…Haka shi ma Mataimakin Shugaban kungiyar Izala
Allah Ya yi wa Mataimakin Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Alhaji Ibrahim Muhammad Na Alhaji Azare rasuwa, a ranar juma’ar da ta gabata. Ya rasu ne a gidansa da ke garin Jos, bayan ya yi fama da doguwar jinya. Ya rasu yana da shekaru 118. Ya rasu ya bar ’ya’ya 7 […]

Allah Ya yi wa Mataimakin Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’ikamatis Sunnah ta kasa, Alhaji Ibrahim Muhammad Na Alhaji Azare rasuwa, a ranar juma’ar da ta gabata. Ya rasu ne a gidansa da ke garin Jos, bayan ya yi fama da doguwar jinya. Ya rasu yana da shekaru 118. Ya rasu ya bar ’ya’ya 7 da jikoki da tattaba kunne sama da 50.
Shi dai marigayin ya rike mukamai da dama a cikin kungiyar kuma kafin kungiyar ta sake hadewa, shi ne shugaban kungiyar na kasa, bangaren Jos. Bayan da kungiyar ta sake hadewa ne aka zabe shi a matsayin mataimakin shugaba na kasa, mukamin da ya rike har ya zuwa wannan lokaci da Allah Ya yi masa rasuwa.
Da yake mika sakon ta’aziyarsa a wajen zaman makoki, Shugaban Majalisar Malaman kungiyar na kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir, ya bayyana rasuwar marigayi Alhaji Na Alhaji Azare da cewar an bar wani babban gurbi mai wuyar cikewa a cikin kungiyar.
Ya ce marigayin ya yi wa kungiya gagarumin aiki, tun daga ranar da aka kafa ta har ya zuwa wannan lokaci da Allah Ya karbi rayuwarsa. Ya ce tun da ake tare da marigayin, ba a taba samun sa da wata damuwa ba a cikin kungiyar.
A wata sabuwa kuma, majalisar zartarwar kungiyar ta kasa, ta ba da sanarwar zaben Alhaji Abdurrahaman Marafa Tambuwal a matsayin sabon Mataimakin Shugaban kungiyar na kasa.
Shi dai Tambuwal, kafin a nada shi wannan matsayi, shi ne mataimakin shugaban kungiyar na kasa na II. Haka kuma an zabi shugaban majalisar malamai ta Jihar Filato,
Ustaz Abdul Nasir Abdulmuhyi a matsayin mataimakin shugaban kungiya na kasa na II, a yayin da kuma aka nada Dokta Hassan Abubakar Dikko a matsayin sabon shugaban majalisar malamai ta jihar Filato.