Hajj 2023: Kamfanonin jirage da NAHCON sun daidaita kan jigilar maniyyata

NAHCON ta ce kamfanonin jirgi na cikin gida sun amince sun sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar maniyyata da suka ki amincewa da farko. 

Hajj 2023: Kamfanonin jirage da NAHCON sun daidaita kan jigilar maniyyata

Hukumar Aikin Hajji a Kasa (NAHCON) ta daidata da kamfanonin jiragen sama hudu na cikin gida da aka ba wa kwangilar jigilar maniyyata a aikin Hajjin da ke tafe.

Bangarorin sun daidaita ne bayan a makon jiya kamfanonin sun ki sanya hannu kan yarjejeniar aikin saboda yakin kasar Sudan da ke bukatar su sauya hanyar jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya, lamarin da zai kara wa afiyar tsawo.

A kan haka ne wakilan kamfanonin suka ki sanya hannu kan yarjejeniyar aikin, bisa hujjar cewa karin sawon tafiyar zai kara yawan kudaden da za su kashe, don haka suka bukaci karin kudin jigilar maniyyatan.

Amma, shugaban hukumar, Hassan Zikrullah Hassan, ya ce, a zaman da aka sake yi ranar talata a ofishinn NAHCON da ke Abuja, kamfanonin — Aero Contractors da Air Peace da Azman Air da kuma Max Air — sun amince sun sanya hannu kan yarjejeniyar da suka ki amincewa da farko.

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja