Hajji: Gwamnatin Jigawa ta bai wa kowane maniyyaci kyautar miliyan ɗaya
Gwamnatin ta bayar da tallafin ne domin rage wa maniyyatan jihar radadin karin kudin kujerar aikin hajjin bana.
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi ya bai wa maniyyata jihar kyautar Naira miliyan daya kowannensu, biyo karin kudin kujerar aikin hajjin bana.
Wannan na cikin wata sanarwa da jami’in hulda jama’a na Hukumar Jin Dadin Alhazai na Jihar, Murtala Usman Madobi ya fitar, a madadin shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo.
- Tinubu zai halarci bikin rantsar da sabon shugaban kasar Senegal
- An Dakatar Da Shugabar APC A Kaduna Kan Caccakar Uba Sani
Sanarwar, ta ce gwamna Namadi ya yi la’akari kan yadda krin kudin ya zo wa maniyyatan a daidai lokacin da wasu daga cikinsu suka kammala biyan kudadensu, ba tare da tsammanin samun karin ba.
Idan ba a manta ba, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Kasa (NAHCON) ce, ta sanar da karin kudin aikin hajji bana, daga Naira miliyan hudu da doriya zuwa Naira miliyan 8.3.
Tuni wasu da suka biya kudadensu suka fara neman hukumar ta dawo musu da kudinsu domin zuwa aikin hajjin ya fi karfinsu.
Karin dai ya janyo cece-kuce a tsakanin ’yan Najeriya, inda mutane ke ganin bai dace a ce kudin ya yi irin wannan tashin gwauron zabin ba.
A gefe guda kuma, Gwamnatin Tarayya, ta bayyana tashin farashin dala a matsayin makasudin abin da ya haifar da tashin kudin kujerar zuwa aikin hajjin.
Kazalika, gwamnatin ta ce ta biya tallafin akalla Naira biliyan 90 domin nema wa masu zuwa aikin hajjin na bana sauki.