Halimah Yacof ta zama Shugabar kasar Singapore mace ta farko

Tsohuwar Shugabar Majalisar kasar Singapore Halimah Yacob ta zama shubagar kasa mace ta farko a kasar a sakamakon zabenta da aka yi   shekaranjiya Laraba. kasar Singapore tuni ta ware mukamin shugaban kasar ga tsirarrun kabilun Malay a wannan karon. Manufar hakan kuwa ita ce a jawo daukacin kabilun kasar a jika, ta yadda kowa […]

Halimah Yacof ta zama Shugabar kasar Singapore mace ta farko

Tsohuwar Shugabar Majalisar kasar Singapore Halimah Yacob ta zama shubagar kasa mace ta farko a kasar a sakamakon zabenta da aka yi   shekaranjiya Laraba.

kasar Singapore tuni ta ware mukamin shugaban kasar ga tsirarrun kabilun Malay a wannan karon. Manufar hakan kuwa ita ce a jawo daukacin kabilun kasar a jika, ta yadda kowa zai ji ana yi da shi. Singapore dai ta mayar da mukami na jeka-na-yi ka ne, don haka ta bar wa tsirarrun kabilun na Malay, wadanda mafi yawansu Musulmi ne.

“Duk da yake zaben ma ware musu aka yi, ni ba shugabar kasa ba ce da aka ware ta,” inji Halimah Yacob. Gogewar Halimah a  jagorancin majalisar kasar ya ba cancantar zama ’yar takara bisa tanade-tanaden dokokin zaben . daukacin  ’yan takarar hudu da suka fafata takarar biyu ne kawai ba su cancanta ba, domin su ba su fito daga kabilar Malay ba. 

dan Malay na karshe da ya rike mukamin shugaban kasar shi ne Yusof Ishak, wanda kimar mutuntakarsa ta haska a kasar, har aka sanya hotonsa a kudin kasar.

Yuosif ya yi mulki a tsakanin shekarun 1965 zuwa 1975, bayan da Singapore ta samu ’yancin kanta, a lokacin da aka waresu daga kasar Malesiya, amma a lokacin karfin ikon tafiyar harkokin mulki duk an tattara ne ga Lee Kuan Yew, Firayiministan kasar na farko.

Rabuwar Singapore daga Malesiya ya sanya Malay suka zama kabila mafi yawa a Malesiya, yayin da ’yan asalin  Sin suka fi yawa a bangare Singapore.