Hajjin bana: Alhazai sun ‘jefi Shedan’ a Saudiyya

Ana Aikin ne yayin da ake fama da tsananin zafi a Saudiyya

Hajjin bana: Alhazai sun ‘jefi Shedan’ a Saudiyya

Alhazan da suke yin Aikin Hajjin bana a kasar Saudiyya a ranar Laraba sun gudanar da jifan Shedan.

Sama da alhazai miliyan daya da dubu 800 ne suke gudanar da Aikin a bana, adadi mafi girma tun bayan annobar COVID-19.

Bayan sun kwana a Muzdalifa jiya, yau da safe sun wuce zuwa wajen jifan Jamrori guda uku, kafin daga nan su koma Makkah su yi Dawafin Bankwana.

A shekarar 2019 dai, mutum miliyan biyu da rabi ne suka gudanar da aikin.

Bugu da kari, aikin na bana na gudana ne yayin da ake fama da tsananin zafin rana,

Alkaluman zafi dai a ranar Talata, ranar da alhazai suka yi tsayuwar Arfa, ya kai 48 a ma’aunin Celsius, kuma ana sa ran na ranar Laraba ya kai 47 a Mina.

Babu sojojin ƙasar waje a yankinmu —Sakkwatawa

Yadda dagacinmu ya sassara ni da adda — Maraya

Bidiyoyin da suka ɗauki hankalin ’yan Najeriya a 2024

An kama mutum 859 da ceto 46 da aka yi garkuwa da su a Filato – ’Yan sanda