Hajjin 2026: Gwamnatin Jigawa ta kammala shirye-shirye, an gargadi maniyyata kan bin dokoki
Ana sa ran fara jigilar maniyyata zuwa ƙasar Saudiyya cikin makonni masu zuwa.
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa, ta bayyana cewa ta kammala muhimman shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin 2026, inda ake sa ran jigilar kusan maniyyata 1,000 zuwa ƙasar Saudiyya domin sauke farali.
Babban Daraktan hukumar, Alhaji Umar Labbo ne, ya bayyana hakan yayin bikin rufe tarukan wayar da kan maniyyata da aka gudanar a dukkanin ƙananan hukumomi 27 na jihar.
- Mutum 19 sun rasu a hatsarin mota a Edo da Taraba
- Sojoji sun ceto mutanen da aka sace, sun lalata maɓoyar ’yan bindiga a Filato
Ya ce an shirya tarukan ne domin ilmantar da maniyyata yadda za su gudanar da ibadar Hajji cikin tsari daidai da koyarwar addini, tare da fahimtar sabbin dokoki da ƙa’idojin da hukumomin ƙasar Saudiyya suka shimfiɗa.
“A dukkanin ƙananan hukumomi 27 mun gudanar da tarukan horaswa domin tabbatar da cewa kowane maniyyaci ya samu cikakken bayani kan yadda zai gudanar da ibadarsa cikin sauƙi da tsari,” in ji shi.
“Muna ƙarfafa musu gwiwa da su kiyaye dokoki da ƙa’idoji tare da amfani da ilimin da suka samu daga malamai domin gudanar da aikin Hajji cikin nasara.”
Dangane da batun jigilar maniyyata, Labbo, ya ce ana ci gaba da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, ciki har da kamfanonin jiragen sama, domin kammala sauran shirye-shiryen, inda ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da ranar fara jigilar.
A nasa jawabin, Sarkin Dutse, Alhaji Muhammad Hameem Nuhu Sunusi, wanda shi ne Amirul Hajj na shekarar 2026, ya buƙaci maniyyata su yi amfani da wannan dama ta aikin Hajji wajen yi wa Najeriya da Jihar Jigawa addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba.
Ya kuma gargade su da su guji duk wani abu da zai saɓa wa dokokin ƙasar Saudiyya ko kuma ya ɓata martabar ibadar Hajji.
“Hajji ibada ce mai tsarki da ke buƙatar ladabi, haƙuri da bin doka. Ina kira ga maniyyata su zama jakadu na gari na jihar da ƙasa baki ɗaya,” in ji Sarkin.
Haka kuma, ya yaba wa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da jin daɗin maniyyata, tare da gode wa malamai da ke horas da su kan yadda ake gudanar da ibadar Hajji.
Shi ma da yake nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) a jihar, kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Dutse, Dakta Sibu Abdullahi, ya gode wa Allah da ya ba su damar kammala shirye-shiryen cikin nasara.
Ya yaba wa gwamnatin jihar bisa naɗa Sarkin Dutse a matsayin Amirul Hajj, yana mai cewa hakan alama ce ta girmamawa da mutunta masarautu.
Dakta Abdullahi, ya kuma jinjina wa malamai da suka sadaukar da kansu wajen horas da maniyyata tsawon shekaru.
“Tsawon sama da shekaru 30, malamai suna bayar da gudunmawa wajen ilmantar da maniyyata ba tare da cikakken albashi ba, amma duk da haka suna ci gaba da jajircewa. Muna matuƙar godiya da wannan sadaukarwa,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa ƙananan hukumomi ma sun bayar da tasu gudunmawa ga maniyyata, inda ya bayyana cewa maniyyata 72 daga Ƙaramar Hukumar Dutse sun samu tallafin Naira 20,000 kowannensu domin taimaka musu wajen sayen muhimman kayayyakin tafiya.
A ƙarshe, ya buƙaci maniyyata su riƙa yi wa ƙasa, jihar da al’ummominsu addu’a, musamman dangane da matsalolin tsaro da kuma zaɓukan da ke tafe.
“Muna roƙon maniyyata su yi addu’ar zaman lafiya da ci gaban Najeriya. Jigawa na daga cikin jihohin da ke da zaman lafiya, kuma muna son a ci gaba da hakan ta hanyar addu’a,” in ji shi.
Ana sa ran fara jigilar maniyyata zuwa ƙasar Saudiyya cikin makonni masu zuwa bayan kammala dukkanin shirye-shiryen da suka haɗa da jadawalin jirage da takardun tafiya.