Hakkokin talaka da suka wajaba a kan shugabanni
Malam Shamsuddin S. Fada Sakkwato 07035617436 ne ya aiko mana da wannan mukala. Babu shakka tana dauke da jan hankali da nusarwa ga shugabanninmu. A sha karatu lafiya: Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. TaimakonSa da gafararSa muke nema, kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah […]
Malam Shamsuddin S. Fada Sakkwato 07035617436 ne ya aiko mana da wannan mukala. Babu shakka tana dauke da jan hankali da nusarwa ga shugabanninmu. A sha karatu lafiya:
Dukkan yabo da godiya da kirari sun tabbata ga Allah. TaimakonSa da gafararSa muke nema, kuma muna neman tsarinSa daga sharrin kawunanmu da munanan ayyukanmu. Wanda Allah Ya shiryar, babu mai batar da shi, wanda kuma Ya batar to babu mai shiryar da shi. Kuma ina shaidawa babu abin bauta da gaskiya sai Allah, Shi kadai ne ba shi da abokin tarayya. Kuma ina shaidawa cewa, Annabi Muhammad (SAW) bawanSa ne kuma manzonSa ne.
Ya ku wadanda suka yi imani, ku ji tsoron Allah yadda Ya cancaci a ji tsoronSa; kada ku mutu face kuna Musulmi. Ya ku mutane ku ji tsoron Ubangijinku wanda Ya halicce ku daga rai guda daya, kuma Ya halicci Abubuwa da dama daga gare shi, kuma ya yada maza da mata daga gare su (su biyu). Ku ji tsoron Allah wanda kuke yi wa junanku magiya da shi, kuma ku kiyaye zumunci. Lalle Allah mai kula ne da ku.
Ya ku wadanda suka yi imani, ku ku ji tsoron Allah kuma ku fadi magana ta daidai, sai Allah Ya gyara maku ayyukanku kuma Ya gafarta maku zunubbanku. Wanda ya bi Allah da manzonSa, hakika ya rabauta da rabo mai girma. Bayan haka, lalle mafi gaskiyar Magana ita ce maganar Allah, kuma mafi kyawon shiriya ita ce shiriyar Annabi Muhammad (S.A.W). Kuma mafi shirrin al’amura (a addini), kagaggunsu, kuma duk wani kagaggen abu (a addini) bidi’a ce, duk wata bidi’a bata ce, duka wata bata kuma tana wuta.
’Yan uwana, Allah Madaukakin Sarki Yana cewa a cikin littafinsa mai tsarki: “A yau na cika mkku addininku, kuma na cika mkku ni’imata.”
Hakika addinin Musulunci addini ne cikakke ta kowane bangare. Don haka Musulmi ba su bukatar wani addini wanda ba shi ba, ba su bukatar wata shari’a wadda ba ita ba, saboda cikar shari’ar Musulunci ta kunshi dukkan abin da yake maslaha ne ga al’umma. Ta bai wa dukkan mutane hakkokinsu – talakawa da masu arziki da masu mulki da wadanda ake mulka, namiji da mace, kai har ma da dabbobi.
To, daga cikin abin da Musulunci ya ba shi kulawa, shi ne al’amarin shugabanci da jagoranci. Musulunci bai bar mutane su zauna kara zube ba, a’a, ya yi umarni da nada shugaba koda a halin tafiya ne saboda amfanin samun shugaba a cikin al’umma amfani ne bayyananne ne; ba ya bukatar wani dogon bayani. Don rayuwar mutane ba za ta tsayu ta gyaru ba sai idan akwai shugabanci a cikinsu, don haka Allah Madaukakin Sarki da manzonSa suka nuna mahimmancin bin shugabanni da samun shugabancin a cikin mutane.
Allah Madaukakin Sarki Ya ce: “Ya ku wadanda kuka yi imani, ku bi Allah, ku bi Manzon Allah, (sannan ku bi) ma’abota al’amari daga cikinku.”
Kuma Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk wanda ya yi mani da’a, to ya yi wa Allah, wanda kuma ya saba mani to ya saba wa Allah. Haka duk wanda ya bi shugaba to ya bi ni, wanda kuma ya saba wa shugaba to ya saba mani. Shugaba garkuwa ne da ake yaki a bayansa, ake kariya da shi. Don haka idan shugaba ya yi umarni da tsoron Allah, ya yi adalci, to yana da lada. In kuwa ya aikata sabanin haka, to wannan laifi yana kansa.”
An karbo daga Ummu Salama, matar Annabi (S.A.W), daga Annabi (S.A.W), wanda ya ce: “Hakika za a nada maku shugabanni a bayana, wadanda za ku ga abu mai kyau a tare da su, kuma ku ga marasa kyau. Wanda ya ki maras kyau din ya kubuta, haka ma wanda ya yi inkari, sai dai wanda ya yarda ya bi (to wannan mai laifi ne). Sai sahabbai suka ce “ba za mu yake su ba ya Manzon Allah?” Sai ya ce, “a’a, matukar dai suna yin Sallah.”
Ya ’yan uwa, wadannan kadan ke nan daga cikin dalilan da suke nuna mahimmancin samar da shugabanci a Musulunci. Saboda haka ma Musulunci ya tsara hakkokin shugaba a kan talakawansa, ya kuma tsara hakkin talaka a kan shugabansa.
Yana cikin hakkin talakawa a kan shugabansu, ya samar masu da kotunan da za su rika yanke hukunci tsakanin mutane da sasanta su, ya samar da kwamitocin da za su rika sasanta mutane, suna umarni da kyakkyawan aiki suna hana mummuna. Kamar yadda yake wajibi ne a kan shugaba ya tsaida haddi a kan duk wanda ya ketare iyaka, ya zalunci bayin Allah, ya taba rayukansu ko jininsu ko dukiyoyinsu. Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “Haddi daya da za a yi aiki da shi a bayan kasa, ya fi a yi wa mutanen kasa ruwa na kwana arba’in.”
Haka nan hakki ne a kan shugaba ya sadar da hakkoki ga masu su, ya samar da ’yan sanda, wadanda za su ba da tsaro ga mutane da dukiyoyinsu saboda rayuwa ba ta yiwuwa sai da tsaro, kamar yadda wajibi ne a kan shugaba ya gina makarantu da wuraren ibada; ya samar da kwararrun malamai wadanda za su koyar da al’umma addini kamar yadda Manzon Allah ya zo da shi. Ya taimaka wa masu bincike, ya taimaka a wajen buga littattafan addini da sauran irin wadannan ayyuka.
Haka nan wajibi ne a kan shugaba ya zama mai adalci tsakaninsa da talakawansa, saboda adalci shi ne tushen rayuwa, kuma da adalci ne al’amura suke daidaita duniya da lahira.
Al’amuran mutane na duniya suna daidaita ne da adalci. Don haka aka ce, Allah Yana tsayar da daula mai adalci koda kuwa Kafira ce, ba Ya kuma tsayar da daula azzaluma koda kuwa Musulma ce. Haka nan ana cewa duniya tana dawwama da adalci da kafirci, amma ba ta dauWwama da zalunci da Musulunci. Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: “Babu wani zunubi da ya fi sanya azaba da wuri fiye da zalunci da yanke zumunci.” Azzalumi ana buge shi a duniya koda kuwa an masa gafara da rahama a lahira, saboda adalci tsari ne a cikin komai da komai, idan aka tsayar da al’amarin duniya a kan adalci sai komai ya tsayu, koda kuwa ma’abocin duniyar nan ba shi da rabo a lahira. Idan kuwa ba a tsayar da al’amuran duniya a kan adalci ba, to lamarin ba zai tsayu ba, koda kuwa ma’abocinsa yana da imanin da zai ishe shi a lahira.”
Haka nan shugaba ya zama karfi wajen zartar da abin da yake gaskiya ne a cikin talakawansa. Amma yanzu idan muka duba mafi yawancin shugabanni, suna amfani da ’ya’yan talakka waje cin zarafin ’yan uwanmu Musulmi. Wannan ba ya da fa’ida saboda ya kamata mu matasa mu san abin da zai taimaka mana da addininmu wajen tafiyar da zaman rayuwarmu ta duniya. Idan muka duba yanzu matasanmu sun zama kwandon shara ga shugabannimu, suna ba su kayan maye tare da daukar miyagun makamai, suna ba su abin hawa domin su ci zarafin ’yan uwansu. Ina kira ga manya da su nisanci zalunci da karya da cin amanar matasa da ha’inci da sauran munanan halaye.
Wadannan su ne kadan daga cikin hakkokin talakawa da matasa a kan shugabaninsu, don haka wajibi ne a kan shugabanni su kiyaye su, saboda al’amuran talakawansu amana ce a wuyansu, Allah zai tambaye su abin da Ya ba su kiwo na daga bayinsa. Ku ji tsoron Allah, ya ku shugabannin Najeriya. Ku kamanta, ku nemi taimakon Allah ta hanyar Sallah da hakuri, Allah Yana tare da masu hakuri, kuma kyakkyawan karshe yana ga masu tsoron Allah.
Allah Madaukakin Sarki Ya yi mana albarka cikin abin da muka ji na Alkur’ani da Hadisi, hakika Shi mai iko ne a kan komi. Allah Ka kara shiryar da mu zuwa Sunnar Annabi Muhammad (S.A.W). Allah Ka amshi ranmu muna Musulmi. Allah Ka kara kusantar da mu zuwa ga rahamarKa. Ina yi wa ’yan uwana Musulmi maza da mata fatan alheri. Allah Ka albarkaci wannan kamfani, ka kara daukaka shi a ko’ina cikin duniya.
Amin! Amin!! Amin Ya Allah!!!