Halaye 20 abin ki na mace

Samun mace mai kyawun hali da dabi’a abu ne mai matukar muhimmanci a cikin al’umma, yayin da mugun hali kan jawo wa iyalai tarnaki da rudani a zamantakewar al’ummu daban-daban. Don haka a cikin mata akwai wadanda suka siffantu da munanan hali, wadannan mata abin a guje masu ne wajen kin aurarsu, idan kuwa har […]

Halaye 20 abin ki na mace
Halaye 20 abin ki na mace

Samun mace mai kyawun hali da dabi’a abu ne mai matukar muhimmanci a cikin al’umma, yayin da mugun hali kan jawo wa iyalai tarnaki da rudani a zamantakewar al’ummu daban-daban. Don haka a cikin mata akwai wadanda suka siffantu da munanan hali, wadannan mata abin a guje masu ne wajen kin aurarsu, idan kuwa har an auresu to akwai bukatar tarbiyantar da su da dora su akan hanya madaidaiciya domin samun al’umma tagari.

Wadannan siffofi sun hada da:
1. Wacce ta kasance mai lalaci da kasala, ga kuma halin ko- in- kula a kan neman Ilimi.
2. Wacce ta kasance ‘yar zaman banza, da gulma da hirarrakin tara abin duniya da burace-burace.
3. Wacce ta zama mai yawan gori, da rashin kunya, ga kuma kage akan abinda ba a yi ba ta ce anyi.
4. Macen da ta kasance mai yawan batsa da jawo jafa’i ga mutane.
5. Da wacce ta kasance mai girman kai da jiji da kai, ga kuma masifa na babu gaira babu dalili.
6. Wacce ta kasance mai kallon finafinan batsa, da sauraron badala.
7. Da mai bakin ciki da kutungwila ga saurayin kawa ko abokiyar zama.
8. Wacce ta kasance mai shan kanshi da nuna isa, sannan ga kokari kai wa inda Allah bai kai ta ba.
9. Macen da ta zama mai son duniya, ta yadda za ka ga babu abinda ta sani sai wahalar da mijinta wajen yin gasa da sauran mata wajen tara abin duniya.
10. Da wacce ta kasance mai mugunta da nuna kyashi, burinta a kullum ta hana mijinta alheri.
11. Da macen da kasance kullum burinta ta hana mijinta yin alheri.
12. Da macen da ta kasance kazama, wanda rashin tsabtar gidan kan tilasta wa maigida zaman majalisa.
13. Sai wacce ta zama mai kwadayin abin duniya da za ka ga babu abinda ta sanya a gaba sai duniya, ko da kuwa za ta sanya mijinta yin sata ne.
14. Sai wacc ta zama jahila, ta yadda za ka ga ba ta da wani shiri na fita daga jahilcin.
15. Da macen da ta kasance mai yawan kausasa wa mijinta, sauran mutane kuwa ta tausasa masu.
16. Da wacce take kullum so take wani bala’i ya samu mijinta, kuma ta yi farin ciki idan ya same shi.
17. Sai wacce ta kasance a kullum burinta ta janyo abinda zai sanya mijinta bakin ciki, har ya zamana cewa ya tsaneta.
18. Sai macen da ta zama mara tausayi, burinta kodayaushe ta dora masa abinda ba zai iya ba.
19. Da wacce ta kasance mai kasala wajen yin hidima ga ‘ya’yanta da mijinta.
20. Da kuma macen da ta kasance ballagaza da za ka ga babu ruwanta da abinda zai zubar mata da kima da mutunci, ita ba ta damu ba.
Wadannan da ma wasunsu na daga cikin halaye abin ki ga mace da yakamata a yi taka tsan-tsan da su. Don haka iyaye suna da rawar takawa wajen saita ya’ya’yansu akan hanya tagari.
Hakika binciken tsanaki akan hali da dabi’un mace kafin aure na daga cikin muhimman abubuwa da sukan taimaka wa namiji samun mace tagari.
Ibrahim Hamisu ya rubuto ne daga Kano kuma za a iya tuntubarsa a 08060651676.