Hajjin Bana: Ana kukan targaɗe sai ga karaya
Har gobe aikin Hajji na daga cikin aikin da gwamnatoci kasar nan ke tutiyar cewa suna yi wa Musulmi sassaucinsa.
Da ma tun bayan kammala aikin Hajjin bara a taron farko da ya yi da shugabanni da sakatarorin hukumomin jin dadin alhazai na jihohi a Abuja, domin yin nazari a kan yadda aikin ya gudana, Shugaban Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) na lokacin, Alhaji Zikirullah Kunle Hassan ya ba da shelar cewa duk mai son tafiya aikin Hajjin bana, to ya fara ajiyar adashin gata da Naira miliyan 4.5.
Babban hanzarin da Alhaji Zikrullah ya bayar a lokacin shi ne maniyyatan bara sun biya kusan Naira miliyan 3.2 bisa ga canjin Dalar Amurka na gwamnati na Naira 450, yana mai karawa da cewa, amma zuwan wannan gwamnati ta Shugaban Kasa Ahmed Bola Tinubu, ta hade kasuwar canjin kudade wuri ɗaya, ba ta gwamnati bare ta bankuna, inda farashin Dala ya koma Naira 750 a kan kowace Dala.
Tun daga lokacin da Hukumar NAHCON ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin bana da neman kowane maniyyaci ya ajiye kafin alkalamin Naira miliyan 4.5, a takaicen takaitawa maniyyata sun biya Naira miliyan 4.9 da tsammanin sun gama ke nan, sai zaman jiran a sa masu ranar fara tashi zuwa Kasa Mai tsarki.
Kwatsam! A yammacin ranar Lahadin makon jiya, sai ga sanarwa daga Mataimakiyar Daraktar Yada Labarai ta Hukumar NAHCON, Hajiya Fatima Sanda Usara tana neman dukkan maniyyatan da suka biya wadancan kudade su gaggauta cika Naira miliyan 1.9 kafin ranar Juma’ar da ta gabata.
Don haka, wannan ya nuna kudin aikin Hajjin bana ya kai Naira miliyan 6.8 ke nan.
Hanzarin da Hajiya Usara ta bayar na wannan ƙari shi ne wai ƙasar nan ta samu tsaikon biyan kuɗaɗen maniyyata ga hukumomin kasar Saudiyya zuwa ranar 12-2-2024 da aka shardanta mata.
A cewarta, Gwamnatin Tarayya ta yi iyakacin iyawarta wajen ganin an samu ragi, amma ragin da aka samu ba zai kai ga dukkan wadanda suka yi rijista da hukumar su 48,418.
Kujeru 95,000 ƙasar Saudiyya ta kebe wa kasar nan a bana kamar bara, wanda a bara har kari aka rika nema duk da ana ganin kuɗaɗen tafiyar sun yi ɗan karen tsadar da ba su taba yi ba a tarihin zuwa aikin ibadar ga Musulmin ƙasar nan.
Ba ma wai ga waɗanda suka riga suka biya kuɗaɗen tafiyar tasu ba, hatta sauran Musulmi sun girgiza da jin irin yadda kuɗaɗen tafiya aikin Hajjin suka wuce hankali, suka kai Naira miliyan 6.8, yayin da waɗanda suke so su biya yanzu sai sun biya Naira miliyan 8.2, kafin a yi hawan Arfar bana da su in Allah Ya so.
Ganin haka ne da kuma kasancewar aikin Hajjin yana daga cikin shika-shikan Musulunci biyar da Allah (SWT) Ya ɗora wa bayinSa Musulmi kuma balagaggu masu hankali da lafiya da wadata su je aikin akalla sau daya a rayuwarsu, ya sa malaman addini da kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa-da-tsaki suke ta kiraye-kiraye ga Shugaban Kasa, Ahmed Bola Tinubu da gwamnonin jihohi, har ma da kananan hukumomi da lallai su kawo dauki ga maniyyatan bana.
Suna masu kafa hujja da cewa, dukiyar ta kasa ce kuma maniyyatan in sun je suna iya yi wa kasa da shugabanninta addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da karuwar arziki da kuma neman Allah Ya yaye mana mawuyacin halin da muke ciki.
Bayan wannan sanarwa, tuni wasu maniyyata masu sukuni a jihohi daban-daban suka fara yin cikon, yayin da waɗanda ba su da hali suka nemi hukumomin jin daɗin alhazai na jihohinsu su mayar masu da kudadensu, suna masu fatan in Allah Ya kai mu badi da rai da lafiya su je aikin ibadar.
Amma kuma a zaman amsa kiraye-kirayen da aka yi ta masu, tuni wasu gwamnatocin jihohi suka fara bayyana yadda za su taimaka wa maniyyatansu.
Alal misali, gwamnatin Jihar Kano ta bakin Darakta Janar na Hukumar Jin Dadin Alhazai, Alhaji Laminu Rabi’u Danbaffa ta tabbatar da cewa, Gwamnan Jihar Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da tallafa wa kowane maniyyaci daga jihar da tsabar kudi har Naira dubu 500.
Alhaji Laminu ya ce, yanzu maniyyatan jihar da suka riga suka biya Naira miliyan 4.9 su 2,096 ne gwamnatin jihar za ta biya masu Naira biliyan 1.048, amma duk mai son ya biya sabon kuɗin aikin Hajji sai ya biya Naira 8,454,464.74 lakadan ba ajalan ba.
Daga Jihar Bauchi mai maniyyata 1,652 da suka biya Naira miliyan 4.9 gwamnatin jihar ta bakin Kwamishinan Kula da Al’amuran Addinai, Alhaji Yakubu Ibrahim Hamza ta ba da shelar za ta tallafa wa maniyyatan da rabin karin kudin, kwatankwacin Naira 959,000, wanda jimilla ya kai Naira biliyan 2.86.
A jihohin Kogi da Ribas, gwamnatocin cewa suka yi maniyyatan su sha kuruminsu, domin gwamnatocin za su biya masu dukkan karin da Hukumar NAHCON ta yi.
Haka dai labarin yake nan da can, inda kowace jiha ke faɗin gwargwadon abin da za ta iya tallafa wa maniyyatanta.
Na san kuma sauran jihohin da ba a ji amonsu ba, za a ji nan ba da jimawa ba.
Kodayake an ce tuni Gwamnatin Tarayya ta sa nata tallafin a aikin Hajjin bana, wanda in ban da ta biya wadancan makudan kuɗaɗe tuntuni ga kasar ta Saudiyya ba, da cikon da maniyyatan za su yi, sai ya kai Naira miliyan 3.5.
Da wannan a iya cewa ba wani abu da Gwamnatin Tarayya za ta yi wajen kara tallafa wa maniyyatan na bana.
A nan ina ga lokaci ya yi da Hukumar NAHCON da hukumomin jin daɗin alhazai na jihohi za su ƙara sa amana da gaskiya da tsoron Allah wajen ganin sun rage cuwa-cuwa da sama-da-fadi da ake zargin suna yi a lokacin aikin Hajjin, musamman wajen ɗaukar jiragen sama da kama masaukin alhazan a Makka da Madina da kudaden sufuri da na hemahema a Mina da filin Arfa da ma duk inda kudi ke gilmawa da sunan hidimar aikin Hajji.
Har gobe aikin Hajji na daga cikin aikin da gwamnatoci kasar nan ke tutiyar cewa suna yi wa Musulmi sassaucinsa, amma kuma mahukuntan sun kasa fitowa su fayyace wa maniyyatan irin sassaucin.