Hajiyar Najeriya mai shekara 66 ta rasu bayan kammala Aikin Hajji
Aminiya ta ruwaito cewa an tsinci gawar marigayiyar a banɗaki.
Wata dattijuwa mai shekara 66 daga cikin alhazan Najeriya ta rasu, washegarin ranar da alhazan kasar suka fara komawa gida bayan kammala Aikin Hajjin bana.
Wata abokiyar zaman dakin su dattijuwar ce ta tsinci gawar marigayiyar a banɗaki a lokacin da ta je kama ruwa.
- Bidiyon Dala: Ganduje ya yi martani kan sammacin hukumar yaki da rashawa
- Malamar jinya ta yi ta bakin aikinta bayan lalata da marar lafiya a Birtaniya
Kawo yanzu ’yan Najeriya kimanin 15 ne suka rasu daga cikin alhazai sama da miliyan 1.8 da suka yi Aikin Hajjin bana.
Marigayiya Alhaja Kuburat Sekoni daga Karamar Hukumar Oshodi, an riga an yi mata jana’iza a yayin da alhazai daga sassan duniya ke ci gaba komawa kasashensu bayan kammala Aikin Hajji a kasa mai tsarki.
Da yake tabbatar da rasuwar, Amirul Hajj na Jihar Legas, Anofiu Elegusi, ya ce sun mika gawar Alhaja Kuburat Sekoni ga Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON), kafin daga bisani aka yi mata janaza.
Game da musabbabin rasuwar, Anofiu ya ce sun riga suna kan tuntubar hukumar NAHCON “saboda ita ke da hurumin tattaunawa da Ma’aikatar Lafiya ta Ƙasar Saudiyya, domin bincike da kuma sanar da musabbabin rasuwar,” wadda ta auku a ranar Laraba.
Ya ce da zarar hukumomin sun kammala aikin za a sanar da sakamakon abin da bincike ya gano.
Amirul Hajj din ya bayyana kaduwar Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Jihar Legas da rasuwar Alhaja Sekoni, yana mai rokon Allah Ya rahamshe ta.
Wakilinmu ya yi kokarin samun karin bayani daga shugaban tawagar likitoci na hukumar NAHCON, Dokta Usman Galadima domin jin inda aka kwana, amma kiran wayar likitan ba ta shiga ba, haka kuma bai amsa sakon da muka tura masa ba har zuwa lokacin da aka kammala hada wannan rahoton.