Hajjin Bana: An kammala jigilar alhazan Kaduna sama da 4,000

Jirgin Kamfanin Max Air ne, ya kwashe kashin ƙarshe na maniyyatan jihar.

Hajjin Bana: An kammala jigilar alhazan Kaduna sama da 4,000

Aƙalla maniyyata sama da 4,000 ne daga Jihar Kaduna da za su yi aikin Hajjin bana aka kammala jigilarsu a jihar.

Kashi na ƙarshe na maniyyatan sama da 300 sun tashi tare da Amirul Hajj na jihar, kuma Sarkin Lere, Injiniya Sulaiman Umar, da sauran jami’ai.

Jirgin Max Air, da aka ware ne don jigilar alhazan Kaduna ya kammala jigilar tasu.

A halin da ake ciki, Gwamna Uba Sani ya yaba wa jami’an hukumar jin daɗin alhazai,  bisa jajircewarsu wajen ganin an samu nasarar aikin hajjin 2024.

Ya buƙace su da su tabbatar da cewa alhazai sun samu kimar kuɗinsu a lokacin zamansu a ƙasar Saudiyya.

Amirul Hajji, ya miƙa saƙon yabon gwamnan ne, a lokacin da yake miƙa saƙon bankwana ga rukunin ƙarshe na alhazan jihar a sansanin alhazai da ke unguwar Mando ranar Litinin.

Ya ce, Gwamna Sani ya gode wa jami’an hukumar da suka samu matsuguni masu kyau ga maniyyatan, inda ya ce sauran jihohi sun yi koyi da hakan.

A cewarsa, hukumar ta kuma samu nagartattun masu bayaf da abinci, tare da haɗin gwiwar Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), waɗanda ke bayar da abinci mai kyau ga alhazai a Ƙasar Saudiyya.

Injiniya Umar, ya tunatar da maniyyatan cewa aikin Hajji ba wai tafiya ce kawai zuwa ƙasa mai tsarki ba, ibada ce da ya kamata a yi ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

Ya kuma yi kira ga alhazai da su bi umarnin masu wa’azi da jami’an aikin Hajji da su za su yi aikin hajji tare da su.

Har wa yau, ya ƙara da cewa kada su yi ƙasa a gwiwa wajen yin tambayoyi kan abin da ya shige musu duhu.

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai

Sojojin ruwa sun gina wa al’ummar Zariya asibiti kyauta