Hajiyar Jihar Kebbi ta rasu a Makkah

Hajiya Maryamu ta rasu ne a Asibitin Sarki Abdulazeez da ke birnin Makkah sakamakon doguwar jinya

Hajiyar Jihar Kebbi ta rasu a Makkah

Yadda ‘yan dubban mutane kalilan suka gudanar da Aikin Hajji a bara. Reuters

Jihar Kebbi ta kara rasa daya daga cikin alhazanta da suka gudanar da aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya.

A yayin da ake ci gaba da kwaso alhazan Najeriya zuwa gida, zuwa yanzu yawan alhazan Jihar Kebbi da suka rasu a Hajjin bana ya karu zuwa mutum biyar.

Adadin ya karu ne sakamakon rasuwar Hajiya Maryamu Suleman Mayalo daga Karamar Hukumar Maiyama a ranar Lahadi.

Hajiya Maryamu ta rasu ne a Asibitin Sarki Abdulazeez da ke birnin Makkah sakamakon rashin lafiya.

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kebbi, Faruk Musa Inabo, ya bayyana cewa, kafin rasuwar Tata, Hajiya Maryamu ta jima tana fama da rashin lafiya.

Faruk Musa Inabo, tare da Gwamna Nasir Idris sun mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayiyar tare da addu’ar Allah Ya sanya ta a Aljannatul Firdaus.

Najeriya ta rasa kimanin alhazai 20 daga cikin sama da 1,300 da suka rasu a aikin Hajjin bana, wanda mutane sama da miliyan 1.8 suka gudanar.