Hakkokin miji a kan matarsa
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga karashen mukalar da muke kawo muku makonni hudu da suka wuce.10 Yin adalci dole ne ga matan da suke da yawa, ana nufin adalci a bangaren muhalli, tufafi, abinci da abubuwan masarufi, amma a bangaren sadaki, walima da kauna, ba lallai ne ya zama daidai […]
Assalamu alaikum, barkanmu da sake saduwa cikin wannan filin. Ga karashen mukalar da muke kawo muku makonni hudu da suka wuce.
10 Yin adalci dole ne ga matan da suke da yawa, ana nufin adalci a bangaren muhalli, tufafi, abinci da abubuwan masarufi, amma a bangaren sadaki, walima da kauna, ba lallai ne ya zama daidai wa daida ba, ana iya samun bambanci, Allah (SWT) Ya ce: “Ba za ku iya yin adalcin (so da kauna) a tsakanin matanku ba, to amma kada ku kuskura ku karkata (zuwa ga mowa) gaba dayan karkata, ku kyale (wata bora) kamar wadda aka rataya (ba a kallonta sai za a yi amfani da ita)” (Nisa’i 129). kauna da so na samun asali ne saboda- hankalin mace, kyawunta, kudinta, ko matsayin iyayenta, da sauransu, don haka a bi a hankali ya ku mazaje kada a fada cikin halaka! Don haka adalci dole ne a tsakanin mata da ‘ya’ya, idan mutum ba zai iya yin adalcin ba, sai ya tsaya ga mace daya, kamar yadda aya ta nuna, (Nisa’i, 03). Mace daya ma dole ne a kiyaye mata hakkokinta, idan ba haka ba a sha azaba.
11 Ado da kwalliya, ya kamata a rika yi wa mata kwalliya da ado don kada hankalinta ya karkata zuwa ga mazajen waje. Ibnu Abbas (RA) ya ce: “Lallai ni ina son in yi wa matata ado, kamar yadda nake son ta yi mini, saboda Allah (SWT) yana cewa: “Su matan suna da irin abin da yake kansu (na hakkoki a gare ku) da kyautatawa.” (Bakara 228).
12 Yin wasanni, sake fuska, tattaunawa da hira hakki ne masu tabbatar da zaman lafiya a tsakanin ma’aurata, kamar yadda aka samo cewa Annabi (SAW) yana wasa da matansa, yana hira da su, yana sake musu fuska. Ya ce: “Mafi alkhairinku shi ne mafi alkhari ga iyalansa, ni kuma (Annabi SAW) na fi ku alkhairi ga iyalina” (Tirmizy 3892, Ibnu Hibban 1312).
13 Dole ne a yi mu’amala mai kyau ga iyalai, hakan shi zai tabbatar da dorewar ci gaba, kwanciyar hankali da more rayuwar duniya da lahira. Idan suna da yawa zai taimaka wajen sassauta mummunan kishi da kiyayya a tsakaninsu da rigingimun da babu gaira babu dalili.
Kiyaye wadannan hakkoki na mata su ne zamantakewa mai kyawu da samun arziki da albarka, Allah (SWT) Ya ce: “Ku zauna da su da kyautatawa (mai kyau)” (Nisa’i 13).
Hakkokin miji a kan matarsa
(1) Dole ne ta yi masa biyayya, ga abin da yake ba sabo ba ne, Annabi (SAW) ya ce: “babu biyayya a cikin sabon Allah, abin sani, da’a tana cikin abin da shari’a ta sani ne.” (Bukhari 7257, Muslim 1840).
(2) Ta zauna a gida ban da yawace-yawace, ban da fita sai da miji.
(3) Ta amsa masa idan ya nema ta, ba tare da matsala ba.
(4) Kada ta bar wata ko wani ya shiga gidansa sai da yardarsa. Manzon Allah (SAW) ya ce: “ka da wata mata ta bayar da izinin (shiga) gidan mijinta, alhali yana nan, sai da yardarsa.” (Muslim 1026), amma idan bai yarda ba, ko ba ya nan bai halatta ta bar wata ko wani ya shigo gidan ba.
(5) Ba za ta yi azumin nafila ba, idan yana nan, sai ya yarda, saboda hadisin da ya hana haka.
(6) Ba za ta dauki wani abu daga dukiyar miji ta bayar ba, sai ya amince, Annabi (SAW) ya ce: “Kada mace ta bayar da wani abu daga gidan mijinta sai ya yarda” (Abu Dawud).
(7) Za ta yi wa mijinta hidima, ta kula da al’amuran ‘ya’yansa, kamar abinci, wanki, share-share da sauransu daidai gwargwado, tun da zaman aure zama ne na cude-ni-in-cude-ka. Nana Fatimah (RA) ’yar Annabi (SAW) tana aikin wahala ainun a gidan mijinta Aliyu bin Ali dalib (RA) (Bukhari 5361, Muslim 2182).
Nana Asma’u (RA) ’yar Abubakar (RA), ita ma tana hidima ainun, har kulawa sosai take yi da dokin mijinta (Bukhari 5224, Muslim 2182). Idan miji ya samu dama sai ya sauwake wa matansa, ko ya rika taya su, don Annabi (SAW) ya kasance yana taya matansa aikace-aikacen gida, idan an yi kiran sallah sai ya fita, ya tafi masallaci, kamar yadda hadisin Nana A’ishatu (RA) ya nuna. (Bukhari 676).
(8) Wajibi ne ta kare mutuncinta, na mijinta da na ‘ya’yansa da kuma dukiyarsa, ban da almubazaranci, Allah (SAW) ya ce: “Matan kwarai, masu kaskantar da kai ne, masu kiyaye (mutunci da dukiya ne) ga gaibin da Allah Ya kiyaye.” (Nisa’i 34).
(9) Ta gode masa idan ya yi abin kirki, ka da ta muzunta masa, ko ta yi masa gori, kuma duk abin da ya samo ya kawo gwargwodon halinsa, ta karba hannu bibbiyu, don Annabi (SAW) ya ce: “Allah ba Ya yi wa matar da ba ta gode wa mijinta kallon rahama ba, kuma ba ta wadatuwa daga gare shi (da duk abin da Ya yi) (Nisa’i 249).
(10) Yi wa miji ado da gyara jiki shi ma babban hakki ne, Annabi (SAW) cewa ya yi: “Fiyayyar mace, ita ce wadda za ta faranta wa mijinta idan ya dube ta” (Nisa’i da Ahmad).
(11) Kada ta cutar da shi ko ta bakanta masa rai, saboda idan ta yi haka, matansa na aljanna wadanda suke jiransa za su tsine mata, su la’ance ta, su ce: “…ya shigo wajenki ne fa kawai! kwanan nan zai rabu da ke ya dawo wurinmu” (Tirmizy 1184, Ibnu Majah 2014).
(12) Ta yi wa iyayensa da ‘yan uwansa mu’amala mai kyau, don haka zai sa ta samu karbuwa a wurinsu, su rika yi mata addu’ar fatan alheri. Mu’amala mai kyawu, ita ce: sake musu fuska, maraba da su, ba su abinci, kyautata musu da sauransu.
(13) Kada ta kuskura ta nemi saki, sai idan abu ya gagara, kuma ta hanyar da ta dace, Annabi (SAW) ya ce: “Duk matar da ta tambayi mijinta saki ba tare da wani laifi ba, to haramun ne ta ji kamshin aljanna.” (Tirmizy 1199, Abu Dawud 2209)
Wadannan su ne hakkokin da aka dora wa mace dangane da mijinta, idan ta kiyaye su, za ta zama ta kwarai, kuma daya daga cikin manyan matan aljannah, kamar yadda Annabi (SAW) ya bayyana cewa: “Idan mace ta sallaci (salloli) biyar dinta (na farilla), ta yi azumin watanta (na ramadan), ta kiyaye farjinta (daga lalata), ta yi biyayya ga mijinta, sai a ce mata “ki shiga aljanna ta kofofin da kika ga dama.” (Ibnu Hibban 41630).
Wannan mata ita ce mace saliha, mai samar da annashuwa da albarkar duniya da lahira, don Annabi (SAW) ya ce: “Duniya jin dadi ne dan kadan, amma fiyayyen jin dadinta ita ce mace saliha.
Idan ma’aurata suka kiyaye wadannan hakkoki, za su samu zaman lafiya da natsuwa a duniyar aure gaba daya, kuma da lahirar ma ta yi kyau.
Muhammad Albani Misau
([email protected]/ [email protected])