Hajji: 15 ga watan Mayu za a fara jigilar maniyyata

Maniyyata kimanin 65,000 ne za su sauke farali daga Najeriya, inda ake sa ran za su yi akalla kwana hudu a Madina domin yin Ziyara, kafin fara aikin Hajji

Hajji: 15 ga watan Mayu za a fara jigilar maniyyata

Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeria (NAHCON), Jalal Arabi. (Hoto: Twittter/NAHCON)

Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya (NAHCON) ta sanar cewa ranar 15 ga watan nan na Mayu za a fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya.

Shugaban NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, ne ya sanar da haka a taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah da ke gudana a Abuja a safiyar Alhamis.

Jalal Arabi ya ce a bana maniyyata kimanin 65,500 ne za sauke farali daga Najeriya, inda za su shafe akalla kwanaki hudu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji.

Shugaban hukumar ya bayyana cewa za a y jigilar maniyyata ne daga cibiyoyi 10 a fadin Najeriya.

 

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos

Kasuwar Laranto da ke Jos ta yi gobara