Hakkokin Musulmi 6 a kan dan uwansa

Hakkoki dole ne Musulmi ya cika su a kan dan uwansa.

Hakkokin Musulmi 6 a kan dan uwansa

A addinin Islama akwai hakkoki shida da suka rataya kan kowane musulmi a kan dan uwansa musulmi da ya zama dole a cika masa su.

Wadannan hakkoki dole ne Musulmi ya cika su a kan dan uwansa kamar yadda yazo a hadisin Manzon Allah (SAW) cikin littafin Imamu Muslim.

Manzon Allah SAW ya ce hakkin Musulmi a kan dan uwansa Musulmi guda shida ne. Sune kamar haka:

  •  Idan Musulumi ya hadu da wani Musulmin to dole ya yi masa sallama shi ma dole ya amsa.
  •  Idan Musulmi ya gayyaci Musulmi to dole ne amsa gayyatarsa.
  •  Idan Musulmi ya nemi a bashi nasiha ko ka ba shi shawara to ya zama wajibi a ba shi.
  •  Idan Musulmi ya yi atishawa ya godewa Allah to ka gaishe shi.
  •  Idan Musulmi ya yi rashin lafiya ka je kaduba shi.
  • Idan musulumi ya mutu to a raka gawarsa kabari.