… Haka ma a birnin Ibadan
Da yammacin Talatar da ta gabata ne mutane maza da mata da kananan yara suka yi dandazo suna kade-kade da raye-raye da wakoki a bisa manyan hanyoyin birnin Ibadan, domin nuna murna da farin ciki tun kafin Hukumar Zabe (INEC) ta fadi sakamakon wanda ya yi nasara a tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu […]
Da yammacin Talatar da ta gabata ne mutane maza da mata da kananan yara suka yi dandazo suna kade-kade da raye-raye da wakoki a bisa manyan hanyoyin birnin Ibadan, domin nuna murna da farin ciki tun kafin Hukumar Zabe (INEC) ta fadi sakamakon wanda ya yi nasara a tsakanin Shugaba Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari, a zaben da aka gudanar Asabar da ta gabata.
Bayan samun labarin mubaya’ar da Shugaba Jonathan ya yi wa Buhari, sai shagulgulan suka karu a cikin birnin na Ibadan. Jagoran APC na unguwar Sabo (ward 6) Alhaji Baba Kutunga, shi ne ya jagoranci dimbin jama’a tare da sayen wani bijimin sa da aka shafe jikinsa da farar kasa launin tutar jam’iyar APC kafin a kai ga yankawa, domin raba naman kyuta ga magoya baya domin nuna farin ciki da nasarar da Janar Buhari ya yi na lashe zaben zama sabon Shugaban kasa.
Jagora Kutunga, wanda ya dauki nauyin sayen dami-dami na tsintsiyar da aka raba ga jama’a domin share kazanta a babbar hanyar unguwar Sabo mai tsawon kilomita daya, ya roki Allah Ya kare Janar Muhammadu Buhari daga sharrin miyagun fadawa kuma ya yi misa jagoranci da yin adalci na tsawon wa’adin mulkin Najeriya da zai yi. “Kuma ina rokon duka ’yan Najeriya mu bayar da hadin kai da goyon baya ga salon mulkin sabon Shugaban kasa wanda ya yi mana alkawarin samar da canji. Kada mu fara tunanin ganin gyaran abubuwan da suka lalace cikin kankanen lokaci. Dole ne mu yi hakuri zuwa wani lokaci mai tsawo, domin samun mikakkiyar hanya da sabon shugaban zai bi wajen gyaran irin barnar da aka yi a cikin shekaru 16 na mulkin dimokuradiyya, wacce suka haifar da tabarbarewar tsaro da cin hanci da rashawa da rashin aikin yi ga miliyoyin matasan kasar nan. Sai idan mun yi hakuri ne sannan za mu kai ga cin ma wannan buri da zai amfane mu a nan gaba.”
Shi kuwa Alhaji Babangida ’Yankara cewa ya yi: “Babban abun farin ciki shi ne irin yadda a yanzu jama’ar Najeriya suka waye da harkokin siyasa fiye da lokutan baya da ake amfani da kudi wajen sayen ra’ayinsu da tilasta musu zaben mutane. Zaben ’yan takarar mukaman shugabancin kasa da ’yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar, shimfida ce ta dorewar mulkin dimokuradiyya kuma darasi ne ga ’yan siyasa da ke ganin za su iya yin amfani da kudi wajen sayan ra’ayin jama’a. Ya kamata mu sanya kishin kasar haihuwarmu a gaba domin irin haka ne ya kai wasu kasashen duniya samun ci gaban da suke cin moriyar rayuwa. Halin dattawa da Shugaba Goodluck Jonathan ya nuna wajen yin mubaya’a ga Janar muhammadu Buhari tun kafin a bayar da sakamakon zabe, abun jinjinawa ne domin yin hakan ya sa jama’ar Najeriya sun fara yafe wa shugaba mai barin gado a kan irin kwabasuwar da gwamnatinsa ta yi.”
A wani labarin makamancin wannan, a ranar Litinin da ta gabat kuma, ’yan takarar kujerar gwamna na jam’iyun hamayya su 4, wato Otunba Christopher Adebayo Alao Akala na Labour da Teslim Folarin na PDP da Seyi Makinde na SDP suka yi taro a gidan Rasheed Ladoja na Accord, a inda suka bayar da sanarwar rashin amincewa da sakamakon zaben ‘yan majalisun tarayya da jam’iyyar APC, ta yi nasarar lashe kujeru 3 na wakilan majalisar dattijai da kujeru 12 na wakilan majalisar tarayya. A wannan rana, an ga daruruwan magoya bayan wadannan jam’iyu suna yin zanga-zangar lumana a harabar ofishin hukumar zabe da ke Ibadan. Sai dai Kwamishinan zabe na Jihar Oyo Dakta Rufus Akeju, ya fadi a ranar Laraba cewa, duk wanda yake da wani korafi a game da zaben na Jihar Oyo sai ya mika kukansa ga kwamitin sauraron kararrakin zabe na jihar.