Hakkin tsaro ya rataya ne a kan jama’a da jami’an tsaro
Salam Edita. A yau ina son in yi tsokaci ne a kan sake yunkurowar da kungiyar Boko Haram ta yi a yankin Arewa maso Gabas. A gaskiya yadda kungiyar ta sake zafafa hare-harenta a wannan yanki, yana da kyau al’ummar yankin masu fama da tabarbarewar tsaro su rika zama a cikin shirin bai wa jami’an […]
Salam Edita. A yau ina son in yi tsokaci ne a kan sake yunkurowar da kungiyar Boko Haram ta yi a yankin Arewa maso Gabas. A gaskiya yadda kungiyar ta sake zafafa hare-harenta a wannan yanki, yana da kyau al’ummar yankin masu fama da tabarbarewar tsaro su rika zama a cikin shirin bai wa jami’an tsaro hadin kai ta hanyar tsegunta wa jami’an tsaron duk wani wanda ba a yarda da shi ba domin ta haka ne kawai za a kawo karshen wadannan hare-hare na kungiyar a Arewa maso Gabas kasashen Nijar da Kamaru. Da fatan Allah Ya ba mu dauwammen zaman lafiya a kasashenmu na Nijar da Najeriya da Kamaru da Afirka baki daya, amin summa Amin.
Daga Ashiru Usman Sabuwar Gwaram, Jihar Jigawa 07030817573.