Hajji 2022: Rukuni na biyu na maniyyata 550 na shirin tashi a Neja

Za mu kwashi maniyyatan kananan hukumomi takwas daga Jihar Neja.

Hajji 2022: Rukuni na biyu na maniyyata 550 na shirin tashi a Neja

Hukumar Alhazai ta Jihar Neja ta ce, ta kammala shiri don jigilar rukuni na biyu na maniyyata su 550 zuwa Kasa Mai Tsarki don sauke farali.

Babban Sakataren Hukumar, Alhaji Umar Maku ne ya bayyana hakan ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya a Minna, babban birnin jihar.

Sakataren ya ce, maniyyatan da za a kwasa a yanzu sun fito ne daga kananan hukumomin Kontagora da Suleja da Rafi da Lavun da Rijau da Shiroro da Agaie da kuma Agwara.

Ya kara da cewa, wannan shi ne rukunin maniyyata na biyu daga jihar wanda jirgin Max Airline zai kwashe su daga Babban Filin irgin Sama na Abuja zuwa Saudiyya.

Haka nan, ya ce rukunin farko na maniyyatan jihar su 560 sun riga sun isa Kasa Mai Tsarki don Hajjin bana.

Hukumar ta ce tana ci gaba da yin bakin kokarinta wajen tabbatar da an kwashe duka maniyyatan jihar zuwa kasa mai tsarki.

(NAN)