Hajjin 2023: An bukaci maniyyatan Abuja su fara biyan N2.5m
Hukumar ta ce wadanda suka riga zuwa su za a fara yi wa rijista.
Hukumar Alhazai ta Birnin Tarayya ta umarci maniyyata Hajjin bana daga yankin da su biyan Naira miliyan biyu da rabi kafin Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta bayyana cikakken kudin kujerar da za a biya.
Cikin sanarwar da hukumar ta fitar ta bakin Daraktanta, Muhammad Nasiru Danmallam, ta ce za a biya kudin ne a cikin asusun bankin hukumar sannan a kai mata takardar shaidar biya.
- Wata daya kafin zabe, Kotu ta haramta wa Elisha Abbo takarar Sanata a APC
- ‘Buhari zai kaddamar da jirgin saman da aka kerawa a Najeriya kafin ya bar mulki’
Nasiru ya ce za a yi wa maniyyata rajistar ne ta hanyar farawa da wadanda suka riga zuwa don kamanta adalci.
Ya ce kawo yanzu, hukumar ta yi wa maniyyata sama da kaso 40 cikin 100 na kason da ta samu a bara rijista.
Daraktan ya kara da cewa, hukumar ta karbi rabin kudin maniyyatan da suka soma biya duba da ingancin aikin da ta samu a lokutan baya.