Hajjin Bana: Ambasadan Najeriya ya yi gargadi kan safarar miyagun kwayoyi

Yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin Hajjin bana, alhazan Najeriya suka kama hanyar zuwa Minna, karamin Ambasadan Najeriya a Saudiyya ya gargadi ga alhazan a kan hadarin yin safarar miyagun kwayoyi da kuma yin wasu ayyuka marasa kyau da za su sanya su fuskanci fushin hukumomin Saudiyya. Lokacin da yake jawabi a […]

Hajjin Bana: Ambasadan Najeriya ya yi gargadi kan safarar miyagun kwayoyi

Yayin da ake ci gaba da gudanar da aikin Hajjin bana, alhazan Najeriya suka kama hanyar zuwa Minna, karamin Ambasadan Najeriya a Saudiyya ya gargadi ga alhazan a kan hadarin yin safarar miyagun kwayoyi da kuma yin wasu ayyuka marasa kyau da za su sanya su fuskanci fushin hukumomin Saudiyya.

Lokacin da yake jawabi a yayin wani taro da ya yi da alhazan Najeriya a Makka daf da fara shirye-shiryen hawan Arafa, karamin Ambasadan ya gargade su da kada wani ya kuskura ya yi yi mu’amala da miyagun kwayoyi saboda duk wanda aka kama da laifin za a yanke masa hukuncin kisa ne kamar yadda dokar kasar Saudiyya ta tanada.

Ya ce, yin mu’amala da miyagun kwayoyi a kasa Mai tsarki laifi ne babba kuma yana da matukar hadari, baya ga haka harka ce da ke zubar da mutuncin mutum da kuma kasar da ya fito.

Ambasadan ya hore su da su mayar da hankali kan ayyukan ibada kuma su dukufa wajen yi wa kansu da kasarsu addu’o’in samun zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin kasa.

Ambasada Yunusa ya hori jami’an shigi-da-fici su rika sanya ido wajen ganin babu wani alhaji da ya samu damar fita da wata kwaya ko duk abin da kasar Saudiyya ta hana a shiga da shi cikin kasarta. 

Ya ce idan jami’an suka mayar da hankali wajen sanya ido a filayen jiragen sama, hakan zai karfafa harkar tsaro da kuma daukaka martabar kasar nan a idon duniya.

Amasada Yunusa ya hori jami’an hukumomin alhazai na jihohi su rika wayar da kan alhazansu kan illar safarar miyagun kwayoyi da wasu kayayyakin da aka haramta shiga da su Saudiyya. Ya ce yin haka zai taimaka wa Hukumar Hana Tu’ammali da Miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da wasu hukumomi makamantanta wajen gudanar da ayyukansu.

Ambasadan ya yaba yadda Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON) take bullo da sababbin dabaru wajen gudanar da ayyukanta musamman a bangaren jigilar alhazai da kula da jin dadinsu. “Ya kamata mu yaba wa Hukumar NAHCON bisa namijin kokarin da take yi wajen jigilar alhazai da kula da jin dadinsu a shekarun nan,” in ji shi.