Hajjin 2025: Ana shirya wa shugaban NAHCON maƙarƙashiya – Musa Iliyasu
Kwankwaso ya ce Pakistan yana da ƙwarewar da zai gudanar da aikin Hajjin 2025 cikin nasara.
![Hajjin 2025: Ana shirya wa shugaban NAHCON maƙarƙashiya – Musa Iliyasu Hajjin 2025: Ana shirya wa shugaban NAHCON maƙarƙashiya – Musa Iliyasu](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/IMG_20250212_112122.jpg)
Jigo a jam’iyyar APC a Jihar Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso, ya tabbatar da cewa Shugabancin Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan a Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ba zai gaza ba duk da ƙoƙarin yaɗa jita-jita da wasu ke yi.
Kwankwaso, ya musanta wani rahoto da ke cewa mahajjata na iya rasa zuwa aikin Hajjin 2025, inda ya bayyan cewar wannan ƙarya ce da aka shirya don yaudarar jama’a da kuma ɓata sunan shugaban NAHCON.
- An yi wa kashi 25 na matan Nijeriya kaciya
- Garkuwa da Mutane: An kama ɗan shekara 13 a wurin rajistar layin waya
Ya buƙaci jama’a, musamman maniyyatan da za su yi aikin Hajjin 2025, da su yi watsi da wannan rahoto, inda ya Farfesa Pakistan yana da ƙwarewa wajen shirya aikin Hajji.
“Muna sane da jita-jitar da ake yaɗawa cewa dubban maniyyata na iya rasa zuwa aikin Hajjjin 2025.
“Wannan ƙarya ce da ake ƙoƙarin amfani da ita don kawo cikas ga Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan,” in ji Kwankwaso.
Ya zargi ’yan adawa da ɗaukar nauyin wannan jita-jita saboda tsoron nasarar da Farfesa Pakistan zai kawo tare da sauyi a tsarin aiki. Hajji.
“Muna da masaniya cewa wasu mutane na yaɗa labarai marasa tushe don ɓata masa suna.
“Manufarsu ita ce kawo cikas ga mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, amma ba za su yi nasara ba,” a cewarsa.
Kwankwaso, ya kuma bayyana cewa NAHCON ba ta soke kowace kwangila ba, inda ya alaƙanta hakan da ƙasae Saudiyya.
Ya bayyana cewa Farfesa Pakistan yana ƙasar Saudiya don warware matsalar lokacin da aka yaɗa rahoton na ƙarya.
Ya kuma tabbatar wa maniyyata cewa za a gudanar da Hajjjin 2025 cikin nasara.
“Ina kira ga duk maniyyata da su kwantar da hankalinsu. Farfesa Pakistan ya samu wannan muƙami ne saboda cancantarsa.
“Kuma yana da ƙwarewar da za ta sa a samu nasara. Babu wani maniyyaci da aka yi wa rijista da ba zai samu damar tafiya aikin Hajji ba,” in ji shi.
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, shi ma ya bayyana cewa babu buƙatar mutane su shiga damuwa game da lamarin.
Ya kuma ya musanta zargin cewa kwangilar da aka bai wa wasu domin gudanar da aikin Hajjin bana na iya samu matsala.
Kwankwaso ya ƙarƙare da cewa waɗanda ke yaɗa jita-jitar suna ƙoƙarin hana gwamnati samun nasara ne, kuma a cewarsa burinsu ba zai cika ba.