Hajj 2022: Dalilin rashin tashin maniyyata daga Filin Jirgin Jos
Filin jirgin saman da ke Jos ya yi wa jiragen da aka ba su jigilar alhazai kankanta.
Maniyyata aikin Hajjin bana daga Jihar Filato ba za su samu tashi daga Babban Filin Jirgi na Yakubu Gowon da ke Jos ba, zuwa Kasa Mai Tsarki.
Hukumar Kula da Jin Dadin Alhazai ta Jihar Filato ta ce maimakon haka, za ta yi jigilar maniyyata ne daga Filin Jirgi na Tafawa Balewa da ke Bauchi.
- An kwakule idon wani karamin yaro a Bauchi
- INEC ta cire sunan Ahmad Lawan daga jerin ’yan takarar 2023
- Ekweremadu na iya fuskantar daurin rai-da-rai a Birtaniya
Sakataren Hukumar, Barista Auwal Abdullahi, ya bayyana wa wakilinmu a ranar Asabar cewa, “Ba zai yiwu a yi jigilar maniyyatan Jihar Filato ta Filin Jirgi na Yakubu Gowon da ke Jos ba a aikin Hajjin 2022.
“Dalili kuwa shi ne titin jirgin da ke filin jirgin na Jos ya yi wa manyan jiragen sama samfurin Jumbo Jet da aka ba su aikin jigilar maniyyata kankanta, don haka ba za su iya tashi ta Jos ba.”
Ya bayyana cewa, “Jirage masu daukar mutum 550 zuwa 600 ne aka bai wa aikin jigilar maniyyata a bana, kuma titin sauka da tashin jirgaren Babban Filin Jirgi na Jos ya yi musu kankanta.
“Duk da cewa filin jirgin ya kai matakin na kasa da kasa, amma yana bukatar a kara fadada shi yadda zai iya daukar manyan jirage; yanzu haka ana shirye-shiryen yadda Ma’aikatar Sufurin Jiragen Sama ta Tarayya za ta zo a yi aikin.
“Ma’aikatar da Gwamnatin Jihar Filato sun samu fahimtar juna a kan dalilin da ba za a iya jigilar maniyyana daga filin jirgin ba a wannan karon.