Hajji 2022: Hajiya Aisha ta zama mahajjaciyar Najeriya ta farko da aka rasa
Allah Ya yi wa daya daga cikin mahajjatan Najeriya daga Jihar Nasarawa, Hajiya Aisha Ahmed, rasuwa a ranar Talata.
Allah Ya yi wa daya daga cikin mahajjatan Najeriya daga Jihar Nasarawa, Hajiya Aisha Ahmed, rasuwa a ranar Talata.
Rahotanni daga Saudiyya sun ce Hajiya Aisha ta kwanta dama ne bayan fama da rashin lafiya wanda hakan ya sa aka dauke ta zuwa Asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makka inda a nan ta cika.
- NAJERIYA A YAU: Tasirin kawancen NNPP da ‘Labour Party’ a zaben 2023
- Dabbobin Layya da ranaku 10 na farkon Zul-Hajji
Tuni dai aka yi jana’izar marigayiyar ranar Talata bayan sallar La’asar bisa tsarin addinin Musulunci.
Sakataren Hukumar Alhazai na Jihar Nasarawa, Malam Idris Ahmed Almkura, ya tabbatar da faruwar hakan.
Wata majiya ta kusa da marigayiyar ta shaida wa Aminiya cewa a makon jiya ne Hajiya Aisha suka bar Najeriya zuwa Saudiyya don sauke farali, sai ga shi Allah Ya yi mata cikawa a Talata.
Da wannan, Marigayiya Aisha ta zama ta farko da aka rasa daga mahajjatan Najeriya a aikin Hajjin bana.
Aisha ’yar asalin Jihar Nasarawa ce daga Karamar Hukumar Keffi.