Halin da muka shiga kafin mu baro Bama – ’Yan gudun hijira
Sama da mako biyu da kungiyar Boko Haram ta kwace iko da garin Bama da ke Jihar Borno a harin da ta kashe mutane da barnata dukiyoyi, ’yan gudun hijira daga Bama da ke zaune a Maiduguri na ci gaba da bayyana irin wahalar da suka sha da ta hada da tafiya mai nisa a […]
Sama da mako biyu da kungiyar Boko Haram ta kwace iko da garin Bama da ke Jihar Borno a harin da ta kashe mutane da barnata dukiyoyi, ’yan gudun hijira daga Bama da ke zaune a Maiduguri na ci gaba da bayyana irin wahalar da suka sha da ta hada da tafiya mai nisa a kafa da yunwa kafin su isa Maiduguri.
Wani magidanci a sansanin ’yan gudun hijira na masu yi wa kasa hidima da Hukumar Agajin Gaggawa (NEMA) ta kai wa taimako, mai suna Musa Muhammad, ya shaida wa wakilinmu cewa sama da mako guda ke nan baya iya barci saboda bai san inda matansa biyu da ’ya’yansa 12 suke ba. “Ina cikin damuwa, na rikice kuma ba na barci saboda yanzu haka ban san halin da iyalaina suke ciki ba. Shin an kashe su ne ko suna da ransu
ko a’a an yi garkuwa da su ne? Sama da mako guda ke nan rabona da matana biyu, kuma dana daya na gani daga cikin su 13, saboda haka ina raye ne amma ba ni cikin hayyacina, fatana Allah Ya bayyanar mini da iyalan nawa, kuma ina roko ga Gwamnatin Tarayya da hukumomin da abin ya shafa su taimaka mana mu koma garinmu don mu hade da iyalanmu.”
Hajja Kalsum wadda ta fito daga kauyen Darul-Jamal a yankin Bama ta ce “A ranar farko da ’yan bindigar suka kawo hari sun fara ne da kauyenmu Darul-Jamal, inda muka watse muka gudu, sai bayan kwana biyar na ga ’ya’yana uku da jikokina takwas a nan Maiduguri. Lokacin da na gudu daga kauyenmu na shiga Bama da tunanin zan samu
mafaka a garin, na makale a garin har kwana biyar da maharan suka fada Bama sun yi ta harba bindigogi kamar sama za ta fado, na ga gawarwakin mutane musamman matasa watse a kan hanya, maharan sun yi ta gargadin tsofaffin da suka rage cewa kada su yarda su dauki wata gawa don su binne, kuma za su kashe duk wanda ya saba wa umarninsu. Har muka bar garin ba a kwashe gawarwakin ba.”
Wata dattijiya mai suna Ya Bintu da ta gudo daga Bama ta ce ta sha da kyar bayan da ta zauna na kwana shida a karkashin ikon Boko Haram. “Abin farin ciki ba su taba ni ba kuma ba su taba ’yan gudun hijirar da ke gidana ba, sai dai suna yawan zuwa su tambaye ni ko akwai ’yan mata a gidana? Ni kuma nakan ce babu, sai na fara sakin jiki da su, to amma da muka samu hanya sai muka gudu zuwa Maiduguri bayan kwana biyar. Suna zuwa ne da misalin karfe 6:00 na yamma a kan babura ta hanyar Gwoza su tsaya a Bama har faduwar rana suna ta harbi a sama, kafin su tafi suna fada wa tsofaffin da suka rage a garin cewa kada su ji tsoro ba za su taba mu ba, amma kada mu binne gawarwakin da suke zube a hanyoyi,” inji ta.
Ta ce sun yi tafiya mai nisa kafi su isa Kawuri inda sojoji suke, suka taimake su suka kawo su Maiduguri.