Hakar ma’adanai: ILO ta horas da masu ruwa da tsaki kan illar bautar da yara
A wani yunkuri na kawo karshen bautar da kananan yara a Najeriya, Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO ) ta horas da masu ruwa da tsaki kan tsaron sana’o’i da kuma yakar bautar da yara a aikin hakar ma’adanai. Kungiyar da ke kula da wurare hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ta shirya taron ne da […]

A wani yunkuri na kawo karshen bautar da kananan yara a Najeriya, Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO ) ta horas da masu ruwa da tsaki kan tsaron sana’o’i da kuma yakar bautar da yara a aikin hakar ma’adanai.
Kungiyar da ke kula da wurare hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ta shirya taron ne da nufin ķarfafa guiwar masu ruwa da tsaki domin kawo karshen bautar da yara a wuraren hakar ma’adinai a jihohin Neja da Osun.
Taron da ya gudanan daga ranar 18 zuwa 27 na watan Fabarirun 2025, wakilan gwamnati da kungiyoyin ma’aikata da shuwagabannin yankunan sun hallara, inda suka tattaun kan hanyoyin kawo karshen matsalar.
Kazalika an bai wa mambobin kwamitin sanya ido kan ayyukan bautar da yara na jihohin kayan aiki da za su taimaka musu wajen sanya ido kuma da kai rahoton game da bautar a kananan yara.
A jawabinta, Daraktan kungiyar kwadago ta Najeriya, Dakta Vanessa Phala, wacce ta samu wakilcin mai kula da ayyuka na kungiyar ACCEL Africa, Misis Celine Oni, ta jaddada cewa za a aiwatar da dokoki da tsare-tsare da za su taimaka wajen kawo karshen wannan matsala.
Kudurin karfo na shirin ACCEL Africa shi ne, aiki tare da ma’aikatun kwadago da na bunkasa ayyuka da na noma, da na ma’adanai da dai sauransu.
Na biyu shi ne, daukar mataki kan sabubban bautar da yara a wuraren haķar ma’adanai, da kuma mai da hankali kan samar da kariya da kudade da kiwon lafiya da kuma aikin yi ga matasa.
Ta jaddada cewa za a magance matsalar bautar da yara, wadda ta ce talauci da rashin samun kariya ne kan gaba wajen haifar da su.
Kwanturola na ma’aikatar kwadago da inganta aiki ta kasa ta Jihar Neja, Hauwa Zakariyya, ta ce, “samar da tsaro da kiwon lafiya hakki ne a kan kowa, kuma ba za a samu wata ci gaba ba tare da tsaro ba.
“Shi ya sa muke daukar wannan kungiya ta ACCEL Africa da muhimmanci, saboda ta mayar da hankali kan wuraren haķar ma’adanai, domin daile aukuwar irin irin abin da ya faru a yankin Kuchiko, inda aka rasa rayuka da dama ciki har da yara kanana. Mun yi imanin cewar wannan tsari zai ilimantar da masu hakar ma’adanai yadda za su kare kansu a nan gaba.”
A nasa bangaren, kwantorulan na ma’aikatar kwadago na Jihar Osun, Solomon Ayinde Alabi, ya ce, “Muna murna da samun rahoto da ke tabbatar da cewa ficewar yara daga makarantu ya ragu sosai. Wannan babban labari ne gare mu a irin wadannan yankuna”.
“Ina kira gare mu a matsayinmu na iyaye masu kulawa, da al’umma da mu yi amfani da wannan dama da kyau wajen kara azama wajen yaki da ta’addanci, bautar da yara a yankunanmu.”
Mahalarta taron sun ziyarci wuraren haķar ma’adanai a jihohi mabambata don gano hadarin da ke tattare da wannan aiki. Wani dan shekaraa Lawali Yusuf daga cikin masu haķar ma’adanai a Korokwa da ke Minna na jihar Neja ya ce, “ina wannan aiki ne saboda iyayena ba su da karfin daukar nauyin karatuna, shi ya sa nake yi don na tara kudi na fara zuwa makaranta kamar sauran abokaina.”
A yankin Idoka da ke Osun, wani dan shekara 11, Ibrahim da ke hakar ma’adanai ya ce, “burina shi ne zama mai hakar ma’adanai idan na girma, don haka ne ma na zo nan a matsayin yaron gida. Ina so na koyi yadda ake hako zinari duk da ma dai sau da dama ana kora ta daga wurin, sai dai ina dawowa saboda muradina ke nan zama mai haķar ma’adanai.”