Hajj 2026: Alhazan Jigawa sun yaba da ciyarwa da kulawar lafiyarsu a Makkah

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan alhazan Jigawa suna cikin ƙoshin lafiya, yayin da jami’an hukumar ke ci gaba da wayar musu kai domin kauce wa faɗawa hannun bata-gari da masu damfara a Saudiyya.

Hajj 2026: Alhazan Jigawa sun yaba da ciyarwa da kulawar lafiyarsu a Makkah

Alhazan Jihar Jigawa da ke gudanar da aikin Hajjin bana sun yaba game da kulawar lafiya mai kyau da kuma ingancin abincin sau uku da Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihar take ba su Kasa Mai Tsarki.

Wasu daga cikin alhazan da suka isa birnin Makkah sun bayyana cewa kulawar da jami’an lafiya ke bayarwa tana zuwa ba tare da ɓata lokaci ba, kuma tana taimakawa musamman ga tsofaffi da masu fama da gajiya yayin gudanar da ibada.

Wani alhaji daga Ƙaramar Hukumar Dutse, Ahmad Muhammad ya bayyana yadda ya kamu da rashin lafiya yayin gudanar da ibadarsa, amma cikin ɗan lokaci jami’an lafiya suka ba shi taimako.

A cewarsa, da isarsa wurin likitocin tawagar Jigawa, nan take suka yi mishi gwaje-gwaje tare da ba shi magungunan da suka dace.

“Na ji jikina ya yi rauni sosai har na kasa ci gaba da yin Ɗawafi. Amma da na je wurin jami’an lafiya, suka kula da ni sosai, suka ba ni magani, cikin ɗan lokaci na samu sauƙi na ci gaba da Ɗawafi da sauran ayyukan ibada,” in ji shi.

Ahmad ya kuma yi wa hukumar addu’a bisa ƙoƙarinta na tabbatar da walwala da lafiyar alhazan jihar baki ɗaya.

Shi ma wani alhaji mai suna Lawan Ilu ya yaba bisa yadda jami’an kiwon lafiya suke ba marasa lafiya kulawa cikin lokaci.

Ya ce bayan ya kamu da rashin lafiya, sun duba shi suka ba shi magunguna kuma ya samu sauƙi cikin ƙanƙanin lokaci.

“Nan take suka kula da ni. Magungunan da suke bayarwa suna da inganci sosai, mutum da ya sau ɗaya ko biyu zai ji sauƙi,” in ji Lawan Ilu.

Wata tsohuwa daga cikin alhazan jihar wadda ta buƙaci a sakaya sunanta, ta bayyana yadda ta shiga mawuyacin hali sakamakon rashin lafiya a Makkah, amma kulawar da jami’an lafiya suka ba ta taimaka sosai.

“Lokacin da na kamu da rashin lafiya na yi tunanin zan mutu saboda yadda jikina ya yi rauni. Amma likitoci da nas-nas ɗinmu sun kula da ni sosai. Alhamdulillah yanzu na samu lafiya kuma na ci gaba da Ɗawafi da sauran ibadu,” in ji ta.

Rahotanni sun nuna cewa mafi yawan alhazan Jigawa suna cikin ƙoshin lafiya, yayin da jami’an hukumar ke ci gaba da wayar musu kai domin kauce wa faɗawa hannun bata-gari da masu damfara a Saudiyya.

Wasu daga cikin alhazan sun kuma yaba da yadda ake samar musu da abinci sau uku a rana cikin tsari da kulawa.

Masu lura da al’amuran Hajji sun bayyana cewa irin wannan kulawar ta taimaka matuƙa wajen ƙara wa alhazan ƙwarin guiwa domin su mayar da hankali kan ibadunsu a Ƙasa Mai Tsarki.