kirana, na dauka wani laifi nayi domin ya je gidan da yammacin wannan rana ni kuma sannan na fita bai tarar da ni ba, sai nake tunanin ko laifi na yi, ina zuwa wajen a a ofis sai ya ce mun kira ki ne domin mu yi maki karin girma, mun nada ki Kwamishiniyar ma’aikatar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano.
Nan ma sai na yi kabbara Allahu Akbar, sai ya sake cewa ko ba kya son wannan aikin? Ni kuma na ce masa farin ciki ne ya yi mun yawa maigirma gwamna kuma zan yi bakin kokarina cikin yardar Allah in ga na yi abin kirki. Babu shakka mu dai a zuri’ar gidan Audu Bako, babu wanda ya yi wa iyalinsa halacci kamar yadda Kwankwaso ya yi mana, kuma da yardar Allah za mu ci gaba da kasancewa masu godiya gare shi.
Abubuwan da suka fi ba ni sha’awa:
Akwai abubuwa wadanda suka ba ni sha’awa, amma babu kamar yadda maigirma tsohon gwamnan Jihar kano Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi mana mu iyalan marigayi Alhaji Audu Bako. Don haka gaskiya muna godiya kuma muna yi masa addu’a ta fatan alheri. Sannan muna godiya ga Alhaji Tanko Yakassai da Sanata Rufa’i Sani Hanga da Alhaji Ahmadu Haruna danzago saboda daukata d a suka yi tamkar ‘yar da suka haifa.