Hajji 2026: An sanar da ranar fara jigilar maniyyatan Katsina
Daraktan ya ce, za a fara jigilar maniyyatan daga ranar Litinin 11 ga watan Mayu, 2026 daga filin jirgin sama na Umaru Musa da ke Katsina wanda kamfanin jiragen Max Air zai yi kamar yadda aka saba duk shekara.
Kamar yadda Babban Daraktan Hukumar Jin daɗin alhazan jihar Katsina Alhaji Yunusa Dankama ya shaida a wani taron masu ruwa da tsaki dangane da shirye-shiryen ɗaukar maniyyatan jahar domin zuwa sauke farali.
Daraktan ya ce, za a fara jigilar maniyyatan daga ranar Litinin 11 ga watan Mayu, 2026 daga filin jirgin sama na Umaru Musa da ke Katsina wanda kamfanin jiragen Max Air zai yi kamar yadda aka saba duk shekara.
Daraktan ya ce, za a gama jigilar maniyyatan a cikin ranaku uku a tsakanin 11 da 12 da 13 ga wata.
Jigilar za a yi ta ne a tsakanin jirage 4, wato, jirgin farko a ranar Litinin sai jirage 2 a ranar Talata yayin da jirgi na ƙarshe zai tashi ranar Laraba.
Jihar ta Katsina na da maniyata 2035.
Alhaji Yunusa Dankama ya ja hankalin maniyatan da su kiyaye dokoki tun daga nan gida har zuwa ƙasa mai tsarki.
“Aikin an tsara shi bisa ga yadda ita ƙasar ta Saudiya ta bayar da umarnin a yi, wato, za a raba maniyatan zuwa tawaga-tawaga ta mutum 45 waɗanda duk abin da za a yi masu a haka za a nemi.
Shiga mota ce, wajen masauki ne da sauran su. Kowace tawaga tana da jagora wanda hakan zai kawo sauƙin aiwatar da abubuwa cikin sauƙi.
Sannan maniyyaci ya sani, muddin aka ce ga jirgin da zai tafi to lallai ya yi ƙoƙarin zuwa a cikin lokaci ba mutum ya ce, shi sai jirgi na gaba ba. Duk jirgin da zai tashi tuni an miƙa sunayen mutanen da zai ɗauka ga ita ƙasar.
Samun akasi na iya janyowa maniyaci fuskantar wani hukunci. Kun san kuma su ba kamar mu ba ne. Don haka a kiyaye”.