Hajji 2025: Kamfanin Saudiyya zai maka Najeriya a Kotun Duniya
Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya ya ba wa Hukumar NAHCON wa’adin kwana 20 ya cika alkawarin yarjejeniyar kwangilar da suka rattaba hannu a kai

Farfesa Abdulahi Usman Saleh, Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya NAHCON
Kula da walwalar maniyyatan Najeriya ya shiga tangal-tangal bayan wani kamfanin kula da alhazai na kasar Saudiyya ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Hukunta Manyan Laifuka na Duniya (ICC), kan saba yarjejeniyar kwangilar aikin Hajji.
Kamfanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na kasar Saudiyya, wanda Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) da Hukumomin Jin Dadin Alhazai na Jihohin suka ba wa kwangilar kula da alhazan Najeriya a aikin Hajjin 2025, ne ya yi barazanar, yana mai zargin Najeriya da yaudarar sa.
Mashariq Al Dhahabiah Al-Mutawazi ya yi barazanar maka Najeriya a Kotun Duniya ne bisa zargin Hukumar NAHCON da karya yarjejeniyar da suka kulla kan aikin kula a alhazan, musamman a Mina da Filin Arfa.
A wata wasika da ya aike wa Shugaban Ofishin Aikin Hajjin Najeriya da ke birnin Makkah a kasar Saudiyya a ranar Litinin 17 ga watan nan na Fabrairu, 2025, kamfanin ya zargi NAHCON da saba yarjejeniyar da suka kulla cewa kanfaninsu ne kadai hukumar za ta wa kwangilar aikin a bana, musammana a Mina da Arafah.
- NAJERIYA A YAU: Ci-gaban Da Hukumomin Raya Shiyyoyi Za Su Samar
- Dattijon Neja Delta Edwin Clark ya rasu
Daga nan sai ya ba wa hukumar kwana 20 ya koma kan sharudan yarjejeniyar da suka rattaba hannu a kai, idan ba haka ba ta maka hukumar a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC).
Binciken wakilinmu ya gano a ranar 17 ga watan Janairu ne kamfanin da NAHCON suka rattaba hannu kan yarjejeniyar kula da alhazan Najeriya a Kasa Mai Tsarki.
Amam daga bisani Kungiyar Hukumomin Jin Dadin Alhazan Jihoi suka daga kara cewa Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdullahi Usman Saleh, ya yi gaban kansa wajen soke yarjejeniyar, kwanaki kadan kafin cikar wa’adin biyan kudi ga kamfanonin da kasashe suka ba wa aikin.
Farfesa Abdullahi Usman Saleh dai ya musanta yin gaban kansa wajen soke yarjejeniyar, yana mai cewa hukumomin Saudiyya ne suka yi.
Ana zargin NAHCON ta raba aikin gida biyu tsakanin Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi da kuma kamfanin Ikram Diyafa kafin cikar wa’adin ranar 14 ga watan Janairu da hukumomin Saudiyya suka sanya.
Mashariq Al Dhahabiah Al Mutawazi na zargin NAHCON da ba shi aikin kula da alhazai 26,287, duk kuwa da cewa hukumar ta sanar cewa ta samu tantunan alhazai 52,544 da za su gudanar da aikin Hajjin, wanda hakan ke nufin hukumar ta ba wa daya kamfanin aikin kula da ragowar alhazai 26,257 ke nan.
Kamfanin ya bukaci zama na gaggawa da mahukuntan NAHCON kan lamarin domin yanke shawara kan mataki na gaba da za a dauka.
Wakilinmu ya yi iya kokarinsa domin samun martanin hukumar NAHCON a game da wannan dambarwa, amma abin ya faskara.