Hakimin bagwai ya nemi al’umma su yi addu’ar zaman lafiya
dan Madamin Kano kuma Hakimin bagwai, Alhaji Nura Shehu Ahmed ya bukaci jama’a su dage da yin addu’o’in zaman lafiya ga masarautar Kano da kasa gaba daya. Hakimin ya bukaci haka ne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a lokacin cikarsa shekara 30 a gadon sarauta.Hakimin ya ce addu’o’in da jama’a ke yi […]
dan Madamin Kano kuma Hakimin bagwai, Alhaji Nura Shehu Ahmed ya bukaci jama’a su dage da yin addu’o’in zaman lafiya ga masarautar Kano da kasa gaba daya.
Hakimin ya bukaci haka ne a lokacin da yake jawabi ga manema labarai a lokacin cikarsa shekara 30 a gadon sarauta.
Hakimin ya ce addu’o’in da jama’a ke yi ne ke rike da masarautar da kasar nan, inda ya ce ba ya da wani abin da na sani a tsawon lokacin da ya dauka yana hakimcin yankin bagwai, duk da kalubalen da ya rika fuskanta.
Ya ce a tsawon wannan lokaci masarautar ta samu ci gaba da daukaka ta fuskar addini da tattalin arziki. “Abubuwa da dama sun faru da suka zama dalilin daukaka wannan masarauta ta fuskar noma da harkokin lafiya da kuma tsarin jin dadin rayuwar jama’a.”
Sanann Hakimin ya yaba wa marigayi Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero bisa nada shi a matsayin Hakimin bagwai shekara 30 da suka wuce.
Haka kuma ya gode wa Sarkin Kano Muhamamdu Sanusi II saboda ba shi damar gudanar da wannan biki.
A jawabinsa a wajen bikin tsohon Wakilin Najeriya a Majalisar dinkin Duniya, Alhaji Yusuf Maitama Sule ya bayyana masarauta da cewa wuri ne na girmamamwa wanda kuma yake kara wa jiha da kasa kima a idon duniya.