Hajjin bana: Za a mayar wa alhazan Sokoto kudadensu
Gwamnatin Jihar Sokoto ta umarci a mayar wa maniyyata aikin Hajjin 2020 kudaden kujeru da suka biya bayan kasar Saudiyya ta soke aikin saboda bullar cutar coronavirus. Hukumar alhazan jihar, bayan samun umarnin daga Gwamna Aminu Tambuwal, ta ce ta fara shirin mayar wa maniyyatan kudadensu nan ba da jumawa ba. Saudiyya ta fitar da […]
Gwamnatin Jihar Sokoto ta umarci a mayar wa maniyyata aikin Hajjin 2020 kudaden kujeru da suka biya bayan kasar Saudiyya ta soke aikin saboda bullar cutar coronavirus.
Hukumar alhazan jihar, bayan samun umarnin daga Gwamna Aminu Tambuwal, ta ce ta fara shirin mayar wa maniyyatan kudadensu nan ba da jumawa ba.
- Saudiyya ta fitar da jerin mutanen da ba za su yi aikin Hajji ba a bana
- Mazauna Saudiyya ne kadai za su yi Hajji bana
Kakakin hukumar, Shehu Muhammad Dange ya ce, “Mun umarci kananan hukumomi su tattara bayanan alhazansu domin a fara biyan su saboda kada a samu matsala”.
Kakakin ya ce za a mayar da kudaden bisa tsarin hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), “ko da yake wasu za su so a ci gaba da ajiye kudadensu har zuwa lokacin aikin Hajjin 2021.
Ya shawarci maniyyatan da su dauki rashin samun halartar ibadar ta bana a matsayin kaddara.