Hajjin 2023: An yi wa maniyyatan Kano bitar aikin Hajji a aikace 

Hukumar ta gudanar da bitar aikin a aikace ga maniyyatan.

Hajjin 2023: An yi wa maniyyatan Kano bitar aikin Hajji a aikace 

Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano, Muhammad Abba Dambatta ya jagoranci jami’an hukumar domin koya wa maniyyata aikin Hajji a aikace a wani bangare na rufe bitar aikin Hajjin bana.

Babban Sakataren wanda kuma shi ne ya wakilici Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce an shirya taron ne da nufin kara ilimintar da alhazai don su fahimci ayyukan da ke kansu wajibi a yayin aikin Hajji.

“Ana fada wa alhazai irin ayyukan da za su gudanar lokacin aikin Hajji da baki kawai, hakan ya sa muka ga dacewar nuna musu yadda ake gudanar da aikin a aikace domin an ce gani ya kori ji,” in ji shi.

Babban Sakataren ya ce gwamnan jihar na taya maniyyata murna bisa zabo su da Allah Ya yi cikin Musulmin duniya domin sauke farali.

Ya kuma roke su da su zama wakilai nagari yayin gudanar sanna su yi addu’ar neman zaman lafiya da karuwar arziki a Kano da Najeriya gaba daya.

Kazalika, ya kaddamar da rabon kananan jakunkuna ga maniyyatan, inda ya bayyana cewa zuwa yanzu hukumar ta kammala samar da duk wasu abubuwa na bukata ga maniyyatan wadanda suka hada da kayan duba lafiya da allurar rigakafi da sauransu.

“A yanzu haka komai ya kammala, dibar maniyyata zuwa Kasa Mai Tsarki shi ne kadai abin da ya rage.

“Hukumar Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanya ranar 3 ga watan Yuni a matsayin ranar da maniyyatan Kano za su fara tashi.”

Maniyyata daga kananan hukumomi 44 ne suka halarci bitar aikin Hajjin a aikace.