Hakkokin Annabi Muhammad (SAW) a kan Musulmi
Fassarar Salihu Makera Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin annabawa da manzanni, Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya. Bayan haka, ya ku ’yan uwa! Ku tafi kowace kasar Musulmi ku ga dogayen husumiyoyi da suke kowace kusurwa inda ake jin muryoyin ladanai […]
Fassarar Salihu Makera
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da Amincin Allah su kara tabbata ga mafificin annabawa da manzanni, Annabinmu Muhammad da alayensa da sahabbansa baki daya.
Bayan haka, ya ku ’yan uwa! Ku tafi kowace kasar Musulmi ku ga dogayen husumiyoyi da suke kowace kusurwa inda ake jin muryoyin ladanai suna kiran muminai zuwa ga Sallah sau biyar a wuni.
Wannan kira mai sauki da daraja tana tunatar da al’umma ce game da rayuwarsu ta yau da kullum – cikin jin dadi ko kunci suke, – har su hadu da Allah – a takaice ana so mutum ya ajiye duniya ya koma ga abin da zai kyautata ruhinsa. Wannan kiran Sallah yana taimaka mana wajen dora rayuwarmu kan abin da yake daidai.
Mai kiran Sallah yana fara kira ne da fadin ‘Allah ne Mafi girma!,’ (daga dukkan wani abu) sannan ya biyo da kalmar alkawarin imani (Kalmar Shahada). Farkon wannan alkawari shi ne Shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah. Na biyu shaidawa Muhammadu Manzon Allah ne. Bangare na farko shi ne tabbatar da tauhidi, kashi na biyu tabbatar da hanyar da za a aiwatar da wannan akida ko aiki na imani. Ya ’yan uwa masu girma! Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne da yake da hakkoki a kan kowane Musulmi kamar yadda aka ambata a cikin Alkur’ani. Kuma malaman Musulunci sun yi bayani a kan wadannan hakkoki a wurare bakwai kamar haka:
- Yin imani da shi
Wannan ba yana nufin gaskata shi a matsayin wani fitaccen mutum a tarihi a Karni na Bakwai a kasashen Larabawa kadai ba ne, a’a har da gaskata Annabtarsa da sakon Allah gare shi (Manzancinsa). Allah Madaukaki Ya ce: “Saboda haka ku yi imani da Allah da ManzonSa da hasken nan da Muka saukar.” (K:64:8). Kuma Annabi Muhammad (SAW) ya ce a cikin Hadisi: “An umarce ni da in yaki mutane har sai sun shaida babu abin bauta da gaskiya sai Allah, kuma sun yi imani da ni a matsayin Manzon Allah.” [Sahih Muslim]
- Yi masa biyayya
Imani da shi (SAW) ta hanyar furci da baka bai wadatarwa. A’a imani na gaskiya yana nufin sakonsa ya zame mana jagora tare da biyayya ga abin ya umarce mu. Allah Madaukaki Ya ce:
“Ya ku wadanda suka imani! Ku yi da’a ga Allah da ManzonSa, kuma kada ku juya daga barinsa alhali kuna ji.” [K:8:20].
Kuma Ya ce: “Wanda ya yi da’a ga Manzon (Allah), to, hakika ya yi da’a ga Allah.” [K:4:80].
Annabi Muhammad (SAW) ya fadi a wani Hadisi: “Dukkan al’ummata za ta shiga Aljanna, sai wanda ya ki. Sai (sahabbai) suka ce: “Ya Manzon Allah wane ne zai ki?” Sai ya ce: “Wanda ya yi min biyayya zai shiga Aljanna, wanda ya saba mini hakika ya ki.” [Sahihul Bukhari].
- Yin koyi da shi
Lura da yadda Allah Ya yabi masoyinSa Annabi (SAW) da cewa: “Kuma lallai hakika kana a kan halayen kirki manya.” [K:68:4], ba abin mamaki ba ne ya zo a zuciya cewa koyi da Annabi Muhammad (SAW) wani hakkinsa ne a kanmu.
Kuma Allah Madaukaki Ya ce: “Ka ce: Idan kun kasance kuna son Allah, to ku bi ni.” [K:3:31]. A wata ayar kuma Madaukaki Ya ce:
“Lallai abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah.” [K:33:21]. Sannan Manzon Allah (SAW) ya ce: “Duk wanda ya kyamaci sunnata ba ya tare da ni.” [Bukhari da Muslim].
Don haka mafi muhimmancin wajibcin yi masa biyayya, shi ne a yi koyi da shi – akwai abubuwa da dama da yin koyi da shi farilla ne, akwai inda a ka karfafa aka nemi a yi amma ba farilla ba ne, (sannan akwai wasu abubuwa da aka tattara game da tarihinsa da kawai don bayani nib a don hukunta shari’a ba.) Samun ilimin fikihu zai taimaka wajen bambance wadannan matakai na koyi ko takalidi. Kuma wajen yin haka ne Musulmi suke bakin kokarinsu wajen bin gwadaben misalan da Annabi (SAW) ya bari kuma suke gina rayuwarsu kan hasken sunnarsa gwargwadon iko. Domin ta koyi da shi ne dan Adam ke samun kamala kuma kyawawan dabi’u suke tabbata.
- Sonsa
Domin Kur’ani ya ce: “Ka ce: Idan iyayenku da ’ya’yanku da ’ya uwanku da matanku da danginku da dukiyoyi wadanda kuka yi tsiwirwirinsu da kasuwancin da kuke tsoron tasgaronsa da gidaje wadanda kuke yarda da su sun kasance sun mafiya soyuwa a gare ku daga Allah da ManzonSa da yin jihadi a hanyarSa, to ku yi jira har Allah Ya zo da umarninSa. Kuma Allah ba Ya shiryar da mutane fasikai.” [K: 9:24].
Hakika son Annabi (SAW) shi yake bambance Musulmi wajen cikar imaninsu, kamar yadda wani Hadisi ya ce: “Babu imani ga dayanku har sai ya so ni fiye da mahaifinsa da ’ya’yansa da mutanen duniya (da abin da ke cikinta) baki daya.” [Bukhari da Muslim].
Kuma yana daga cikin son Annabi (SAW) son iyalan gidansa. Annabi (SAW) ya ce: “Ina yi muku wasiyya game da iyalina.”[Sahih Muslim].
Lokacin da Zaid bin Sabit (RA) ya yi Sallar Janaza wa mahaifiyarsa , bayan ya idar sai ya matso da godiyarsa zai hau, sai Ibn Abbas (RA) ya matso ya kama ragamarta. Sai Zaid ya ce: “Ka bar Ya Kawun Manzon Allah!” Sai Ibn Abbas ya ce: “Haka aka koyar da mu kan mu girmama malamai.” Sai Zaid ya kama hannun Ibn Abbas ya sumbace shi ya ce: “Haka aka koyar da mu mu yi wa iyalan Annabinmu.” [Dabarani a cikin Mu’jam’al-Kabir].
- Girmama shi da karfafa shi
Imani na gaskiya bai tsaya ga neman a nuna soyayya kadai ba, ya hada da girmamawa. Allah Madaukaki Ya ce: “To wadanda suka yi imani da shi, suka karfafa shi kuma suka taimake shi kuma suka bin hasken da aka saukar tare da shi, wadannan su ne masu cin nasara.” [K:7:157]. Kuma Ya ce: “Kuma ku karfafa shi, kuma ku girmama shi.” [K:48:9].
Imam Al-Kazwini ya daddale kan kalmar girmamawa da karfafawa (ta wajen bayyana ta da Tabjil, Tawkir da Ta’azim) da soyayya, inda ya kawo misali da abin da Imam Baihaki yake cewa: “Wannan kaiwa makura ce wajen soyayya, domin ba kowane wanda ake so ba ne ake girmamawa. Misali mahaifi yana son dansa ko ubangida yana son bawansa amma ba ya girmama shi ya kambama shi. Amma duk wanda aka girmama ana sonsa.” [Mukhtasar Shu’ab al-Iman].
- Imani da cikar Annabta da shi
Allah Madaukaki Ya ce: “Muhammad ba mahaifin daya daga cikin mazanku ba ne, amma shi Manzon Allah ne kuma Cikamakin Annabawa. Kuma Allah Masani ne ga dukkan komai.” [K:33:40].
Sananne ne cewa idan aka ce wani abu ya ‘cika’ yana nufin an gama don haka babu bukatar kari a kansa. Kamar haka Annabi Muhammad (SAW) ya zame cikamakin aiko annabta idan ya rufe wannan kofa, shi ne Annabi na karshe a bayansa ba za a sake samun wani Annabi ba. Don haka malamai ne za su ci gaba da bayyana gaskiya da jaddada ta amma ba wani Annabi ba. Annabinmu (SAW) shi ne Cikamakin Annabawa kuma hakan ya tabbata a cikin hadisai da dama daya daga cikinsu shi ne wanda yake cewa: “Za a samu wadansu makaryata talatin a cikin al’ummata, kowannensu yana da’awar shi Annabi ne. Ku sani ni ne Annabin karshe; babu wani Annabi a bayana.” [Muslim da Abu Dawud].
- Yi masa salati da taslimi
A cikin Alkur’ani Mai girma an shaida mana cewa Allah da mala’ikunSa suna salati da taslimi domin grimama Annabi Muhammad (SAW), inda Allah Madaukaki Ya ce: “Lallai ne Allah da mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.” [K:33:56]
Annabi Muhammad (SAW) ya ce a wani Hadisi: “Duk wanda ya yi mini salati daya, Allah zai yi masa salati goma.” [Sahih Muslim]. Kuma ya ce: “Wadanda suka fi kowa kusa da ni a Ranar Alkiyama su ne wadanda suka yawaita yi min salati.” [Al-Tirmidhi]. Kuma (SAW) ya sake cewa: “Marowaci shi ne wanda aka ambaci sunana a gabansa amma bai yi mini salati ba.” [Tirmizi].
Game da ma’anar salatin Allah ga Annabi (SAW), Abu Aliyah wani fitaccen Tabi’i ya ce:
“Salatin Allah shi ne yabonsa a gaban mala’iku; salatin mala’iku shi ne addu’ar da suke yi masa (SAW).” [Sahihul Bukhari].
Amma ra’ayi mafi rinjaye shi ne wanda Imam Tirmizi ya ruwaito: “An ruwaito daga Sufyanus Sauri da wadansu ma’abuta ilimi cewa: Salatin Ubangiji shi ne rahamarSa, Salatin mala’iku shi ne nema masa gafara.” [Imam Tirmizi].
Allah Ya riga Ya yi albarka ga Annabi Muhammad (SAW) ta hanyar yawaita yi masa rahama; wannan rahama tana nufin: haske da ilimi da wahayi da taimako da karfafawa da karuya da saurin amsar addu’a da daukaka a matsayi da kuma kusanci gare Shi da girmama ambatonsa da sauran abubuwan da Allah Madaukaki ne kawai da ManzonSa MasoyinSa suka sani.
Su kuma Musulmi idan suka Salati gare shi (SAW) da taslmi suna addu’a ce don neman tsari da kariya da aminci a gare shi.
A karshe ina mai cewa; Ya Allah! Ka yi Salati da taslimi a kan Shugabanmu Masoyinmu Annabi Muhammad a duk lokacin da masu ambato suka ambace Shi, ko gafalallu suka gafala daga gare Shi. Allah Ya yi Salati a gare shi a tsakanin mutanen farko da na karshe da mafificiya mafi girma da yalwa da tsarkin salati da Ya taba yi wa wani daga cikin halittunSa.
Kuma kamar yadda bawan Allah, Imam Shafi‘i ya rubuta: “Babu wata rahama, ya alla wadda ake iya gani da wadda ba a iya gani da ta taba sauka a kanmu wadda muka samu ribar imani ko ta duniya ko wadda ta kawar da abin da zai cutar da imani ko jin dadin duniya, kamar Annabi Muhammad (SAW), wannan ne dalilin aiko shi; shugaban ne mafi dacewa, jagoran mai shiryarwa mai kare jama’a daga hallaka da abin da zai kawo cikas ga hanyar kwarai kuma mai gargadi. Ya Allah Ya kara salati a gare shi da alayensa, kamar yadda Ya yi salati ga Annabi Ibrahim da iyalansa. Lallai Kai (Allah) Abin godiya ne Mai girma.”[Al-Risalah ta Imam Shafi’i].
Dukkan godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga Manzonmu Mai girma Annabi Muhammad da alayensa da sahabbansa da masu binsa na gaskiya.
Imam Murtada Gusau Babban Limamin Masallacin Juma’a na Nagazi-Ubete kuma Limamin Masallacin Alhaji Abdur-Rahman Okene da ke Okene, Jihar Kogi za a iya samunsa ta: [email protected] ko +2348038289761.