Hajjin Bana: Gwamnati ta ɗauki nauyin maniyyata 47 a Ribas
Fubara ne Gwamna na farko da ya biya dukkan kuɗaɗen da Hukumar Hajji ta Ƙasa ta buƙata daga maniyyata.
Gwamnatin Jihar Ribas ta ɗauki nauyin maniyyata 47 domin sauke farali a aikin Hajjin bana.
Wannan ya sa gwamnatin ta samu alamar yabo daga Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar a yayin bikin tashinsu zuwa Ƙasa Mai tsarki.
Shugaban Hukumar, Alhaji Deprieye Abdulrazaƙ ya ce Gwamnan Jihar, Mista Similiani Fubara ne Gwamna na farko da ya biya dukkan kuɗaɗen da Hukumar Hajji ta Ƙasa (NAHCON) ta buƙata daga maniyyatan kafin wa’adin yin hakan ya cika.
“Haƙiƙa gwamnanmu ka yi rawar gani na ɗaukar nauyin maniyyatan baki ɗayansu daga wannan jihar baya ga taimaka wa wannan hukuma da duk abin da ya kamata kuma a kan lokaci.
“Kuma tun lokacin kama mulkin kaka a jihar nan ka mai da hankali kan kula da jin daɗin Musulmin jihar,” in ji shi.
A jawabin Gwamna Fubara ga maniyyatan kafin tashinsu daga filin jirgin saman Fatakwal, ya yi kira ga maniyyatan su tsaya su gudanar da rukunan aikin Hajjin yadda ya kamata kamar yadda addini ya buƙaci su yi.
Ya kuma ƙara kira gare su da su zama mutane kirki da nuna hali nagari a Ƙasa Mai tsarki kuma su yi wa jihar da ƙasar nan addu’a.