Hajji Bana: Maniyyata 1,031 sun gaza samun kujera a Zamfara

Kwamitin Tantance Maniyyata Aikin Hajjin na Jihar Zamfara, ya ce kimanin maniyyata 1,031 ba za su samu zuwa aikin Hajjin bana daga jihar saboda karancin kujera.Shugaban kwamitin kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Wakkala Muhammad ya bayyana haka a lokacin da ya kira taron manema labarai a karshen mako jiya.Shugaban ya ce gwamnatin jihar ta […]

Hajji Bana: Maniyyata 1,031 sun gaza samun kujera a Zamfara
Hajji Bana: Maniyyata 1,031 sun gaza samun kujera a Zamfara

Kwamitin Tantance Maniyyata Aikin Hajjin na Jihar Zamfara, ya ce kimanin maniyyata 1,031 ba za su samu zuwa aikin Hajjin bana daga jihar saboda karancin kujera.
Shugaban kwamitin kuma Mataimakin Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Wakkala Muhammad ya bayyana haka a lokacin da ya kira taron manema labarai a karshen mako jiya.
Shugaban ya ce gwamnatin jihar ta samu bayani daga Gwamnatin Tarayya cewa a bana maniyyata dubu hudu da 71 ne kawai aka yarda su tafi aikin Hajji daga jihar, alhali maniyyata dubu biyar da 102 ne suka biya kudin kujera daga jihar, har an riga an duba lafiyar wasu daga cikinsu, kafin su samu wannan bayani.
“Don haka ba yadda za mu yi dole muka rage mutum dubu daya da 31 muka ba su hakuri,” inji shi.
Ya ce lokacin da suka samu wannan umarni suka ga babu abin da ya dace sai dai su bi sunayen wadanda suka biya kudin don fitar da wadanda suka gama biya a yi amfani da su, saura kuma sai su zo su karbi kudinsu ko su yi hakuri sai badi idan Allah Ya kai mu su tafi.