Hajjin 2023: An dawo wa mahajjata 3,000 kuɗaɗensu a Kaduna

Hukumar ta ce duk wanda bai ga kuɗinsa, ya tuntuɓi jami’an rajistar ƙaramar hukumarsa don ƙarin bayani.

Hajjin 2023: An dawo wa mahajjata 3,000 kuɗaɗensu a Kaduna

Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kaduna, ta bayyana cewa sama da mahajjata 3,000 da suka yi aikin Hajjin 2023 sun karɓi ragowar kuɗinsu da ya yi saura.

Mai magana da yawun hukumar, Malam Yunusa Abdullahi ne, ya bayyana hakancikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar a Kaduna.

Ya ce hukumar ta karɓo kuɗaɗen daga Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON).

Ya ce kowanne mahajjaci ya samu Naira 61,080.

Ya kuma ce an tura wa kuowa kuɗinsa kai-tsaye zuwa asusun bakinsu.

“NAHCON ta mayar da waɗannan kuɗaɗen ne saboda matsalar katsewar wutar lantarki da ta faru a Mina, wanda ya shafi sanyaya wuraren kwana kuma ya haifar wa mahajjata tsaiko,” in ji shi.

Abdullahi, ya ce akwai wasu da ba su karɓi kuɗinsu ba saboda rashin bayar da cikakkun bayanan asusun bankinsu.

Ya bayyana cewa biyan zagaye na biyu zai fara a mako mai zuwa, don haka ya buƙaci waɗanda ba su karɓi kuɗinsu ba da su gaggauta bahar da cikakken bayani domin samun kuɗinsu a kan lokaci.

Ya kuma jaddada cewa dukkanin mahajjatan 2023 da ba su karɓi kuɗinsu ba, su tuntubi jami’an rajista a ofisoshin ƙananan hukumominsu domin ƙarin bayani.

Hakazalika, ya ce yayin da ake ci gaba da biyankuɗaɗen na 2023, hukumar ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin bana.

Hajjin 2023: An dawo wa mahajjata 3,000 kuɗaɗensu a Kaduna

’Yan sanda sun ceto mutum 23 da aka sace a Kaduna

Arsenal ta yi sukuwar salla a kan Man City da ci 5

Fasinjoji 30 sun ƙone ƙurmus a hatsarin mota a Ondo