Hajjin bana: Minsitan Lafiya ya kawar da tsoron da ake yi kan zazzabin Lassa
Minista Lafiya Farfesa Isaac Adewole ya sanar da Gwamnati da al’ummar Saudiyya cewa cewa Najeriya a matsayninta na kasa babu wata barazana da za ta haifar ga kasashen duniya saboda rahotannin bullar cutar zazzabin Lassa a wasu ’yan yankuna na jihohi uku na kasarta. Farfesar Isaac Adewole ya bayyana haka ne a wajen taron masu […]

Minista Lafiya Farfesa Isaac Adewole ya sanar da Gwamnati da al’ummar Saudiyya cewa cewa Najeriya a matsayninta na kasa babu wata barazana da za ta haifar ga kasashen duniya saboda rahotannin bullar cutar zazzabin Lassa a wasu ’yan yankuna na jihohi uku na kasarta.
Farfesar Isaac Adewole ya bayyana haka ne a wajen taron masu ruwa-da-tsaki kan cutar zazzabin Lassa da Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya ya shirya tare da hukumomin jin dadin maniyyata na jihohi 36 da kuma Abuja game da abin da ya shafi aikin Hajjin bana.
Jaridar AljazeeraNajeriya da ake bugawa a Intanet wadda ta ruwaito labarin a shekaranjiya Laraba, ta ce, Minstan ya yaba wa Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya kan shirya taron inda ya bayyana shi da mai matukar muhimmanci. Ya ce Gwamnatin Tarayya ta dauki hayar ma’aikatan sanya ido kan cutar su 400 a sassan kasar nan, wadanda aikinsu shi ne su rika zagayawa suna gano inda aka samu bullar kowace irin cuta don magance ta nan take.
Ya ce, Najeriya tana samun nasarar kawar da cutar zazzabin Lassa, inda mutum daya kawai aka samu rahoton ya kamu da cutar a makon jiya a duk fadin kasar nan. Kuma ya ce Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai ta ga bayan cutar kwata-kwata, inda ya bayar da sanarwar cewa nan da shekara biyu zuwa uku za a bai wa Naijeriya takardar shaidar ban-kwana da cutar shan inna.
Minista Adewole ya roki ’yan Najeriya su ci gaba da tsabtace muhallansu domin kawar da cututtukan zazzabi a kasar nan. A cewarsa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da inganta asibitocinta da ke sassan kasar nan ta yadda za su rika gudanar da ayyukansu yadda ya kamata. Ya bai wa ’yan Najeriya tabbacin cewa nan kusa za a bayyana Najeriya ta yi ban-kwana da zazzabin Lassa, kuma ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya saki kudi domin daukaka darajar wasu asibitoci da sayo magungunan zazzabin Lassa.
“Ina kira ga dukan ’yan Najeriya cewa su kula da tsabtar muhallinsu sosai, kuma su guji yi wa kawunansu jinya, maimakon haka su rika kai rahoton bullar duk wani zazzabi ga asibiti mafi kusa cikin gaggawa. Mun shawo kan zazzabin Lassa, kuma ina shaida muku cewa a cikin makon da ya gabata, rahoton kamuwa da cutar daya kawai aka samu a Najeriya, kuma duk wani zazzabi za a yi gwaji a kansa domin a tabbatar ban a Lassa ba ne,” inji Ministan.
Shugaban Hukumar Hajji ta kasa (NAHCON), Barista Abdullahi Muhammad Mukhtar ya ce Saudiyya ta fito da dabaru tare da daukar matakai don tabbatar da cewa babau dan Najeriya da ya shiga kasar da abin da zai jawo harbuwa ko kamuwa da cutar zazzabin Lassa.
Ya ce, “Akwai rahotannin da kafafen watsa labarai suka bayar game da zazzabin Lassa a Najeriya, wadanda suka jawo hankalin Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya, kuma a bisa hangen nesansu sai suka bullo da wasu hanyoyin kariya da rigakafi don hana watsa cutar a lokacin aikin Hajji. Manufar wannan taro ita ce mu bullo da dabarun da za su gamsar da Ma’aikatar Lafiya ta Saudiyya da sauran kasashen duniya cewa maniyyatan Najeriya ba za su sanya rayukansu a cikin hadari ba a lokacin aikin Hajji da Umarah.”
Ya ce Hukumar NAHCON ta yanke shawarar hanzarta kafa kwamitin likitoci da malaman jinya don aikin Hajjin bana inda zai yi aiki kafada-da-kafada da dukan hukumomin da suka kamata wajen tantance maniyyata domin tabbatar da cewa suna da koshin lafiyar da za su iya zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin.
Shugabar Kwamitin Harkokin kasashen Waje na Majalisar Dattawa, Sanata Monsurat Sunmonu ta yi kira ga hukumomin jin dadin Alhazai na jihohi su tabbatar sun tantance lafiyar maniyyatansu don zuwa aikin Hajjin bana.