‘Hali mara kyau’

Barkamu da warhaka Manyan gobe. Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya.  A yau na kawo muku labari ne mai taken:  “Hali mara kyau”. Labarin ya yi nuni ne ga yadda ake kokarin canza halin mutum daga mara kyau zuwa na kirki. A sha karatu lafiya. Akwai wani Sarki a wani kauye wanda  […]

‘Hali mara kyau’

Barkamu da warhaka Manyan gobe. Tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya.  A yau na kawo muku labari ne mai taken:  “Hali mara kyau”. Labarin ya yi nuni ne ga yadda ake kokarin canza halin mutum daga mara kyau zuwa na kirki.

A sha karatu lafiya.

Akwai wani Sarki a wani kauye wanda  yake da wani hatsabibin da.   Saboda rashin ji, a kullum sai an kai karar yaron wajen Sarki.  Da zarar gari ya waye za ka ga jama’a na tururuwa wajen Sarki don su kai karar wannan yaro.  Haka abin yake daga makwafta.

Abin ya damu Sarki, sai ya shiga tunanin yadda zai bullo wa al’amarin.

Ana cikin haka sai labari ya iso wa sarki cewa akwai wani tsoho mai ilimi da dabara kuma ana kyautata zaton zai iya taimaka wa dan Sarkin zama mutumin kirki a rayuwa.

Mu kwana nan