Hakuri yanki ne na imani (2)

Fassarar Salihu Makera Sannan Allah Ya yi umarni da hakuri a al’amura kebantattu saboda tsananin bukatar yin hakuri a cikinsu, sai Ya yi umarni da hakuri da hukuncin Allah shari’antacce da mukaddari, Allah (SWT) Ya ce, “Saboda haka ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi daga cikinsu mai zunubi ko mai kafirci.” […]

Hakuri yanki ne na imani (2)

Masallacin Annabi (SAW) da ke Birnin Madina

Fassarar Salihu Makera

Sannan Allah Ya yi umarni da hakuri a al’amura kebantattu saboda tsananin bukatar yin hakuri a cikinsu, sai Ya yi umarni da hakuri da hukuncin Allah shari’antacce da mukaddari, Allah (SWT) Ya ce, “Saboda haka ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi daga cikinsu mai zunubi ko mai kafirci.” (K:76:24).

Kuma Ya yi umarni da hakuri bisa cutarwar kafirai, sai Madaukaki Ya ce: “Lallai ne za a jarraba ku a cikin dukiyarku da rayukanku, kuma lallai ne kuna jin cutarwa mai yawa daga wadanda aka bai wa Littafi a gabaninku da kuma wadanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi hakuri kuma kuka yi takawa, to, lallai ne wannan yana daga cikin manyan al’amura.” (K: 3: 186). Sannan Ya yi umarni bisa abubuwan da suka shafi umarni da alheri da hana abin ki, saboda abin da ke cikin hakan na wahalhalu, kuma saboda mutane suna ganin mai umarni da alheri da hana abin ki, yana shiga tsakaninsu da son zukatansu da abubuwan amfaninsu, alhali amfani da maslaha suna cikin bin abin da shari’a ta tabbatar ne kuma ta yi umarni da shi, barna kuma tana cikin bin abin da shari’a ta yi hani a kansa ne. Allah Madaukaki Ya ce: “Ya karamin dana! Ka tsaida Sallah, kuma ka yi umarni da abin da aka sani (alheri), kuma ka yi hani ga abin ki (barna), kuma ka yi hakuri a kan abin da ya same ka, lallai wancan yana daga cikin muhimman al’amura.” (K: 31:17). Kuma an umarci wanda aka ba shi shugabancin wani abu na al’amarin Musulmi kadan ne, ko mai yawa ya yi hakuri, domin hakika Manzon Allah (SAW) ya ce: “Hakika an cutar da Annabi Musa (AS) fiye da haka, kuma sai ya yi hakuri.”

Kuma Allah Ya umarci Musulmi ya nemi taimakon Allah wajen dabi’atuwa da hakuri da riko da da’a, sai Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma ku nemi taimako da yin hakuri da Sallah” (K: 2: 45). Kuma an umarci Musulmi ya sabar wa kansa dabi’ar hakuri a kowane hali da al’amari na al’amuran duniya da duk wani sha’ani, domin wannan ada tana taimakawa wajen samun hali nagari. Ya zo cikin Sahihaini cewa: “Duk wanda ya nemi ya yi hakuri, Allah zai ba shi damar yin hakurin, wanda kuma ya koyi dabi’ar wadatuwa daga mutane, sai Allah Ya wadatar da shi.”

Allah Ya yi alkawarin lada mai girma ko tsira daga ukuba ga masu hakuri, sai Madaukaki Ya ce: “Masu hakuri kawai ake cika wa ijararsu (ladansu) ba tare da wani lissafi ba.” (K: 39: 10). Sannan Madaukaki Ya ce kan ladan masu hakuri. “Wadancan suna da akibar gida mai kyau. Gidajen Aljannar zama suna shigarsu, su da wadanda suka kyautatu daga iyayensu da matansu da zuriyarsu, kuma Mala’iku suna zuwa gunsu ta kowace kofa. (Suna ce musu) “Amincin” (Allah) Ya tabbata a kanku saboda abin da kuka yi wa hakuri.Saboda haka madalla da ni’imar akibar gida.” (K: 13: 22-24).

Allah Ya albarkace mu cikin Alkur’ani Mai girma, Ya amfanar da mu daga ayoyinSa da Ambato Mai hikima. Ya amfanar da mu shiriyar Shugaban Manzanni da maganarsa madaidaiciya. Ina fadin wannan magana tawa ina neman gafarar Allah Mai girma a gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi, ku nemi gafararSa, lallai ne Shi Mai gafara ne Ma jinkai.

 

Huduba ta Biyu

Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Mai rahama Mai jinkai. Mai nuna mulki a Ranar Sakamako. Ina godiya ga Ubangiji ina yi maSa shukura. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai Yake ba Ya da abokin tarayya, Mamallaki, kuma Gaskiya Mabayyani. Ya Allah Ka kara tsira da aminci da albarka a bisa bawanKa kuma ManzonKa Muhammad da Alayensa da Sahabbansa baki daya.

Baya haka, ku ji tsoron Allah, kuma ku yi maSa da’a, domin yi maSa da’a shi ne mafi tsayuwa da karfin ayyukan ibada, kuma tsoron Allah guzuri ne gare ku a duniya da Lahira.

Ya bayin Allah! Lallai hakuri abu ne mai daci a lokacin da ake yin sa, amma abu ne mai zaki a karshen al’amari. Allah Madaukaki Ya ce, “Kuma idan kuka yi hakuri, lallai shi ne mafi alheri ga masu hakuri. Kuma ka yi hakuri, kuma hakurinka ba zai zama ba face domin Allah, kuma kada ka yi bakin ciki saboda su, kuma kada ka kasance a cikin kuncin rai daga abin da suke yi na makirci.” (K:17: 126-127). Kuma Allah Madaukaki Ya kara da cewa: “Kuma wadanda suka yi imani, kuma suka aikita ayyukan kwarai, lallai ne za Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidajen bene, koramu suna gudana daga karkashinsu, suna madawwama a cikinsu. To madalla da sakamakon masu aikin kwarai. Wadanda suka yi hakuri kuma suna dogara ga Ubangijinsu kawai.” (K: 29: 58-59).

Me ya kai girman dacewar mai hakuri bisa da’a ga Allah kuma ya kauce wa haramce-haramce, ya nemi lada a wurin Allah kan musibun da aka kaddaro masa, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya ce, “Hakika ba wani abu ne hakuri ba, face wanda aka yi a tashin farko, (ma’ana a farkon aukuwar musiba).”

Ya kai Musulmi! Ka yi aiki domin gidan tabbata da ni’ima madawwamiya, kada rayuwa mai gushewa ta rude ka, lokaci kadan ya rage ka yi gaba ka bar ta a bayanka, kuma dukiyarka da ’ya’yanka da abokin da ka fi ji da shi ba za su iya amfana maka komai ba! Ibn Umar (Allah Ya yarda da su), ya ce: “Manzon Allah (SAW) ya ce, “Ka kasance a duniya kamar bako, ko mai tsallake hanya.” Shi kuma Ibn Umar ya kara da cewa: “Idan ka wayi gari, to kada ka jira yammaci, idan kuma ka yi yammaci, to kada ka jira asubanci, ka ribaci lafiyarka kafin rashin lafiyarka, ka ribaci rayuwarka kafin mutuwarka.”

Duk wanda ya san Ubangijinsa kuma ya san abin da ya tanada ga masoyanSa da abin da ya yi tattali ga makiyanSa, ya kuma san matsayinsa game da rayuwar duniya, to, ya ji dadin yin hakuri wajen neman yardar Allah, ya rika ganin duk aikin da yake yi na da’a bai isa ba, ya rika tsoron kada Allah Ya leka irin ayyukan da yake yi, kuma ba makawa ya guji abubuwan da aka haramta.

Ya bayin Allah! “Lallai Allah da Mala’ikunSa suna salati ga Annabi. Ya ku wadanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi.” (K:33: 56). Ku yi salati ku yi taslimi a kan shugaban mutanen farko da na karshe, kuma Shugaban Manzanni. Ya Ubangiji! Ka yi salati ga Shugabanmu Muhammadu da alayen Muhammad, kamar yadda Ka yi salati ga Ibrahim da alayen Ibrahim. Lallai Kai abin godewa ne Mai girma. Ya Ubangiji! Ka yi albarka ga Annabi Muhammadu da alayen Annabi Muhammadu, kamar yadda Ka yi albarka ga Annabi Ibrahim da alayen Annabi Ibrahim. Lallai Kai abin godewa ne Mai girma, da aminci aminci mai yawa.

Ya Ubangiji! Ka yarda da sahabban Manzonka baki daya, Ka yarda da Halifofin Annabi (SAW), Abubakar da Umar da Usman da Aliyu da sauran sahabbai baki daya da wadanda suka biyo su da kyautatawa har zuwa Ranar Sakamako. Ya Ubangiji! Mu ma Ka yarda da mu don kyautarKa da karimcinKa da rahamarKa,  ya Mafi rahamar masu rahama.

Ya Ubangiji! Ka daukaka Musulunci da Musulmi, Ka kaskantar da kafirci da kafirai, Ka darkake makiyanka, makiya addini ya Ubangijin talikai! Ka daidaita tsakanin zukatan Musulmi, Ka gyara tsakaninsu, Ka shiryar da su tafarkin zaman lafiya, Ka fitar da su daga duffan zalunci da kafirci da wahalhalu zuwa ga hasken adalci da imani da sauki.

Ya Ubangiji! Ka taimake su a kan makiyanKa kuma makiyansu ya Ubangijin talikai! Ya Ubangiji! Ka taimaki addininKa da LittafinKa da Sunnar ManzonKa, ya Mai ikon yi! Ya Mai cikakken karfi!

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos