Haka nan Siyasa ta gada

Adawa a Najeriya ba daidai take ba da irin ta kasashen da ke bin mulkin dimokuradiyya, inda jama’a ke da ‘yancin fadin albarkacin bakinsu, ko daukar matakan da dokokin kasa suka amince da su wajen yin gyara ko kyautata harkokin gudanar da mulki. A Najeriya ‘yan adawa ba su da dama su soki lamirin gwamnati […]

Haka nan Siyasa ta gada
Haka nan Siyasa ta gada

Adawa a Najeriya ba daidai take ba da irin ta kasashen da ke bin mulkin dimokuradiyya, inda jama’a ke da ‘yancin fadin albarkacin bakinsu, ko daukar matakan da dokokin kasa suka amince da su wajen yin gyara ko kyautata harkokin gudanar da mulki. A Najeriya ‘yan adawa ba su da dama su soki lamirin gwamnati sai a ce suna fito-na-fito ne da ita, ba su kuma da halin kyamar manufofin gwamnati wadanda suke gani illoli ne ga rayuwarsu.
Wannan yanayi ya yi kamari ne a Najeriya sakamakon dogon zamanin da kasar ta yi a karkashin mulkin soja, yayin da babu wani mahalukin da zai bijire musu, ko muzanta manufofi da ka’idojinsu, sa’annan kuma hatta gwamnatin farar hular da sojojin suka yi ta daure gindi wajen kakkafa su ba su yarda a yi masu gyara a al’amaruransu cikin majalisa, ba su kuma karbar shawarwari game da take-takensu na siyasa ko a tsarinsu na zartar da mulki.
Ana cikin wannan hali ne sai ga shi nan an kafa jam’iyyar APC, wacce a yanzu take tsone wa makiya ci gaban talakawa idanu, kuma tun daga wancan lokaci ne wannan sabuwar jam’iyyar ta canja yanayin adawa, ta kuma fara daukar matakan da ba safai aka saba ganin irinsu ba a kasar nan, tana  karya wa gwamnati tsinken tsire a ido don taka mata birki, kada ta wuce gona da iri.
Sa’ilin da  rikicin siyasa ya kazanta a Jihar Ribas inda gwamnati ke takura zababben gwamnan Jihar, Cif Rotimi Ameachi ya kazanta, har ta kai ana hana shi rawar gaban hantsi daidai da yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya yarje masa, sai wannan sabuwar jam’iyyar ta APC  ta fito fili, firi-falo, ta nuna rashin amincewarta da yadda gwamnati ke yi wa tsarin dimokuradiyya karan-tsaye a jihar, tana kuma yi wa shugabanninta hawan kawara don suna ganin sun fi karfin wani ya tankwara su. Hanyar da jam’iyar APC ta fahimci za ta iya bi don sanya gwamnatin tarayya da kuma shugabannin jam’iyyar da ta kafa sanin Annabi ya faku, za a kuma yi tashin duniya, shi ne ta kaurace wa dukkan wasu kudurori da shawarwarin da za a kawo gaban majalisa don a nuna ma makaho cewa ana ganinsa, ba lallai sai an taba shi ba.
Yin haka kuwa wani sabon salon bin tafarkin dimokuradiyya  ne wanda zai hada da yin watsin da ‘ya’yanta za su yi game da batun nazarin kasafin kudin bana da ke  gaban majalisun kasa guda biyu da kuma kin shiga cikin sabgar tantance sunayen mutanen da shugaba Goodluck ya aike don nada su ministoci. Wannan abu ya tayar da hankalin gwamnati da makararrabanta, wadanda suka yi ta yin muggan alkaba’i ga jam’iyyar da shugabanninta, sun mance cewa tafarkin dimokuradiyya ake bi a kasar nan, suna da ‘yancin yin haka bisa ga tsarin mulki. A cewar  ‘yan PDP hakan wai bai dace ba, domin kuwa jam’iyyar da ke ikirarin kawo canji irinta, bai kamata  ba ta dauki irin wannan matakin da ta ce zai iya takalo yamutsi da rashin kwanciyar hankali ba.
To amma ai wannan mataki da jam’iyyar adawa ta APC ta dauka ba wani sabon abu ne ba, haka nan tsarin dimokuradiyya ya gada a duk duniya. Alal misali a watan Oktobar shekarar 2013, jam’iyyar adawa ta Republican a kasar Amurka,  ta toshe dukkan wasu hanyoyin zartar da kudurori ko shawarwarin gwamnatin Barack Obama  na tsawon kwanaki 16, kuma hakan bai sa  Shugaba Obama zargin kowa ba da kokarin kawo rudani dangane da haka, kamar yadda shugabannin PDP da ‘yan korensu ke yi a Najeriya a yanzu yayin da suke nuna cewa wakilan talakawa ba su da damar takura wa gwamnati janye miyagun manufofin da ke tauye masu ‘yanci, suna kuma kuntata wa rayuwarsu. Shugaba Obama ya yi amfani ne da tsananin basirarsa  ta hanyar fadakar da ‘yan majalisa dalilan da ya sa gwamnatinsa daukar wasu matakai har hakan ya sa ‘yan majalisa suka fahimta, suka bude kafafen da suka tottoshe don a ci gaba da harka da gwamnati.
Ashe ke nan ya kamata shugabannin PDP su yi koyi da Amurkan da suke kwaikwaya, su daina cewa ana muzguna masu ne da gangar da niyyar kai su kasa a dukkan lokutan da ‘yan adawa suka nemi uzzura wa gwamnati don yin abubuwan da suka kamata, wadanda za su taimaki rayuwar jama’a da kuma ci gaban kasa. Siyasa ce dai ake yi, ita ce kuma Shugaba Jonathan ke yi a Jihar Ribas don neman gindin zama.
A yanzu dai ya kamata jam’iyyar PDP ta fahimci inda aka dosa don ta canja halayenta da suka janyo mata haka. Hanyoyin zartar da shawarwari da kudurorin gwamnati a majalisa  ba saban ne ba a siyasar kasashen duniya. Shin wai sa’ilin da ba a nemi yin watsi da batun kasafin kudI ba a majalisa, aka yi ta zartar da na shekarun da suka gabata, me  hakan ya tsinana wa talaka?  Idan kwalliya ta biya kudin sabulu  ai shi ke nan. A nan kwalliyar ita ce ingantaccen shugabanci, kudin sabulun kuwa shi ne wannan sabon matakin da za a dauka don tursasa wa gwamnati sakar wa talakawa mara su fitsare. Haka nan dai siyasa da dimukuradiyya suka gada.