‘Hali mara kyau’ (3)
Sai tsoho ya yi murmushi ya ce “yadda ka gagara tuge wannan bishiya na ga kamar ranka ya baci, haka kowa a kauyenku yake cikin bakin ciki da munanan halayenka, don haka sai ka dauki darasi ka gyara don ka zama mutumin kirki. Wannan misali da tsoho ya ba dan Sarki ya yi matukar girgiza […]
Sai tsoho ya yi murmushi ya ce “yadda ka gagara tuge wannan bishiya na ga kamar ranka ya baci, haka kowa a kauyenku yake cikin bakin ciki da munanan halayenka, don haka sai ka dauki darasi ka gyara don ka zama mutumin kirki.
Wannan misali da tsoho ya ba dan Sarki ya yi matukar girgiza shi tun daga nan ya canja halayensa zuwa na kirki, inda Sarki da sauran mutanen gari suka rika murna da kuma mamakin yadda dan Sarki ya canja halayensa zuwa na kirki.
Nan take Sarki ya yi wa tsoho godiya da kuma yi masa kyauta mai yawa a bisa wannan jihadi da ya yi a kan dan Sarki mara jin magana.